Shafin Farko

PTA


Gabatarwa

Ƙungiyar Iyayen Yara da Malaman Makaranta, ƙungiya ce da ake kafa ta a makarantu, wacce mambobinta sune iyayen yara da kuma malaman da ke karantarwa a wannan makaranta. A Turance ana kiranta da Parent Teacher Association da ake taƙaitawa da PTA. Wannan ƙungiya, inuwa ce da ke haɗa iyayen yara da malaman da ke karantar da ‘ya’yansu waje guda da nufin haɗa ƙarfi-da-ƙarfe waje guda don ganin an cimma manufa guda, wacce manufar ita ce gina yaro mai nagarta domin amfanin al’umma baki ɗaya.

Wannan ƙungiya takan shirya tarurruka waɗanda suke zama wata kafar da ke sanar da iyayen yara abubuwan da makaranta take gudanarwa don ɗorawa a gida da kuma cike giɓin da yake akwai game da buƙatun makaranta.

Manufofi

Manya-manyan manufofin kafa wannan ƙungiya su ne:

 1. Tabbatar da ganin an aiwatar da abubuwan da suke cikin manhajar karatu;
 2. Cike dukkan wani giɓi da yake akwai na ɗaukar nauyin makaranta. Wannan ƙungiya ita ke ɗaukar gabaren samar da dukkan wani abu da makaranta ta ke buƙata don gudanarawar karatu a daidai gaɓar da aka samu tangarɗa daga ɓangaren gwamnati. Misali,
  • Ɗaukar Malamai: Idan aka samu cewa malamai sun yi ƙaranci a makaranta, kuma an samu jinkiri daga ɓangaren gwamnati wajen samar da waɗannan malamai ko malami, wannan ƙungiya takan ɗauki malamin ko malamai ta kuma riƙa biyansu alawus har zuwa lokacin da gwamnati za ta samar. Ko kuwa ma a wasu lokutan kuma a wasu makarantun kamar irin makarantun al’umma community schools, to wannan ƙungiya takan ɗauki malamai na din-din-din.
  • Samar da Kayan Aiki: Wannan na daga cikin ayyukan wannan ƙungiya na yau-da-gobe. Kayan rubutu, ruwan sha, magani da sauran su da sauransu na daga cikin abubuwan da wannan ƙungiya take samarwa.
  • Gina ajujuwa, ɗakunan karatu (libraries), ɗakunan shan magani, ɗakunan girki, suma suna daga cikin ababen da wannan ƙungiya take samarwa.
 3. Sada Zumunci: Wannan ƙungiya takan zama wata kafar sada zumunci tsakanin iyayen yara a junansu, da kuma tsakaninsu da malaman makaranta.
 4. Kyautata Dangantakar Makaranta da Al’umma: Haka nan ƙungiyar takan zama wata kafa da take ƙulla zumunci tsakaninta da al’ummar da makarantar take a cikinta. Akan samu wani lokaci da za a gayyaci jama’ar yankin da makarantar take, a gabatar musu da wani jawabi da zai ilimantar da su game da wani abu idan buƙatar hakan ta taso;
 5. Yaƙar Jahilci: Wannan ƙungiya takan zama wata kafa ta yaƙar jahilci ta hanyar haɗa kai da malaman makaranta domin buɗe ajujuwan karatun manyan da basu samu damar yin karatu ba a lokacin da suke ƙanana.

Tsarin Shugabanci

Wannan ƙungiya tana da tabbatacciyar hanyar shugabanci. Shugabcinta daban dana makaranta. Shugabanci ne wanda yake sarƙafaffe tsakanin iyayen yara da kuma malaman makaranta.

Wasu kujeru guda biyu an sadaukar da su ga ɓangarorin biyu; ɗaya daga ɓangaren malamai, ɗaya kuma daga ɓangaren iyaye. Sauran kuma mai rabo ka samu daga kowane ɓangare.

Dimin-da’iman, shugaba da muƙaddashinsa (chairman da vice chairman) sukan fito ne daga ɓangaren iyayen yara ta hanyar zaɓe. Sakatare kuma, ba zaɓe, kai tsaye shugaban makaranta (headmaster/head teacher), shi ne yake zama sakataren ƙungiya. Ba canji har sai idan an yi wani sabon shugaban makarantar. Alhakin adana bayanai, da sauran ɗawainiyoyin rubuce-rubuce, kaɗan ne daga cikin ayyukan sakataren wannan ƙungiya.

Akan so a samar wa wannan ƙungiya jami’an hulɗa da jama’a (PRO) guda biyu ko fiye da haka, bisa la’akari da girman makaranta da kuma yankin da makarantar take. Idan guda biyun ne, to ɗaya daga cikin malamai, ɗaya kuma daga cikin iyayen yara.

Tarurruka

Wannan ƙungiya takan gudanar da tarurrukan tattaunawa gwargwadon hali. Daga ciki akwai:

 1. Babban Taro: Wannan shi ne taron da yake haɗa kowa-da-kowa a lokaci guda. Yawanci a irin waɗannan tarurruka ana buɗe asusun ƙungiya don neman gudunmawa daga mahalarta taron. Saboda haka dukkan wanda ake ganin zai iya bayar da gudunmawa koma daga ina yake, akan gayyace shi wannan taro. Sannan kuma akan gudanar da irin wannan taro sau biyu ko sau ɗaya a dukkan zangon karatu. Mafi ƙaranci shi ne a yi shi sau ɗaya a shekara. Yawaita wannan babban taron, yana da matuƙar fa’ida.
 2. Taron Shugabanni: Taro ne da iya zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiya ke zama don tattaunawa game da wasu abubuwa a madadin ‘yan ƙungiya ko kuma shirya babban taro da sauransu.
 3. Ɗaya-da-Ɗaya: Taro ne ko a ce zaman tattaunawa ne tsakanin jami’an wannan ƙungiya da kuma wani baban yaro ko yara da suke fuskantar wata matsalar da ta gagari kundila. Akwai matakai daki-daki da ake bi wajen warware matsalar ɗalibai a makaranta kamawa tun daga aji, ko unguwa har zuwa kan shugaban makaranta. Idan dukkan waɗannan matakai suka ci tura, to akan miƙa matsalar ga kwamatin sasanto na ƙungiyar iyaye da malaman makaranta.

Manazarta:


Lauermann f. V. (2013). Teacher Responsibility: Its Meaning, Measure, and Educational Implications. The University of Michigan.

Missokia E. (2013). Who is a Teacher? Quality Teachers for Quality Education, Role/Responsibilities of a Teacher. HakiElimu Position Papers. Dar-es Salaam, Tanzania.

Wikipedia (2017). Teacher. https://en.m.wikipedia.org/wiki/teacher