Sana'ar Arkomanci

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Arkomanci


Gabatarwa

Arkomanci sana’a ce ta sayar da kayan amfanin gona wanda aka cire shi daga jikin zangarniyarsa. Mai yin wannan sana’a shi ake kira arkomi.

Ana gudanar da wannan sana’a ta hanyar karɓar kayan amfanin gona gyararre daga hannun mai shi a sayar da shi ta hanyar awo. Duk mutumin da ke son saye ko sayar da kayan amfanin gona gyararre, yakan je wajen arkomi ya aunar ko ya auna gwargwadon buƙata, kamawa tun daga rabin mudu har zuwa iya ƙarfi. Dukkan abin awon da ya zuba a ƙasa a lokacin da ake awo, to ya zama rabon arkomi. Idan kasuwa ta ci, ta tashi, sai arkomi ya share kan shimfiɗarsa ya yi gaba da wannan ragowar. Haka nan kuma a duk cikin mudu goma da arkomi ya sayar, to kuɗin mudu ɗaya ladarsa ce.

Arkomi kan sayar da buhu-buhu na kayan amfani da kuma dami-dami, amma wannan ba kasafai ake kai musu ba, sai tsalli-tsalli. An fi kai buhu-buhu, da dami-dami zuwa ga dillallan kayan amfanin gona.

Kayan Aiki


Shinkafa a Cikin Sanho


Masaki, abin zuba kayan da za a aunar

Kayayyakin da ake buƙata don gudanar da sana’ar arkomanci sun haɗa da: Mudu, masaki, sanho, shimfiɗa wacce a da can baya, suna amfani da tabarma buji-kura (babbar tabarma) yanzu kuma sukan shimfiɗa leda ko tamfal, da kuma basilla.

Kayayyakin da Suke Sayarwa

Dukkan nau’in kayana amfanin gona da ka iya kasancewa gero, dawa, maiwa, alkama, wake, shinkafa, gyaɗa, gurjiya, acca, ibiro, da sauransu.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare. Northern Publishing Company, Zaria-Nigeria.

Ziyarar Gani da Ido zuwa Kasuwar Garki, a ranar 16/12/2016. Ƙaramar Hukumar Garki, Jahar Jigawa, a Najeriya


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub