Sana'ar Dukanci

Me ka ke nema?


Shafin Farko   

Dukanci


Gabatarwa

Sana’ar Dukanci, sana’a ce da ake sarrafa fata a mayar da ita wani abu mai amfani kamar takalmi, guga, riga da sauransu domin samun abin masarufi. Baduku shi ne sunan mai yin sana’ar Dukanci. Fatar da masu jima ke samarwa, ita dukawa ke sarrafawa. Akwai unguwar da ta yi fice a kan wannan sana’a a cikin birnin Kano da ake kira Dukawa.

Kayan Aiki

Dukawa sukan gudanar da sana’arsu ta dukanci ta hanyar amfani da kayayyakin da suka haɗa da: fata, almakashi, guduma, da sauransu

Kayayyakin da Dukawa ke Yi

Matashi (fulo), majingini, buzu, laya, guru, daga, kambu, salka, garkuwa, maratayi, taraha/tintimi, rigar sirdi, ragama, kube, gafaka, zabira, linzami, takalmi, kwari, tandu, burgami, warki, guga, dagumi, sulkami, zugazugi (abin da masu sana'ar ƙira ke hura wuta da shi), taiki, da sauransu.


Jemammiyar Fata.

Zabira (Jakar Wanzamai)

Laya

Baduku A Bakin Aiki

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Kendal (2009). The Importance of Animals. An ciro daga https://www.toxicology. org/pubs/docs/air/AIR_Final.pdf

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).

Zarruƙ R.M., Kafin-Hausa A.A. da Al-Hassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub