Sana'ar Farauta

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar farauta


Gabatarwa

A sauƙaƙƙiyar kalma, ana iya fassara farauta da nema. A wasu lokutan idan magidanta a Ƙasar Hausa za su fita neman abinci sukan ce ‘Mun tafi mu farauto’, kai mata ma a cikin gida wasu lokutan sukan yi bankwana da mazajensu ta hanyar faɗin ‘A farauto da yawa’. Sana’ar Farauta sana’a ce da masu gudanar da ita ke shiga daji su riƙa kaso namun daji domin samun abinci. Wannan sana’a ta farauta ana ganin kusan ita ce sana’ar farko a tarihin bil-adama (Ƙwalli, 1996; Alhassan, Musa, da Zarruƙ (1982).

Wasu daga cikin garuruwan Hausawa, mafarauta ne suka kafa su, saboda zuwansu neman gurin yin farauta mafi dacewa. Daga cikin irin waɗannan garuruwa akwai da kuma Dutse.

Kusan a farkon lamari, farauta sana’a ce ta kowa da kowa, saboda kasancewar ta hanya ɗaya tilo ta samun abinci, sutura, da kuma kare kai daga harin namun daji. Amma daga baya, da aka samu wasu hanyoyin sana’a kamar irin su noma, ƙira, da sauransu, sai ya zama wasu mutane ne suka taƙaitu da ita.

Sana’ar farauta sana’ace da sai jarumin mutum ke yin ta. Ba a rasa mafarauci da rashin tsoro, zafin rai, kuzari, da kuma cikakkiyar lafiyar jiki. Sana’a ce da ake shiga cikin daji a ɗau lokaci mai tsawo, mafi ƙaranci shi ne yini guda, ana ta karakaina a daji, idan an ci karo da wata dabbar daji ko tsuntsaye ko ƙwari kamar irin su maciji, damo, da sauransu a kama a yanka.

Makamai

Makami shi ne kayan aikin mafarauci. Yana amfani da kayayyakin da suka haɗa da wuƙa, adda, takobi, barandami, tsitaka, gariyo, kwari-da-baka, bindiga, kulki, gora, kokara, ƙaho, kere, ruzu, buzu, da sauransu.

Rabe-Rabe

Yanayin yadda da ake gudanar da farauta da kuma irin kayan aikin da ake amfani da su shi ne abin lura wajen rarraba ta. Daga ciki akwai:

  1. Farautar mutum ɗaya: Akwai mutane kamar maharba da ke amfani da makamai irin su kwari da baka, daga baya kuma suka ƙara da bindiga, waɗanda basu da wata sana’a in banda shiga daji su kaso dabbobi domin ci da kuma sayarwa.
  2. Farautar Gangami: Farauta ce da ake gudanar da ita ta hanyar haɗa gangamin jama’a waɗanda ka iya zamowa daga gari guda ko kuma garuruwa su haɗu a wani daji domin gudanar da wannan sana’a ta farauta. Su irin waɗannan mutane sune ke amfani da makamai da suka haɗa da gora, kere, sanda, barandami, gariyo, bindiga, kwari-da-baka, wuƙa, adda, da sauransu.

    Idan aka shirya irin wannan farauta kai ka ɗauka yaƙi za a fita. A irin wannan farauta ce ake faɗa tsakanin abokan gaba.

  3. Sharani: Farauta ce da yawanci yara ne ke yin ta a dajin da bashi da girma da kuma duhu, yawanci akan yi irin wannan farauta a lokacin rani. Samari da yara masu ƙwazo su ke yin wannan farauta. Sukan kaso dabbobi irin su zomo, bushiya, muzuru, yanyawa, gafiya, maciji da sauran ƙananan dabbobin da ba sa nisa da gari.

Ba a cika nisa da gari ba wajen gudanar da wannan farauta. Haka nan kuma ana ma gudanar da ita da daddare musamman lokacin da farin wata yake tsaka da haske.

Kiɗa

Mafarauta suna da kiɗansu kamar irin su gangi da sauransu.

Kiɗan Gangi

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Ƙwalli K.M. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa (Babu sunan gurin ɗab’i).

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub