Sana'ar Fawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Fawa


Gabatarwa

Sana’ar fawa na ɗaya daga cikin tsofaffin sana’o’in ƙasar Hausa. Sana’a ce da ake yanka dabbobi domin a sayar da namansu ga mabuƙata. Wanda ke aiwatar da wannan sana’a shi ake kira Mahauci. Ya zo a Alhassan, Musa, da Zarruƙ (1982). Cewa ana kiran wannan sana’a da suna ‘Rudanci’.

Naman da aka yanka akan sayar da shi a nau’i huɗu; ko dai a sayar da shi ɗanye ga masu buƙatar dafawa da kansu, ko kuma a gasa shi a matsayin tsire, ko kuma a gasa shi a matsayin balangu, ko kuma a gasa shi a matsayin kilishi.

Kayan Aikin Fawa

 1. Wuƙa: da ita ake yanka dukkan abin da yake buƙatar yanka kamawa tun daga ita kanta dabbar, zuwa feɗe ta, har zuwa yanka naman.
 2. Jantaɗi: Da shi ake wasa wuƙa ko gatari.
 3. Gatari: Ana sara ƙashi mai tauri da shi.
 4. Gungume: Itace ne mai kauri da ake ɗora ƙashi a kai a daddatsa shi.
 5. Daro: A cikinsa ake wanke nama, sannan kuma bayan an gasa naman kamar balangu sai a sake zuba shi a ciki.
 6. Tire: A cikinsa ake ɗora tsire ko kilishi.
 7. Takarda: Da ita ake naɗe naman.
 8. Leda: Ana zuba nama a cikinta.


Tukubar Tsire ana Gashi

Guraren Aikin Fawa

 1. Mahauta: Yanki ne na kasuwa wanda mahauta ke gudanar da sana’arsu a wajen.
 2. Tirke ko Kara: Yanki ne na kasuwa da mahauta da makiyaya ke zuwa domin saye ko sayar da dabbobi.
 3. Mayanka/Kwata: Gurin da ake yanka dabbobi.
 4. Tukuba: Gurin da ake gasa nama. Akwai tukubar tsire, akwai kuma ta gasa kilishi ko balangu.

Kayan da Fawa ke Samarwa

 1. Nama: Mahauta kan sayar da ɗanyen nama ga masu dafawa ko yin miya a gida.
 2. Tsire: Shi ne naman da ake yayyanka shi sannan a lulluɓe shi da garin ƙuliƙuli (ƙarago), a yayyafa masa mai (man ƙuli/man gyaɗa), sannan a soka a jikin tsinke, sai kuma a gasa.
 3. Balangu: Nama ne da ake gasa shi a dunƙulensa ba tare da an saka masa komai ba in banda gishiri, bayan an gasa kuma sai a yaryaɗa masa mai. Sannan a zuba a mazubi mafi yawanci daro, a ɗora a kan teburi ana jiran masu saya.
 4. Kilishi: Nama ne da ake yayyanka shi sannan a fere shi, sai kuma a shanya a kan gadon kara, sannan a sake tsoma shi a cikin damammen garin ƙuliƙuli, ko kuma a gauraya ƙuliƙulin da dabino ko aya da sauransu, sannan a sake shanya shi, sai kuma daga baya a gasa. Wannan nau’i na nama akan ajiye shi na lokaci mai tsawo ana amfani da shi.  

 5. Kilishi

 6. Fata: Akan babbake ta a cire gashin a yi ganda ko ragadada da ita, ko kuma a sayar da ita ga masu sana’ar jima.
 7. Kai da Ƙafa: Ana dafa su a sayar.

Al’adu

A gargajiyance, mahautan kan gudanar da wasanni kala biyu:
 1. Hawan Ƙaho: Wasa ne da mahauta kan samu wani bajimi ƙosasshe kuma mafaɗaci su fito da shi cikin jama’a suna hawa ƙahonsa.
 2. Dambe: Wasa ne da mahauta ke yi a lokutan bukukuwansu musamman lokacin bikin aure. A wani lokaci a baya, mahauta suna ganin dukkan matashin da baya dambe a matsayin rago.

Tsage

Tsagen mahauta shi ne bille.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub