Sana'ar Gini

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Gini


Gabatarwa

Sana'ar Gini sana’a ce da ake sarrafa abubuwan da suka shafi ƙasa kamar irin su yumɓu, taɓo, yashi da sauransu domin su zama masu amfani. Kamar gina muhalli da kuma gina mazubi kamar irin su tukunya, tulu, da sauransu.

Wannan sana’a ta gini daɗaɗɗiyar sana’a a ce. Asali mutane kan gina bukka ne ta hanyar amfani da kara sannan kuma daga baya a yaɓe shi da ƙasa. Daga nan kuma sai aka samu cigaba, aka koma ana gina ɗaki da zallar tubalin ƙasa, kama-kama har zuwa yin bulon ƙasa sannan a gina ɗaki da shi.


Ramin Bulon ƙasa.

Rabe-Raben Sana’ar Gini

Sana’ar Gini ta kasu gida uku:
  1. Akwai ginin muhalli da ya shafi gina gida baƙi ɗayansa da dukkan nau’ukan ɗakuna kamawa tun daga ɗakin kwana, ɗakin hutu, ɗakin girki, ɗakin karatu da sauransu.
  2. Ginin Tukwane da sauran kayayyakin adana ruwa, abinci da sauransu.

  3. Tukunya

  4. Ginin Rijiya, sana’a ce da ake haƙa rami domin samo ruwan amfanin yau-da-kullum, ko kuma masai (shadda ko sarga).

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Kendal (2009). The Importance of Animals. An ciro daga https://www.toxicology. org/pubs/docs/air/AIR_Final.pdf

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).

Zarruƙ R.M., Kafin-Hausa A.A. da Al-Hassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub