Horo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Horo a Tarbiyya


Gabatarwa

Bahaushe yana da matakai da yake bi wajen horas da duk wanda ya kaucewa kyakkyawar tarbiyyar da aka ɗora shi a kai. Wannan kuma yana bambanta da bambancin shekaru. Sannan kuma yana da matakai. Akwai waɗanda suka keɓanta da yara, akwai kuma hanyoyin horas da manya, sannan kuma akwai gama-gari. Ga kaɗan daga cikinsu:

 1. Harara, mummunan kallo da gyaɗa kai.
 2. Tsawatarwa da baki.
 3. Gargaɗi da kashedi (Manya kawai).
 4. Kurari (Yara kawai).
 5. Hana fita yawo (Yara kawai).
 6. Mayar da mutun saniyar ware.
 7. Duka (Yara kawai).
 8. Korar mutum daga gida (Manya).
 9. Kai mutum ga hukuma (Manya).
 10.  Ɗauri a gidan kaso (Manya).
 11.  Ɗauri a mari/turu (Yara).

Manazarta:


Abu Hamza B.D. (2013). Jawabin Darasin Aji Biyu na Babbar Sakandare. Kulliyatul Mu’allim Luggatul Arabiyya, Keffi, Jahar Nassara, Najeriya.

Abu Zakariyya I. (2007). Riyadhus-Salihiina. Darel Fikr Printers, Publishers and Distributors. Beirut-Lebanon.

Ɗan’abubakar U. (Babu Shekara). Buguyatul Muslimina Wal Kifayatul Waa’iziina Wal Mutta’iziin. Maɗaba’ar Alƙali Sharfi Bala, Kano, Najeriya.

Mesel B.D. (2015). Wittengenstein, Meta-Ethics and the Subject Matter of Moral Philosphy Ethical Perspective 22, no 1 (2015): 69 – 98. Center for Ethics, KU Leuven.

Rayner S. (2005). Hume’s Moral Philosphy. Manchester Journal of Philosphy Vol. 14: 185 eu 1, Article 2. An ciro daga shafin http://digital commons.macalester.edu/philo/vol14/iss1/2

Sayyadi A. (2004). Mukhtaril hadithun-nabawi wal hikimatul Muhammadiyya. Maɗaba’ar Alƙali Sharif Bala. Kano, Najeriya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantu 3. University Press PLC. Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Tarbiyya


  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub