Rubutun Boko

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Rubutun Boko


Gabatarwa

Salon rubutu ne da Bahaushe ya ara daga Turawan Ingilishi, ya sarrafa shi, yake rubuta maganganunsa da shi.

Masana fannin Hausa sun ce Turawa ne suka ƙagi rubutun Hausa da salon rubutunsu kamar yadda na naƙalto Yahaya, Zariya, Gusau da 'Yar'aduwa (2006), suna cewa: "Tun kafin Hausawa su fara yin amfani da wannan hanyar rubutu, Turawa ne da kansu suka fara yin amfani da wannan hanya, suna rubuta Hausa da wasu harsunan Afirka ta Yamma a cikin ƙarni na goma sha takwas".

Shi kuma Bahaushe ya fara yin amfani da wannan salon rubutun ne bayan Turawan sun ci shi da yaƙi a farkon ƙarni na ashirin. An kafa makarantar boko ta farko a shekarar 1909 a garin Sakkwato, amma bata samu karɓuwa ba sai aka ɗiɗe ta daga can aka yi Kano da ita, aka dasa ta a can sannan kuma aka raɗa mata suna; Makarantar Ɗanhausa. Gurbin wannan makaranta yana nan a Kanon Dabo cikin unguwar Nassarawa GRA wanda a yanzu ake kira da Gidan Ɗanhausa.

Ita kuwa kalmar boko, Farfesa Bunza (2002), cewa ya yi: "Ina ganin kalmar boko asalinta daga book yake". Wannan kuma saboda zamowar karatun da rubutun na boko duk a makaranta ake yin su, sannan kuma kowane ɗalibi yana da nasa littafin. Bayan haka kuma karatun farko da ake fara koyar da ɗalibai a makaranta shi ne sanin abubuwan da ke makaranta wanda kuma littafi, abu ne mai matuƙar muhimmanci a wannan fuskar. Abin nufi, littafi yana daga cikin muhimman abubuwan amfani a makaranta. Saboda haka Farfesa Bunza (2006), yake ganin cewa waccar kalma ta Turanci, wato book aka aro, aka lafazantar da ita zuwa Hausa kamar yadda ya ce: "Bahaushe ya Hausantar da ita a lafazance, ya yi mata ɗauri/ƙarin wasalin /o/ ga harafin /k/, ya bar gaɓoɓinta biyu yadda suke, ya ƙara wa gaɓar ƙarshe wasali da jan wasali irin na gaɓar farko. Kalmar ta tashi daga book ta koma /boo/ /koo/. A iya gwargwadon nazarin da na yi, a nan ne aka haifi kalmar boko".

Saboda haka rubutun da aka koya ko ake yi da harrufan Turawa sai ake kiransa da Rubutun Boko.

Tushe

Tushen wannan rubutu shi ne abjadin Turanci; wato harrufan Turanci aka ɗauka a taƙaice aka yi wurgi da wasu: PQVX, waɗanda Bahaushe bashi da muhallin amfani da su, sannan kuma aka ƙara wasu: Ƙ, Ɓ, Ɗ, ƘY, GW, 'Y da saransu waɗanda Bature bashi da su amma kuma suna da muhalli a Hausa.

Wannan rubutun da mai karatu yake karantawa, kyakkyawan misali ne na rubutun boko. Amma tun kafin samun wannan rubutu na boko, Bahaushe yana da salon rubutunsa ƙagagge daga abjadin Larabci, wanda ake kira Rubutun Ajami.

Yanzu kenan a taƙaice mun fahimci cewa, Rubutun Boko ya faro ne a cikin ƙarni na goma sha takwas, kuma Turawa ne da kansu suka fara yi. Bahaushe kuwa sai a farkon ƙarni na ashirin, bayan cin Ƙasar Hausa da yaƙi da Bature ya yi sannan ya san shi ya kuma fara amfani da shi.

Makarantar farko da aka yi a Ƙasar Hausa a Sakkwato aka fara ta amma ta haɗu da tangarɗar da dole ta saka aka mayar da ita Kano aka yi mata suna da Makarantar Ɗanhausa wanda yanzu kuma gurbinta ya zama Gidan Ɗanhausa wanda kuma shi ne matsugunnin Cibiyar Tarihi da Al'adu ta Jahar Kano.

Abjadin Turanci aka ɗauka, aka mayar da du na Hausa bayan an cire wasu waɗanda Bahaushe baya amfani da su sannan kuma aka ƙago wasu waɗanda Bahaushe yake da su shi kuma Baturen Babu.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Yahaya I. Y., Zariya M. S., Gusau S. M. da ‘Yar’aduwa T. M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun akandire 3. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Zarruƙ R. M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B. S. Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Ɗaya. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Zuwan Turawa


    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub