Sana'ar Kitso

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Kitso


Gabatarwa

Sana’ar Kitso sana’a ce ta mata zalla, kamar yadda sana’ar aski take ta maza zalla, sai dai cewa ita sana’ar aski tana ƙarƙashin wanzanci.

Mata, kan je wajen mace bayan sun tsefe gashin su ta rangaɗa musu kitso. Mai yin wannan sana’a ana kiranta da makitsiya.

Ana biyan su ladar aikinsu kodai ta hanyar basu kuɗi kai tsaye kamar yadda ake yi yanzu, ko kuma basu wasu kayayyaki kamar sabulu, turare, man shafawa da sauransu kamar yadda yake a tsohuwar al’adar Bahaushe.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub