Masu Bayar da Tarbiyya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Masu Bayar da Tarbiyya


Gabatarwa

Dukkan masana fannoni da fagagen nazarin ɗan’adam da suka haɗa da masana halayyar ɗan’adam (Psychologist), masana falsafa, masana kimiyyar walwala (sociologist), masana falsafar kyawawan ɗabi’u (Moral Philosophy), masana fannin jagoranci da bayar da shawara (Guidance and Counselling) da sauransu. Duk sun yarda cewa, iyali, al’umma da makarantu su ne ke da ruwa-da-tsaki wajen gina mutum; abin nufi, su ne masu bashi tarbiyya da ta shafi rayuwarsa baki ɗaya da ta haɗa da gangar jiki, ruhi, cuɗanya da kuma walwala.

Iyali

Kalmar iyali a Hausance tana ɗaukar ma’anoni guda biyu; tana ɗaukar ma’ana ta mata ko matar mutum. Sai kuma ma’ana ta biyu wacce ke nufin dukkan wanda nauyinsa yake wuyan mai gida.  Yanayin zamantakewar iyali, shi ke fassara yawan iyalan mai gida. A wannan gaɓar, ma’ana ta biyu za mu yi aiki da ita.

Iyali, su ne tubalin gina mutum a Ƙasar Hausa. Masu iya magana sun ce: “Salla daga liman take farawa”.

Idan muka ɗauki gida mai kakanni, mahaifa, yayye, da ƙannen mahaifi da kuma yayyen yaro, za mu taras cewa, kowane ɗaya daga cikinsu akwai tasa gudunmawa da yake bayarwa wajen gina kyakkyawar tarbiyyar yaro ko akasin haka.
Babban makamin gina ko ɗora yaro a kan tafarkin daidai, shi ne mahaifi da mahaifiya su zamo masu tarbiyya; babu ma kamar mahaifiya, domin ita jariri yake fara sani kafin kowa a duniya, sannan kuma ita tafi kowa kusa da shi tun daga samun ciki har zuwa shekarun yaye. Wannan lokaci kuwa, yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan’adam.

A wannan mataki, idan gida ya zama gidan tarbiyya mai kyau, to babu makawa za ka taras yaro ya tashi da kyakkyawar tarbiya a mafi rinjayen yanayi. Haka ne, ba a rasa waɗanda za su fanɗare, wannan ce ma ta saka masu iya magana suke cewa: “Albasa bata yi halin ruwa ba”. Abin nufi, yaro ya fito daga gidan mutanen kirki shi kuma ya zama fanɗararre. Allah ya kiyaye.

Saboda haka idan ya zama kowane ɗaya daga cikin iyali yana bayar da gudunmawar da ta kamace shi wajen gina yaro, to za ka samu yaro ya tashi abin yabo.

Al’umma

Abin da ake nufi da al’umma a nan shi ne jama’ar da ke wajen gida. Wanda a cikinsu ake samun maƙwabta, abokai, dangi, abokan iyaye da kuma sauran jama’ar da wata hulɗa za ta iya haɗa su da yaro kamar cinikayya da sauransu.

Kowane ɗaya daga cikin waɗannan rukunan jama’a, yana da tasa gudunmawa da yake bayarwa wajen gina tarbiyya a Ƙasar Hausa. A wannan rubutun, zan dunƙule su gida biyu: Manyan mutane da kuma abokai.

 1. Manyan Mutane: Manyan mutane a nan  na nufin duk wani mutumin da ya girmi yaro wanda yaron zai iya karɓar hani da horo daga hannunsa. Masu iya magana suna cewa: “Yaro na kowa ne”. Saboda haka a al’adance kuma a Hausance, da zarar yaro ya fita daga gida, ya zama abin kulawa da tattali ga duk wanda ya grime shi a wajen gida.

  Idan yaro zai aikata wani aikin da bai dace ba, to waɗanda suka girme shi za su hana shi kuma ya hanu. Sannan suna da dama ta saka shi aiki da kuma bashi gudunmawar da duk yake nema. An taɓa yin wani lokaci a baya a Ƙasar Hausa, wanda idan yaro ya fito daga gida, barci ne kawai yake mayar da shi gidansu. Duk gidan da ya faɗa za a yi masa wanka idan bai kai shekarun da zai yi da kansa ba, za a bashi abinci ya ci kamar a gidansu. Sannan kuma za a bashi kariya daga dukkan abin da zai cutar da shi. Kai a wasu lokutan ma duk gidan da dare ya ƙwace wa yaro, musamman a gidan da ake zuwa domin sauraron tatsuniya, to a nan yaro zai ɓingire sai gari ya waye.

 2. Abokai: Abokai ko sa’anni a Ƙasar Hausa, su ne waɗanda suke da shekarun haihuwa ɗaya. Amma duk da haka akwai bambanci a tsakanin waɗannan kalmomi guda biyu; wato aboki da sa’a. Aboki shi ne wanda ra’ayi ya zo ɗaya, shi kuwa sa’a shi ne wanda aka haifa a shekaru guda. Saboda haka akan yi abota da mutumin da ya girme ka a shekaru. Idan kuma abota ta yi nisa sai ta koma aminanta.

  A tsarin tarbiyya a Ƙasar Hausa, akwai abubuwan da a wajen abokai ake koyar su. Misali, jarumtaka. Cuɗanya da abokai ita ke gogar da mutum ya zama mai juriya tun yana ƙarami. Wasannin yara da ake yi, kusan duk idan muka bibiye su za mu taras cewa, cike suke da koyar da jarumtaka da kuma juriya. Mu ɗauki langa a misali, za mu ga cewa, wani guri ne mutum yake hanƙoron zuwa amma ga wasu jama’a sun tare shi sun ce ba zai je ba, to a haka zai yi ta haƙilo sai ya kai.

Makaranta

Ilimi Hasken Rayuwa, sannan kuma shi ne fitilar da ke haskakawa tunani duhun da zai samu kyakkyawar turbar da zai bi. Shi kuwa ilimi, ana samunsa ne a makaranta. Saboda haka dole ne duk yaron da ya kai shekarun zuwa makaranta a kai shi makaranta.

Tun shekaru sama da ɗari shida da hamsin da suka shuɗe, Bahaushe yana da makaranta da kuma tsarin karantarwa. Akwai makarantun allo dana ilimi da ake kai yara domin samun ilimi da aƙida.

Bahaushe ya samu ƙarin wani ilimi a shekaru ɗari da suka shuɗe sakamakon zuwan Bature Ƙasar Hausa. Wannan ilimi kuma, shi Bahaushe ya kira da Karatun Boko wanda shima ya zo da nasa salo da tsare-tsare.

Saboda haka, makaranta muhalli ce mai matuƙar tasiri a rayuwar yaro. A wannan gaɓa ma, dole iyaye su riƙa lura da canjin halayya daga ‘ya’yansu tare kuma da sanin wacce irin makaranta ya kamata su kai ‘ya’yansu. Idan ya zama makarantar da za a kai yaro akwai tarbiyya, to ɗorawa kawai za a yi a kan ginin da aka fara daga gida. Amma idan akasin haka ne, to sai gini ya rushe.

Manazarta:


Abu Hamza B.D. (2013). Jawabin Darasin Aji Biyu na Babbar Sakandare. Kulliyatul Mu’allim Luggatul Arabiyya, Keffi, Jahar Nassara, Najeriya.

Abu Zakariyya I. (2007). Riyadhus-Salihiina. Darel Fikr Printers, Publishers and Distributors. Beirut-Lebanon.

Ɗan’abubakar U. (Babu Shekara). Buguyatul Muslimina Wal Kifayatul Waa’iziina Wal Mutta’iziin. Maɗaba’ar Alƙali Sharfi Bala, Kano, Najeriya.

Mesel B.D. (2015). Wittengenstein, Meta-Ethics and the Subject Matter of Moral Philosphy Ethical Perspective 22, no 1 (2015): 69 – 98. Center for Ethics, KU Leuven.

Rayner S. (2005). Hume’s Moral Philosphy. Manchester Journal of Philosphy Vol. 14: 185 eu 1, Article 2. An ciro daga shafin http://digital commons.macalester.edu/philo/vol14/iss1/2

Sayyadi A. (2004). Mukhtaril hadithun-nabawi wal hikimatul Muhammadiyya. Maɗaba’ar Alƙali Sharif Bala. Kano, Najeriya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantu 3. University Press PLC. Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Tarbiyya


  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub