Sana'ar Rini

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Rini


Gabatarwa

Sana’ar rini sana’a ce da ake canza launin tufafi zuwa wani launi ko kuma a yi ta mai launuka da dama kamar gaban hankaka a misalce. Idan mai kaɗi ta kaɗa zare, masu saƙa suka saƙa shi ya zama zani, sannan kuma maɗinka suka ɗinka ya zama tufafi, to sai a je kuma marina su rina shi zuwa launin da ake so.

Ba wai kawai suturar ake rinawa ba, a’a, akan ma rina shi kansa zaren kafin a saƙa, ko kuma kayan da aka saƙa ɗin kafin a ɗinka, ko kuma kayan da aka ɗinka.

Kayan Aiki

Katsi, kurada, ƙaro, makuba, muciya, kawatarniya, guga, itace, kutubi, baba, ƙaiƙayi, shuni, ruwa, marina, zarta, da sauransu.


Kwatarniya

Guri

Akan samu guri mai tudu wanda ba a zaton zuwan ruwa gurin sai a haƙa rijiyoyin da zurfinsu ya kai gaba uku ko huɗu, sannan a shafe bakinsu da makuba da katsi. Irin waɗannan gurare su ake kira karofi. Misali a garin Kano ta Najeriya akwai wani guri da ya shahara da wannan sana’a ta rini da ake kira Karofin Zage.


Marina
An ciro wannan hoto daga shafin: http://www.caboose.org.uk. A shekarar 2016.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Serɓices (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Kendal (2009). The Importance of Animals. An ciro daga https://www.toɗicology. org/pubs/docs/air/AIR_Final.pdf

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).

Zarruƙ R.M., Kafin-Hausa A.A. da Al-Hassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub