Hausa Saƙa

Me ka ke nema?


Shafin Farko  

Sana'ar Saƙa


Gabatarwa

Saƙa sana’a ce da ake sassarƙa abun saƙa wanda ka iya zama zare, gashi, ko kaba, domin saƙa sutura, ko shimfiɗa. Sutura a nan na nufin, riga wacce ka iya zama babba ko ƙarama, wando, hula, zani, ko mayafi da sauransu.

Sana’ar saƙa ta kasu kashi biyu: Akwai saƙar sutura, akwai kuma saƙar shimfiɗa. Saƙar sutura da zare ake yinta, ko gashi. Ita kuwa sana’ar saƙar shimfiɗa ana yinta ne da kaba, ko waninsu.

Masu sana’ar saƙa sutura suke saƙa riga, mayafi, zane, gyale, wando, hula, ko takalmi. Bayan zaren auduga da ake amfani da shi wajen saƙa, akwai kuma wata tsutsa da ake samu a jikin tsamiya wacce ke fitar da wani irin zaren da ake ɗinka siliki da ita.


Saƙar Tufafi

Masu sana’ar saƙa kayan shimfiɗa kuma su ke saƙa tabarma, malafa, lefe, dukuru, kwando, igiya, mangala, da sauransu.

Masaƙi A Masaƙa Yana Saƙa

Kayan Aikin Saƙar Sutura

  1. Gwafa: A jikinta ake tara zaren saƙa, haka nan kuma a jikinta ake ɗaura takala.

  2. Gwafa

  3. Ɗanƙwali: Ice ne na zamarƙe ake daddatsa shi. A jikinsa ake tara zare a saka a cikin ƙoshiya.
  4. Ƙoshiya: Ice ne na bagaruwa, ƙirya ko aduwa ake sassaƙe shi, a yi masa kwarmi a tsakiya. Da shi ake zuzzura zaren saƙa.

  5. Ƙoshiya

  6. Hanjin Ƙoshiya: Tsinke ne da ake zura shi a cikin ɗanƙwali bayan an naɗa zare a jikin ɗanƙwalin, sannan sai a maƙala shi a tsakiyar kwarmin ƙoshiya. Shi yake riƙe ɗanƙwalin a cikin ƙoshiya.
  7. Allira: A cikinta ake shirya zare. Sannan kuma ita ke sassarƙa zaren saƙar. Wato ana iya cewa ita ke yin saƙar. Allira guda biyu ce.
  8. Matsefi: Shi yake warware zaren da ake saƙa da shi, sannan kuma ya matse shi.

  9. Allirori da Matsefi (na 4 da na 5)

  10. Kunkuru: Dutse ne da ake danne ƙarshen zaren saƙa da shi.

  11. Kunkuru

  12. Takala: Ice ne da ake ɗauro shi daga jikin gwafa. A jikinsa ake nannaɗe ainihin saƙar da aka yi.

  13. Takala

  14. Cakarkara: Ƙarfe ne da ke jan allira sama ko ƙasa bayan an taka mataki.
  15. Bidan Tuƙi: Ƙarfe ne dogo mulmulalle kuma siriri. Ana saka shi a jikin takala sannan ya dire har ƙasa. Idan aka ɗago shi sama sai abin da aka saƙa ya naɗe a jikin takala, sannan kuma zaren saƙar ya jawo kunkuru ya kusanci mai saƙa, har zaren ya ƙare.

  16. Bidan Tuƙi

  17.  Gwauro: Tsawon zaren saƙa ne da yake ɗauka daga farkon rumfa har zuwa kan kunkuru.
  18.  Mari: Shi ne sashen da ake gudanar da saƙar da shi wanda ya tattare allirori, matsefi, cakarkara, mataki, bidan tuƙi, da sauransu.

  19. Mari

  20. Mazauni: Dukkan abin da masaƙi zai iya zama a kansa kamawa tun daga turmi, kututture, da sauransu.
  21.  Mataki: Itatuwa ne guda biyu, a jikinsu ake ɗaura allira, ɗaya daga dama, ɗaya kuma daga hagu, sannan sai a ɗaura allirorin a jikin cakarkara. Idan aka taka na dama, sai allira guda ɗaya ta yi sama, idan kuma aka taka ta hagu, sai ɗaya allirar ta yi ƙasa. Wannan sama da ƙasa da allirorin ke yi, shi yake sassarƙa zaren, sai saƙa ta samu.

  22. Mataki da Mazauni (13 da 14)

  23. Ɗantariya: A jikinsa ake zura ɗanƙwali sai a tara zare a jikin ɗanƙwalin.
  24.  Masaƙa: Gurin da ake yin saƙar. Haka nan rumfar da ake yin saƙar ma suna kiranta da masaƙa.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Madauci I. Isa Y. da Daura B. (1968) Hausa Customs. Northen Nigerian Publishing Company. Zaria – Nigeria.

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).

Tattaunawa a Ranar Laraba 9/11/2016 da Malam Usaini na Idi da ke Unguwar Mabuga a Garin Garji/Kadage, Ƙaramar Hukumar Minjibir, Jahar Kano, Tarayyar Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub