Sana'ar Sassaƙa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Sassaƙa


Gabatarwa

A cikin sauƙaƙƙiyar Hausa, muna iya kiran sassaƙa da kafintanci. Sassaƙa sana’a ce da ake fiƙe itace ko a kankare shi don a mayar da shi abin amfani. Masu yin wannan sana’a su ake kira masassaƙa.

Masassaƙi Yana Sassaƙa

Kayan Aiki

Kayan aikin sassaƙa basu da yawa, suna amfani da wuƙa, adda, gatari, zarto, itace, da gizago, da makankari da sauransu.


Gizago

Gatari

Adda

Kayayyakin da Suke Yi

Masu sassaƙa suke samar da kayan amfani da suka haɗa da: kujerar zama, turmin daka, taɓarya, ƙota (hannun riƙe kayan aiki irin su wuƙa, lauje, fartanya, da sauransu), ƙyaure (marufin ƙofa), akushi; ana zuba abinci ko abin sha kamar tuwo da miya, kunu, d.s. a cikinsa, kwacciyar sirdi, allo, da sauransu.

  1. Turmi da Taɓarya
  2. Ƙotar Gatari
  3. Akushi/Akwashi

  4. Akushi, ana zuba abinci ko abun sha a cikinsa

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare. Northern Publishing Company, Zaria-Nigeria.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub