Hausa Su

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Su


Gabatarwa

Sana’ar su ita ce sana’ar kamun kifi da sauran namun cikin ruwa. Akan shiga ruwa kodai kai tsaye a yi amfani da hannu ko kuma ta hanyar amfani da wani abu domin kama kifi a ci ko a sayar. Wannan sana’a ta kamun kifi tana daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa. Mai yin wannan sana’a shi ake kira masunci; jama’unsu kuma a ce ‘masunta’. Ana gudanar da sana’ar kamun kifi a cikin kogi, tafki, ƙorama, gulbi, injari da sauran guraren wucewa da kuma taruwar ruwa.

Tasirin da sana’ar su take da shi a ƙasar Hausa ya saka suma suna da sarkin ruwa. Sannan kuma suna bukukuwa irin nasu. Masunta kan jefa ‘ya’yansu a cikin ruwa su yi kwana-da-kwanaki a ciki ba tare da sun ciro ba.

Kayan Aiki

Muhimman kayan aikin su, sun haɗa da:

  1. Ƙugiya: Ana kafa ta a cikin ruwa a lanƙaya wani abu da kifi zai ci a jikinta, sai a baza ta a cikin wani yanki na ruwan da ake son kama kifin a ciki.
  2. Mali: Abu ne da ake yinsa da itace da raga ta zare. Ana tsoma shi a cikin ruwa, idan kifaye suka shiga ciki sai a fito da shi a kwashe.
  3. Kalli: Shima dai kamar sauran kayan kamun kifi, raga ce ta zare ake kafewa a cikin ruwa, sai a ja ta zuwa wani gefen, idan kifaye suka taru a ciki sai a fito da su a adana.
  4. Birgi: Raga ce ta zare, wacce ake cin bakinta da dalma. Shi kuma birgi watsa shi ake yi a cikin ruwa, sai dalmar ta shiga cikin yashi ta kafe. Duk kifin da ya shiga ciki baya iya fita, idan suka shiga ciki suka taru, sai a janye shi zuwa gaɓar ruwa a firfito da su a adana.

  5. masunci yana riƙe da Birgi a cikin kogi

  6. Fatsa: Ita fatsa ƙugiya ce guda ɗaya ko biyu ake ɗaurawa a jikin sanda, sai a lanƙaya wani abincin da aka san kifi yana so, da zarar ya haɗiyi wannan abinci sai ƙugiyar nan ta maƙale masa a wuya, sai a fizgo da ƙarfi a wullo shi wajen ruwa a kama.
  7. Dalla: Ita ma dalla raga ce ta zare, wacce ake riƙe gefe da gefenta, sai mutane su ratsa cikin ruwan suna ja. Duk kifin da suka tokare shi to ba zai iya wucewa ba. Can zuwa wani lokaci sai su nannaɗe ta da kifayen a ciki su fita da ita wajen ruwa sai su ciccire kifin.
  8. Koma: Ita kuma koma jaka ce ta raga da ake yiwa ƙaton baki. Riɓi biyu ake yinta. Ana riƙe kowace ɗaya da hannu ɗaya. Wato ɗaya a dama ɗaya kuma a hagu. Idan aka shiga ruwa da ita sai a riƙa tafiya, can kuma sai a haɗe bakin a fitar waje.
  9. Gora: Ita kuma gora hawa kanta ake yi ana iyo a cikin ruwa domin zuwa gurin da aka kafa mali, birigi ko makamantansu.

  10. Masunci a kan Gora

  11. Kwale-kwale: Abin sufuri ne a cikin ruwa.

  12. Mawallafin wannan shafi a cikin Kogin Kaduna a shekarar 2016.

Al’adu

Masunta suna da al’ada ta gudanar da bikin kamun kifi. Misali, a Najeriya akwai bikin kamun kifi na Argungun da ake yi shekara-shekara.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Madauci I., Isa Y., da Daura B. (1968) Hausa Custom. Northern Nigerian Publishing Compnay, Zaria-Nigeria.

Yakasai K.I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cikinsa (Babu Sunan Maɗaba’a).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub