Sana'ar Ginin Tunkwane

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Ginin Tukwane


Gabatarwa

Ginin tukwane kamar yadda sunan ya gabata, sana’a ce da masu ita ke gina kayayyakin amfanin gida da suka haɗa da tunkuya, randa, buta, tulu, kasko, asusu, da abubuwan da suka yi kama da haka. Ana gudanar da wannan sana’a ne da ƙasa (taɓo), sannan a gasa ta da wuta.

Alhassan, Musa, da Zarruƙ (1982), sun bayyanata a matsayin reshe ta sana'ar gini. Wato kenan sana'a ce da ta faɗo cikin rukunin sana'ar gini.

Matakai:

 1. Farko za a fara haƙar ƙasa.

 2. Gurin Haƙo Ƙasar Gina Tunkuya

 3. Sannan a kwaɓa ta.

 4. Ana kwaɓa ƙasar gina tunkuya


  Kwaɓaɓɓiyar ƙasar gina tunkuya; ana kiranta Moli

 5. Sannan a gina tukunyar da sauran dangoginta.

 6. Ana gina tukunya

 7. Sai kuma a barta ta sha iska.
 8. Sannan kuma a gasa ta da wuta.

 9. Gurin gasa tukunya. Amma wasu sukan yi amfani da rami.


  Gasasshiyar Tukunya

 10. Sannan a gyara ta.

 11. Gyararriyar Tunkuya.

Ita wannan sana'a ta ginin tukwane ba kasafai ake yinta da damina ba. Sana'ar rani ce.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Yakasai K.I. (Babu Shekarar Bugu). A San Mutum A Kan Sana'arsa, (Babu sunan gurin ɗab'i).

Ziyarar gani da ido zuwa wani ƙauye a cikin ƙaramar hukuma Bichi ta jahar Kano a Najeriya ranar 20/5/2016.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub