Amfanin Kwamfuta
Gabatarwa
Amfanin kwamfuta a yau wani abu ne da ke da wahalar ƙididdiguwa, saboda kusan babu wani ɓangare na rayuwa da kwamfuta ba ta shafa ba, kaɗan daga cikinsu su ne:
- Ilimantarwa: Kwamfuta wata babban makami ce ta samun ilimi wacce ke baiwa mai amfani damar zama tutur yana karatu da ita ba tare da ƙosawa ba. Ana samun wannan ta hanyar amfani da furogiram ɗin da aka shirya domin ilimantarwa misali, softuwayar Maidarasu wacce za ta baka damar koyon karatun alƙur’ani, littattaffai, sanin tarihi, koyon ibada dama sauran fannonin ilimin addinin Musulunci duka cikin harshen Hausa.
- Nishaɗantarwa: Ana amfani da kwamfuta wajen samun nishaɗi, misali, kallon fim, sauraron waƙoƙi, d.s.
- Adana Bayanai: Ana amfani da kwamfuta wajen adana bayanai, wani babban muhimmanci da kwamfuta ke da shi a nan fiye da komai wajen adana bayanai shi ne bayar da bahasi nan take.
- Nazari da Bincike: Ana amfani da kwafutoci wajen gudanar da nazari da bincike a kowane fanni na ilimi.
- Gwaje-Gwajen Kimiyya da Fasaha: Ana amfani da kwamfuta wajen gudanar da gwaje-gwajen kimiyya da fasaha don gano wasu abubuwa. Kamar gano ko akwai wani nau’in ma’adani a guri.
- Aune-Aunen Kimiyya: Ana amfani da kwamfuta a asibitoci don gwada jini, fitsari, d.s.
Kwamfuta na kula da maras lafiya
An ciro daga: www.heraldextra.com - Sadarwa: Ana amfani da kwamfuta wajen sadarwa.
- Sana’o’i: Kwamfuta wata kafa ce da ta samar da guraben sana’a, wanda hatta matayen da ke cikin gidajensu na aure za su iya amfani da wannan dama wajen samun kuɗaɗen shiga.
Ɗalibai suna aiki da kwamfuta
An ciro daga: www.schoolsworld.tv
Yanna kallon wasan-kwaikwayo a kwamfuta domin sanun nishaɗi.
An ciro daga: www.patriyaasia.blogspot.com
Manazarta:
Tsangarwa A.M. (2010). Kwamfuta a Sauƙaƙe, Sabon Bugu. Tsangarwa ICT Limited, Kano-Nigeria.
Darrusan Kwamfuta
Kwamfuta
- Amfanin Kwamfuta
- Siffofin Kwamfuta
- HTML
- Algorizim
- Ofareshin Risac
- Makirosoft Eksel
- Fesbuk
- Bulog
- Burawuza
- Aikin Gona
- Kiwon Kifi
- Dabbobi
- Ɗakin Karatu
- Ɗakin Karatun Congress
- Adabin Turanci
- Nahawun Turanci
- Wasika-Turanci
Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin