Garin Namaran

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Garin Namaran


Gabatarwa

Namaran gari ne a cikin ƙaramar hukumar Kanam ta jahar Plateau. Shekaru sama da 500 da suka shuɗe wani maharbi mai suna Nimmam ya kafa wannan gari wanda daga baya aka riƙa kiran garin da sunansa amma a jikirce.

Kafuwa

Wani maharbi mai suna Nimmam, ɗan asalin garin Zinn, wacce a yanzu ta ke cikin ƙaramar hukumar Lantang ta arewa, a cikin jahar Plateau a Tarayyar Najriya, shi ya kafa wannan gari. Tun da farko, mahaifan Nimman su suka tashi daga garinsu na asali mai suna Tal, wanda shi ma yanzu ya ke cikin ƙaramar hukumar Pankshin ta jahar Plateau, suka koma Zinn ɗin da zama, inda suka haifi Nimman da sauran ‘yan’uwansa a garin.

Bayan da Nimmam ya girma, sai ya riƙi harbi a matsayin sana’arsa. A cikin irin yawace-yawancensa na harbi sai Allah ya kai shi wani dutse wanda ya ga cewa wannan dutse ya yi masa daidai da rayuwa a wajen. Kasantuwar akwai namun daji a gurin. Saboda haka ya share waje ya zauna a kan wannan dutse shi da iyalansa.

Sannu a hankali, Nimman ya riƙa kashe dabbobin daji yana ci tare da iyalansa sannan kuma yana adanawa. Kasantuwar wannan dutse mai tsawon da ake iya hango shi daga garuruwan nesa musamman da daddare idan sun kunna wuta domin ganin haske, sai jama’a suka fara zuwa kan wannan dutse domin ganin abinda ke gudana ko kuma wanda ke raye a wajen.

Nimman, mutum ne mai karɓar baƙi, saboda haka duk mutanen da suka zo, sai ya ɗebo nama daga cikin irin waɗanda ya ke adanawa ya basu. Wasu idan suka karɓa, sai su yi godiya su ƙara gaba, wasu kuma sai su share guri su zauna tare da iyalansu, sun samu garin rayuwa. A kwana a tashi wannan dutse ya zama gari. Saboda haka sai aka riƙa kiran wannan dutse da Dutsen Nimmam.

Suna

Jama’ar da suka riƙa zuwa ƙungiya-ƙungiya, suna zama a kan wannan dutse tare da mazauninsa na farko, wato Nimmam, sai furta sunansa ya wuyata ga wasu ƙabilun suka riƙa kiransa da Namwang. Da Hausawa suka yawaita a wannan gari, bayan jahadin Shehu Ɗanfodiye, suma sai furta kalmar ta yi nauyi a bakinsu. Saboda haka sai suka riƙa kiran garin da Namaran kai tsaye, wanda daga bisani da Turawa suka zo suma suka karɓe shi yadda Bahaushe yake furtawa. Saboda haka sai wannan suna ya zama shi ne sunan wannan gari a hukumance.

Bigire

Garin Namaran yana nan a Kudu-maso-yammacin Ƙaramar Hukumar Kanam, a cikin jahar Plateau a Najeriya. Ya yi iyaka da Ƙaramar Hukumar Lantang ta Arewa daga Kudu-maso-yamma. Sannan kuma ya yi iyaka da Ƙaramar Hukumar Wase daga Kudu-maso-gabas.  

Manazarta:


Shehu A.Y. (2018). Out of Mountain A Dynasty Is Born. Yaliam Press Limited (Babu adireshi).



Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub