Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Dattawa ta NajeriyaHatimin Shugaban Majalisar Dattawa

'Yan Majalisar Dattawa Suna Gudanar da Zama a Zaurensu

Sandar Majalisa (Mace)

Gabatarwa

Majalisar Dattawa ta Tarayya wadda a Turance ake kiranta da House of Senate, ita ce majalisa ta ɗaya a daraja a tsarin siyasar Najeriya mai tagwayen zaurukan majalisu (Bicameral legislature) wanda aka gina a kan tsarin  dimokuraɗiyyar Amurka kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya na shekarar 1999 ya tanada; sashe na 47 ya nemi a kafa Majalisar Dokoki mai tagwayen zauruka; Zauren Majalisar Dattawa da kuma Zauren Majalisar Wakilai.

Shugaban Majalisa, wanda a Turance ake kira Senate President, shi ne jagoran zauren wannan majalisa ta Dattawa wadda take da wakilai ɗari da tara da suka fito daga jahohin Najeriya talatin da shida da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Mambobin Majalisa

Majalisar Dattawa ta Tarayya tana da mambobi 109 da suke wakiltar jahohi 36 da kuma babban Birnin Tarayya, Abuja. Kowace jaha tana bayar ba wakilai uku in banda babban Birnini Tarayya, Abuja da take da wakilcin dattijo ɗaya rak.

Tsayawa Zaɓe

Sashe na 65 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya na shekarar 1999, ya zayyana cewa duk mai son tsayawa takarar zama ɗan Majalisar Dattawa a Najeriya dole ne ya zama:

 1. Haifaffen ɗan Najeriya;
 2. Yana da shekaru 35 da haihuwa;
 3. Cikakkiyar shedar kammala karatun sikandire ko madadinta;
 4. Zama ɗan jama’iyyar sisayasa mai rajista tare da amicewar jama’iyyar na ta  tsayar da shi takara a ƙarƙashin tutarta.

Zaman Majalisa

Kudin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, sashe na 63 ya bayyana cewa majlisar Dattijai za ta gudanar da zama ɗai-ɗai-ɗai har guda ɗari da tamanin da ɗaya a kowace shekara. Kenan, a iya tsawon rayuwarta za ta zauna sau ɗari bakwai da saba’in da huɗu.

Cancantar Shiga Zaman Muhawara

Sahe na 52, ƙaramin sashe na (1), na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya na shekarar 1999 ya tanadi cewa, kafin kowane ɗan majalisa ya samu damar shiga zaman muhawara a Zauren Majalisar Dattawa, dole sai ya:

 1. Bayyana kadara da bashi ko nauyin da yake kansa;
 2. Rantsuwar Mubaya’a a gaban shugaban Majalisa;
 3. Rantsuwar zama wakili a gaban shugaban Majalisa.

Amma kafin yin dukkan waɗannan zai zaɓi shugaban majalisa da mataimakinsa domin samun jagoranci.

Rantsuwar Mubaya’a

Ni ………………………………………… na rantse, na tabbata zan kasance mai biyayya tsakani da Allah, biyayya kuma cikakkiya ga Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, kuma zan mutunta, zan tsare, na kuma kare Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.
Ya Allah ka taimake ni.

Rantsuwar Kama Aiki

Ni …………………………………… na rantse, na tabbata zan kasance mai biyayya tsakani da Allah, biyayya kuma cikakkiya ga Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; kuma a matsayina na ɗan Majalisar Dattijai………………………..; zan yi aikina gwargwadon iko kuma bisa gaskiya kamar yadda Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya da kuma doka suka zayyana da kuma ƙa’idojin Majalisar Dattijai…………………………..; sannan koda yaushe zan kula da ɗiyaucin Najeriya, kasancewar ta ƙasa ɗaya, haɗin kai, zaman lafiya da yalwar arziƙin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; zan tsaya tsayin daka wajen ganin Najeriya ta cim ma manyan burace-buracenta tare da manyan manufofinta kamar yadda suke a Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; kuma zan yi iyakar bakin ƙoƙarina, na mutunta, kare, tare kuma da tsare Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, sannan zan kiyaye ƙa’idojin kyan hali na ma’aikaci da aka shimfiɗa a rataye na biyar na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.
Ya Allah ka taimake ni.

Shugabancin Zama

Sashe na 53, ƙaramin sashe na (1), tanadi na (a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadi cewa shugaban Majalisar Dattawa shi ne zai jagoranci dukkan zaman Majalisa sai dai idan baya nan mataimakinsa ya kama.

Zaman Haɗin Guiwa

Zaman haɗin guiwa shi ne zama tsakanin tagwayen Zaurukan Majalisun Tarayya a lokaci guda kuma a waje guda.

Shugabancin Zaman Haɗin Guiwa

Sashe na 53, ƙaramin sashe na biyu na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya na shekarar 1999 ya bayyana cewa, shugaban Majalisar Dattawa ne zai jagoranci zaman haɗin guiwar tagwayen majalisu. Idan kuma baya nan sai Kakakin Majalisar Wakilai ya jagoranta, idan kuma duka biyun basa nan to sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya jagoranta, idan shi ma baya nan to sai Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ya jagoranta. Idan kuma duka babu ɗaya, to sai Majalisar Dattawa ta wakilta, idan haka bata yiwu ba, sai Majalisar Wakilai ta wakilta idan kuma duk hakan bata samu ba, to sai mahalarta zaman su wakilta wanda zai jagoranci zaman.

Wakilci

Sashe na 48 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya wallafar 1999 ya zayyana cewa Majalisar Dattawa za ta ƙunshi Dattawa uku-uku daga kowace jaha da kuma ƙarin wakili ɗaya daga babban birnin Tarayya.

Shugabanci

Majalisar wakilai ta Tarayyar Jamhuriyar Najeriya tana da manyan jami'ai kamar haka:

 1. Shugaban Majalisa (President).
 2. Mataimakin Shugaban Majalisa (Deputy President).
 3. Shugaban Masu Rinjaye (Majority Leader).
 4. Shugaban Marasa Rinjaye (Minority Leader).
 5. Babbar Bulaliyar Majalisa (Chief Whip).
 6. Ƙaramar Bulaliyar Majalisa (Minority Whip).
 7. Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye (Deputy majority leader).
 8. Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye (Deputy Minority leader).
 9. Mataimakin Babbar Bulaliyar Majalisa (Deputy Chief Whip).
 10. Mataimakin Ƙaramar Bulaliyar Majalisa (Deputy Minority Chief Whip)

Manazarta


Ikenwa C. (2019). Full List of Nigeria's Senat Presidents Till Date. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://nigerianinfopedia.com.ng/full-list-of-nigerias-senate-presidents-till-date/

National Assembly (2019). Federal Republic of Nigeria, National Assembly, An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.nassnig.org/

Wikipedia (2019), List of Senate Presidents. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/President_of_the_Senate_of_Nigeria


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Majalisun Tarayya:

Shugabannin Majalisar Dattawa

 • Ahmed Lawan
 • Bukola Saraki
 • David Mark
 • Ken Nnamani
 • Wabara
 • Pius Anyim
 • Okadigbo
 • Evan Enwerem
 • Ameh Ebute
 • Iyorchia Ayu
 • Joseph Wayas
 • Nwafor Orizu
 • Dennis Osadebay
 • Nnamdi Azikiwe

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub