Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Tarayyar NajeriyaGabatarwa

Majalisar Tarayya ɗaya ce daga cikin turaku uku na Gwamnatin Tarayyar Najeriya; Tsagin Gudanarwa (Executive), Dokoki (Legislative) da kuma Shari’a (Judiciary) wadda nauyin yin dokoki ya hau kanta a bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.

Sashe na 47 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya shi ya nemi a kafa Majalisar Dokoki ta Tarayya mai tagwayen zauruka; Zauren Majalisar Dattawa da kuma Zauren Majalisar Wakilai.

Ayyukan Majalisa

Babba, sannan kuma muhimmin aikin Majalisar Tarayya shi ne yin dokoki kamar yadda ya zo a sashe na 4, ƙananan sassan da suka zo a ƙasansa, a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 cewa:

 1. Ikon yin doka da ta shafi Tarayyar Jamhuriyar Najeriya yana hannun Majalisar Dokoki ta Tarayya, wato majalisun Majalisar Dattijai da ta Wakilai.
 2. Majalisar Dokoki ta Tarayya tana da ikon yin doka domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da mulkin adalci a duk faɗin Tarayyar Najeriya, ko wani ɓangare na Tarayyar kamar yadda aka kawo da sunan Keɓantattun Ayyukan Tarayya waɗanda aka bayyana su a Kashi na 1, rataye na biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (An zayyano su a ƙasa).
 3. Ikon Majalisar Tarayya da ke cikin keɓantattun ayyukan Gwamnatin Tarayya na yin doka domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da mulkin adalci, nata ne ita kaɗai, sai dai a guraren da wani tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa majalisun jahohi ikon tsoma baki.
 4. Ƙari a kan abin da aka ambata a ƙaramin sashe na (2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya shi ne cewa, Majalisar Tarayya tana da ikon yin doka a kan waɗannan al’amura kamar haka:
 5. Ayyukan da ke cikin jerin ikon da Gwamnatoci suka yi tarayya waɗanda aka jera a Kashi na II na Rataye na Biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wallafar 1999 (An jero su a ƙasa).
 6. Duk wani abu wanda aka ba ta ikon kafa doka a kansa a cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Keɓantattun Ayyukan Majalisar Tarayya

Ya zo a Kashi na I, Rataye na Biyu, na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ita ke da alhakin:

 1. Ƙididdige asusun gwamnatin Tarayya, ma’aikatu, kotuna da hukumomi tare da tantance shigi da ficin kuɗaɗen.
 2. Lura da shigowar makamai da suka haɗa da bindigogi, harsasai da kuma nakiyoyi.
 3. Lura da harkokin jiragen sama da na ruwa ta fuskacin ingancin jiragen, da kuma tashoshinsu.
 4. Lura da harkar bayar da lambobin girmamawa da na yabo.
 5. Lura da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da kuma tarin bashi.
 6. Kula da harkokin bankuna da suka danganci ajiya, canjin kuɗi da takardun bashi.
 7. Lura da rancen kuɗaɗe da gwamnatin Tarayya ko na Jahohi za su yi a ciki da wajen ƙasa.
 8. Harkokin ƙidayar jama’a da ya haɗa da rajistar haihuwa, lura da yawan jama’a a-kai-a-kai da kuma rajistar mutuwa a duk faɗin tarayya.
 9. Lura da harkokin zama ɗan ƙasa, canjin asali da kuma walwalar baƙi.
 10. Saka ido a kan harkokin cinikayya, sana’o’i, kasuwancin haɗin guiwa da kuma dukiyar amana.
 11.  Kula da hanyoyin gwamnatin tarayya ta fuskacin gina wasu da kuma tattalin waɗanda ake da su.
 12. Ƙayyade girman jari.
 13.  Haƙƙin mallakar wallafa da kuma tsarawa.
 14.  Ƙirƙirar sababbin jahohi.
 15.  Saka ido a harkar tsaron ƙasa.
 16.  Fitar da baƙin haure daga Najeriya.
 17. Samar da hanyoyin kashe kuɗaɗen wata gidauniya.
 18.  Wakilcin hulɗa da kuma cinikayya.
 19.  Lura da harkokin magunguna da kuma dafi.
 20.  Lura da harkokin zaɓen Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnonin Jahohi, Mataimakan Gwamnoni da dukkan sauran muƙaman da Kundin Tsarin Mulki ya bayar da damar a tsaya takara in banda na Shugabannin Ƙananan Hukumomi da ma duk wani muƙami da yake ƙarƙashin ƙaramar hukuma.
 21.  Bayar da shaida.
 22.  Lura da harkar canjin kuɗi.
 23.  Lura da lamuran tarkardun kuɗi, tsabar kuɗi da kuma takardun cinikayya.
 24. Lura da harajin fitar da kayayyaki wajen ƙasa.
 25.  Kuɗin fito (Harajin shigo da kayayyaki) da harajin kayan da aka sarrafa a cikin gida.
 26.  Lura da hulɗa da ƙasashen waje.
 27. Lura da shiga da kuma fita daga ƙasar Najeriya.
 28. Miƙa mai laifi ga ƙasar da ya yi wa laifi idan akwai buƙatar hakan.
 29.  Ɗaukar hoton yantsun mai laifi, tantance mai laifi tare da adana tarihin laifin nasa.
 30.  Sana’ar kiwo da kuma kamun kifi amma banda kiwo da kamun kifi a koguna, tafkuna, kwarurruka, kududdufai da sauran ruwayen da ke cikin Najeriya.
 31.  Aiwatar da yarjejeniyoyin da aka ƙulla da suka shafi wani batu da aka lissafa a nan.
 32. Kafawa, kulawa da kuma rufe kamfanoni amma banda na ƙungiyoyin taimakon juna, majalisun ƙananan hukumomi da kuma ƙungiyoyin da majalisun dokokin jahohi suka kafa bisa doka.
 33. Harkar Inshora.
 34. Ƙwadago, da abin da ya shafi ƙungiyoyin ma’aikata, alaƙar masana’antu, dokoki, kariya da kuma walwalar aiki, rigingimun kamfani, ƙayyade mafi ƙarancin albashi ga Tarayya ko wani reshenta da kuma sasanton rikice-rikecen ƙwadago.
 35.  Sasanta rigima tsakanin jaha da jaha, Gwamnatin Tarayya da jaha, tsakanin hukomomi ko kuma ɗaiɗakun mutane.
 36. Harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa da suka haɗa da:
  • (a)Tuƙi da zirga-zirga a teku;
  • (b) Tuƙi da zirga-zirga a Kogin Neja da sauran kogunan da suke faɗawa cikinsa da ma sauran dukkanin kogunan da Majalisar Tarayya ta ke gani a matsayin kafar zirga-zirga a tsakanin jahohin Najeriya ko kuma ƙasashen waje.
 37.  Harkokin sanin yanayi.
 38.  Sojoji (Na ƙasa, ruwa da sama) da ma dukkan sauran rassan rundunonin mayaƙan Tarayya.
 39.  Haƙar ma’adanai da suka haɗa da haƙo mai, gudanar da binciken gano arziƙin ƙarƙashin ƙasa da iskar gas da ke ƙarƙashin ƙasa.
 40. Guraren Hutawa da Majalisar Tarayya ta ware a matsayin guraren hutawa koda sun zamo wasu yankuna a wata jaha kamar yadda za ta iya faruwa, tare da sanin gwamnan jaha.
 41.  Makamashin Nukuliya.
 42.  Fasfo da biza.
 43. Rijistar haƙƙin mallakar ƙirƙira, tambarin kamfani, sunan sana’a ko kasuwanci, ƙawa kan kayan masana’antu da kuma alamar kaya.
 44. Fansho, giratuti ko kuɗin sallamar aiki da aka yi amfani da asusun Tarayya ko kuma daga wani kuɗin Gwamnatin Tarayya.
 45. ‘Yansanda da sauran jami’an tsaro na Gwamnati waɗanda doka ta kafa.
 46.  Gidan-waya, hanyar sadarwa ta telegiraf da kuma wayar tangaraho.
 47.  Ikon Majalisar Ƙasa, alheri da kuma kariyar wakilci.
 48. Gidajen Yari.
 49.  Sana’a ta aiki da ilimi kamar yadda Majalisar Ƙasa za ta iya fayyacewa.
 50. Bashin da yake kan Tarayyar Najeriya.
 51.  Ranakun hutu na Gwamnati.
 52.  Ayyukan hulɗa da jama’a na Tarayya.
 53.  Aikace-aikacen Tarayya har da sasanta saɓanin da ya shiga tsakanin Gwamnatin Tarayya da ma’aikatanta.
 54.  Keɓantattun ayyukan kawar da annoba.
 55.  Tashoshin jiragen ƙasa.
 56. Saka ido kan jama’iyyun siyasa.
 57. Aiki da umarnin kotu kan wani saɓani ko laifi, hukunci, oda ko wani umarni na wata kotu wadda ba ta Najeriya ba ko kuma wata kotu a Najeriya wadda ba Majalisar Dokokin wannan jahar ce ta kafa ba.
 58.  Haraji da aka aza wa waɗansu kaya waɗanda Gwamnati ta san da zaman su.
 59. Haraji kan samu da ake yi, riba da alheri kan uwar kuɗi, sai ko a irin waɗanda wannan Tsarin Mulkin ya ɗage biya.
 60. Kafa hukumomi na Tarayya ko na wani ɓangare domin a:
  • (a)Haɓɓaka da kuma ƙarfafa aiki da babban buri da kuma manufa kamar yadda lamarin yake ƙunshe a Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Najeriya.
  •  (b)Ganowa, tarawa, adana kayan tarihi, rubuta al’amuran da suka faru,  rubuta sassa masu birbishin kayan tarihi na ƙarƙashin ƙasa da duk abubuwa waɗanda Majalisar Ƙasa ta ɗauka ana iya tinƙaho da su ko kuma muhimmai ne ga ƙasa (A fannin tarihi).
  • (c)Lura da gidajen ajiye kayan tarihi, ɗakunan karatu amma banda waɗanda gwamnatin jaha ta kafa.
  • (e)Saka ido kan kwararowar masu ziyara da kuma
  • (f)Ƙayyade mafi ƙarancin zurfin ilimin da ya kamata a samu daga firamare zuwa jami’a.
 61. Ɗaurin aure, kashewa da kuma rabuwa banda auren da aka yi bisa tafarkin Islama da aurace-auracen gargajiya da duk maganar da ta shafi mace da miji.
 62. Kasuwanci da cinikayya, musamman ma:
  • (a)Saye da sayarwa tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen duniya har da shigi da ficin kaya daga Najeriya da kuma saye da sayarwa tsakanin jahohi;
  • (b)Kafa hukumar da za ta lura da ciniki, wadda za a ba ta ikon sayar da amfanin gona na Najeriya a waɗansu ƙasashen waje kamar yadda Majalisar Ƙasa za ta iya ƙayyadewa;
  • (c)Duba amfanin gona waɗanda za a fitar da su waje daga Najeriya sannan da kimanta darajar waɗannan kaya da aka duba;
  • (d)Kafa wata hukuma wadda za ta kimanta daraja da kyawun kaya da aka yi tanadi domin sayarwa;
  • (e)Ƙayyade farashin haja wadda Majalisar Ƙasa ta zartar da hukuncin cewa kaya ne na masarufi;
  • (f)Rijistar kamfani.
 63. Zirga-zirga a manyan hanyoyin mota mallakar Tarayya.
 64. Tafiyar ruwa a kan kogin da Majalisar Ƙasa ta yanke shawarar cewa ba mallakar jaha guda ba ne.
 65. Mizanin aune-aune da gwaje-gwaje.
 66.  Hanyar sadarwa maras waya, radiyo da talabijin in banda waɗanda Gwamnatin Jaha ta kafa; ƙayyade ƙarfin hanyar sadarwa maras waya, radiyo da talabijin.
 67.  Kowane irin batu wanda tanade-tanaden wannan Tsarin Mulki ya bai wa Majalisar Ƙasa damar yin doka a kai.
 68. Kowane batu da ya taso ko ya shafi ɗayan batutuwan da aka ambata a baya (Duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wallafar 1999 domin ƙarin bayani).

Daga abubuwan da        suka gabata, za mu fahimci cewa, Majalisar Dokoki ta Tarayya, ita ce tushen dukkan dokokin Najeriya, kuma duk wanda aka zaɓa domin ya wakilci jama’a a ɗaya daga cikin zaurukanta guda biyu, an zaɓe shi ne domin ya yi doka ba domin wani abu na daban ba.

Wannan, shi ne abin da ya samu dangane da bayani a kan Majalisar Dokokin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya. Cewa kuma, a duk lokacin da aka samu wani ci gaba, to za a sabunta wannan shafi cikin yarda da kuma taimakon Allah Maɗaukakin Sarki.

Manazarta


Ikenwa C. (2019). Full List of Nigeria's Senat Presidents Till Date. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://nigerianinfopedia.com.ng/full-list-of-nigerias-senate-presidents-till-date/

National Assembly (2019). Federal Republic of Nigeria, National Assembly, An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.nassnig.org/

Wikipedia (2019), List of Senate Presidents. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/President_of_the_Senate_of_Nigeria


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Majalisun Tarayya:

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub