Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Wakilai ta Najeriya


Hatimin Kakain Majalisar Dattawa

'Yan Majalisa Suna Gudanar da Zama a Zaurensu

Sandar Majalisa (Mace)

Gabatarwa

Majalisar Wakilai ta Tarayya wadda a Turance ake kiranta da National House of Representatives, ita ce majalisa ta biyu a daraja a tsarin siyasar Najeriya mai tagwayen zaurukan majalisu (Bicameral legislature) wanda aka gina a kan tsarin  dimokuraɗiyyar Amurka kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya na shekarar 1999 ya tanada.

Sashe na 47 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya nemi a kafa Majalisar Dokoki mai tagwayen zauruka; Zauren Majalisar Dattawa da kuma Zauren Majalisar Wakilai.

Kakakin Majalisa, wanda a Turance ake kira speaker, shi ne jagoran zauren wannan majalisa ta wakilai wadda take da wakilai ɗari uku da sittin da suka fito daga jahohin Najeriya talatin da shida da kuma babban birnin Tarayya, Abuja.

Mambobin Majalisa

Majalisar Wakilai ta Tarayya tana da mambobi 360 da suke wakiltar jahohi 36 da kuma babban Birnin Tarayya, Abuja. An rarraba yawan mambobin da kowace jaha za ta bayar ta hanyar la’akari da yawan jamar jahohin Tarayyar Najeriya; wato gwargwadon yawan jama’ar da jaha take da su, gwargwadon yawan wakilanta a Zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya abin da ya bai wa jahohin Kano da Lagos damar samun wakilai mafiya yawa a majalisar inda kowace ɗaya daga cikinsu take da wakilai 24, sai kuma Bayelsa da Nassarawa da suke da mafiya ƙarancin lamba da adadin wakilai biyar-biyar a saman Babban Birnin Tarayya mai wakilai biyu kacal. Ga su kamar haka:

 1. Abia                8
 2. Adamawa            8
 3. Akwa Ibom      10
 4. Anambra          11
 5. Bauchi           12
 6. Bayelsa           5
 7. Benue             11
 8. Borno            10
 9. Cross Rivers    8
 10. Delta             10
 11. Ebonyi           6
 12. Edo                9
 13. Ekiti               6
 14. Enugu             8
 15. Gombe           6
 16. Imo                 10
 17. Jigawa            11
 18. Kaduna              16
 19. Kano              24
 20. Katsina           15
 21. Kebbi             8
 22. Kogi               9
 23. Kwara            6
 24. Lagos             24
 25. Nassarawa     5
 26. Niger              10
 27. Ogun              9
 28. Osun              9
 29. Oyo                13
 30. Plateau           8
 31. Rivers             13
 32. Sokoto           11
 33. Taraba            6
 34. Yobe              6
 35. Zamfara             7
 36. FCT                2

Tsayawa Zaɓe

Sashe na 65 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya zayyana cewa duk mai son tsayawa takarar zama ɗan Majalisar Wakilai a Najeriya dole ne ya zama:

 1. Haifaffen ɗan Najeriya;
 2. Yana da shekaru 30 da haihuwa;
 3. Cikakkiyar shedar kammala karatun sikandire ko madadinta;
 4. Zama ɗan jama’iyyar sisayasa mai rajista tare da amicewar jama’iyyar na tsayar da shi takara a ƙarƙashin tutar jama’iyyar.

Zaman Majalisa

Kudin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, sashe na 63 ya bayyana cewa Majlisar Wakilai za ta gudanar da zama ɗai-ɗai-ɗai-ɗai har guda ɗari da tamanin da ɗaya a kowace shekara. Kenan, a iya tsawon rayuwar wa’adin mulkinta cikin shekaru huɗu, za ta zauna sau ɗari bakwai da saba’in da huɗu (774) kenan.

Cancantar Shiga Zaman Muhawara

Sashe na 52, ƙaramin sashe na (1),  na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadi cewa, kafin kowane ɗan majalisa ya samu damar shiga zaman muhawara a Zauren Majalisar Wakilai, dole sai ya:

 1. Bayyana kadara da bashi ko nauyin da yake kansa;
 2. Rantsuwar Mubaya’a a gaban Kakakin Majalisa;
 3. Rantsuwar zama wakili a gaban Kakakin Majalisa.

Amma kafin yin dukkan waɗannan zai zaɓi Kakakin Majalisa da mataimakinsa domin samun jagoranci.
Rantsuwar Mubaya’a

Ni ………………………………………… na rantse, na tabbata zan kasance mai biyayya tsakani da Allah, biyayya kuma cikakkiya ga Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, kuma zan mutunta, zan tsare, na kuma kare Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.
Ya Allah ka taimake ni.

Rantsuwar Kama Aiki

Ni …………………………………… na rantse, na tabbata zan kasance mai biyayya tsakani da Allah, biyayya kuma cikakkiya ga Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; kuma a matsayina na ɗan Majalisar Wakilan………………………..; zan yi aikina gwargwadon iko kuma bisa gaskiya kamar yadda Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya da kuma doka suka zayyana da kuma ƙa’idojin Majalisar Wakilan…………………………..; sannan koda yaushe zan kula da ɗiyaucin Najeriya, kasancewar ta ƙasa ɗaya, haɗin kai, zaman lafiya da yalwar arziƙin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; zan tsaya tsayin daka wajen ganin Najeriya ta cim ma manyan burace-buracenta tare da manyan manufofinta kamar yadda suke a Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya; kuma zan yi iyakar bakin ƙoƙarina, na mutunta, kare, tare kuma da tsare Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, sannan zan kiyaye ƙa’idojin kyan hali na ma’aikaci da aka shimfiɗa a rataye na biyar na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.
Ya Allah ka taimake ni.

Shugabancin Zama

Sashe na 53, ƙaramin sashe na (1), tanadi na (b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadi cewa Kakakin Majalisar Wakilai shi ne zai jagoranci dukkan zaman Majalisa sai dai idan baya nan mataimakinsa ya kama.

Zaman Haɗin Guiwa

Zaman haɗin guiwa shi ne zama tsakanin tagwayen Zaurukan Majalisun Tarayya a lokaci guda kuma a waje guda.

Shugabancin Zaman Haɗin Guiwa

Sashe na 53, ƙaramin sashe na biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa, shugaban Majalisar Dattawa ne zai jagoranci zaman haɗin guiwar Tagwayen Majalisu. Idan kuma baya nan sai kakakin Majalisar Wakilai ya jagoranta, idan kuma duka biyun basa nan to sai mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya jagoranta, idan shima baya nan to sai mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ya jagoranta. Idan kuma duka babu ɗaya, to sai majalisar Dattawa ta wakilta, idan haka bata yiwu ba, sai Majalisar Wakilai ta wakilta idan kuma duk hakan bata samu ba, to sai mahalarta zaman su wakilta wanda zai jagoranci zaman.

Shugabanci

Majalisar wakilai ta Tarayyar Jamhuriyar Najeriya tana da manyan jami'ai kamar haka:

 1. Kakakin Majalisa (Speaker).
 2. Mataimakin Kakaki (Deputy Speaker).
 3. Shugaban Masu Rinjaye (Majority Leader).
 4. Shugaban Marasa Rinjaye (Minority Leader).
 5. Babbar Bulaliyar Majalisa (Chief Whip).
 6. Ƙaramar Bulaliyar Majalisa (Minority Whip).
 7. Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye (Deputy majority leader).
 8. Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye (Deputy Minority leader).
 9. Mataimakin Babbar Bulaliyar Majalisa (Deputy Chief Whip).
 10. Mataimakin Ƙaramar Bulaliyar Majalisa (Deputy Minority Chief  Whip)

Ayyukan Majalisa

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ɗora wa Majalisar Wakilai Ta Tarayya alhakin yin dokoki domin samar da zaman lafiya, bin doka da kuma samar da kyakkyawan yanayin shugabanci a faɗin Tarayyar Najeriya.

Ƙari a kan haka kuma tana da wasu nauye-nauye masu tarin yawa waɗanda ake tafiyarwa ta hanyar kafa kwamatocin da suka ƙunshi mambobin Majalisar waɗanda suke bibiyar lamuran da suka shafi kwamatocin nasu domin yin ƙudurin dokokin da suka shafi lamarin abin da ya bayar da damar kafa kwamatocin da yawansu ya kai har guda 84.

Wannan shi ne zance game da Majalisar Wakilai ta Tarayyar Jamhuiyar Najeriya. Kuma dai muna sa ran cewa, a duk lokacin da muka samu wani sabon bayani mai amfanarwa, to da izinin Allah za mu sake sabunta shafin kamar yadda yake a al’adar rubuce-rubce.

Manazarta


Ikenwa C. (2019). Full List of Nigeria's Senat Presidents Till Date. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://nigerianinfopedia.com.ng/full-list-of-nigerias-senate-presidents-till-date/

National Assembly (2019). Federal Republic of Nigeria, National Assembly, An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.nassnig.org/

Wikipedia (2019), List of Senate Presidents. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/President_of_the_Senate_of_Nigeria


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Majalisun Tarayya:

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub