Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hukumar Ilimi  ta Najeriya


Gabatarwa

Hukumar Ilimin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, wadda ake kira Federal Ministry of Education a Turance sannan kuma ake taƙaita ta da FME, reshe ce ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya wadda alhakin tsara harkokin ilimi, gudanarwa, kulawa, ɗaukar nauyi da sauran lamuran da suka shafi ilimi ya rataya a wuyanta kaco-kaf a duk faɗin Tarayyar Najeriya kuma a dukkan matakai kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da kuma Ƙudurin Dokar Ilimi ta Ƙasa suka ɗora mata. Ta hannunta Gwamnatin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya ta ke son cimma manufofinta na ilimi.

Babban shugabanta shi ne babban minister wanda shugaban ƙasa yake naɗawa ta hanyar sahalewar ‘yan majalisar dattawa kamar sauran ministoci bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Tarayya Najeriya na shekarar 1999.

Manufofin Ilimin Gwamnatin Najeriya

Tanade-tanaden sashe na 18 a Babi na II na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, an zayyana waɗannan manufofi da za a su zo a ƙasa, a matsayin manufofin ilimi na Gwamnati:

 1. Gwamnati za ta mai da hankali wajen ganin an bayar da damar samun ilimi kowane iri ne, kaɗan ko kuma mai yawa.
 2. Gwamnati za ta haɓɓaka ilimin kimiyya da na fasaha.
 3. Gwamnati za ta tashi tsaye wajen ganin ta kawar da jahilci a duk lokacin da ta ga ya dace ta hanyar:
 4. Bayar da ilimin firmare kyauta tare kuma da mayar da shi tilas a kan kowane ɗan Najeriya.
 5. Bayar da ilimin sakandire kyauta.
 6. Bayar da ilimi jami’a kyauta.
 7. Buɗe ajujuwan yaƙi da jahilci.

Ayyukan Hukumar Ilimi

Waɗannan ayyuka da za a zayyano a ƙasa, su ne ayyukan da suka rataya a wuyan Hukumar Ilimin Tarayyar Najeriya kamar yadda ta wallafa a shafinta na Intanet cikin harshen Turanci a shekarar 2019:

 1. Tsara manufofin ilimi na ƙasa;
 2. Tattara bayanai domin tsara harkokin ilimi da kuma ɗaukar ɗawainiyoyin ilimi ta fuskacin kuɗi;
 3. Tsarawa tare kuma da tabbatar da yanayi ko darajar ilimin bai ɗaya a duk faɗin ƙasa. Wato ta tabbar da cewa a duk faɗin Najeriya tsarin ilimi guda ɗaya ake bi;
 4. Kula tare kuma da saka ido game da ingancin ilimi a dukkanin faɗin ƙasa;
 5. Daidaita manufofin ilimi da kuma tsare-tsaren ilimi na dukkanin jahohin Tarayya ta hanyar Majalisar Ilimi ta Ƙasa (National Council on Education);
 6. Aiwatar da haɗin kai a cikin al’amuran ilimi a ma’aunin ƙasa-da-ƙasa; da kuma
 7. Samar da manhajojin ilimi a matakin ƙasa baki ɗaya.

Rukunai

Hukumar Ilimin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya ta kasu zuwa rukunai uku bisa tsarin Tarayya (Federal System of Government) kamar haka:

 1. Matakin Tarayya: Ita ce asalin hukumar ilimin Gwamnatin Tarayya wadda aka kira Federal Ministry of Education a Turance wadda kuma Ministan Ilimi shi ne babban jami’inta kuma shugaban ƙasa ne yake naɗa shi bisa sahalewar ‘yan Majalisar Dattawa ta Najeriya.
 2. Matakin Jaha: Ita ce hukumar ilimi ta jaha wadda aka kira State Ministry of Education a Turance. Kwamashina shi ne babban jami’inta kuma gwamnan jaha ne yake naɗa shi bisa sahalewar ‘yan majalisar dokoki ta jaha.
 3. Kula da gudanarwar dukkan harkokin ilimi a matakin jaha, ya rataya a wuyanta kamawa tun daga gina manya da ƙananan makarantun sikandire da ma makarantun gaba da sikandire ciki kuma har da jami’o’i, ɗaukar ma’aikata da sauransu.

 4. Matakin Ƙaramar Hukuma: Ita ce hukumar ilimi ta ƙaramar hukuma wadda ake kira Local Education Authority a Turance. Babban shugabanta shi ne Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukuma wato Education Secretary a Turance.

Alhakin kula da harkar ilimi a dukkan faɗin ƙaramar hukuma ya rataya a wuyanta kamawa tun daga gina makarantun firamare da ƙaramar sikandire, samar da kayan aiki, ɗaukar malamai, kula da gudanawar ilimi da sauransu.

Sassan Hukumar Ilimi

Hukumar Ilimin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya tana da sassa a cikinta domin samun cikakkiyar damar cimma manufofinta kamar yadda aka zayyana ta hanyar rabon-ayyuka. Ga sassan nata kamar haka:

 1. Sashen Ilimin Manyan Makarantu (Tertiary Education).
 2. Sashen Ilimin Bai-Ɗaya da na Sikandire (Basic and Secondary Education).
 3. Sashen Tabbatar da Ingancin Ilimi na Tarayya (Federal Education Quality Assurance Services).
 4. Sashen Ilimi Kimiyya da Fasaha (Technology and Science Education).
 5. Sashen Tsare-Tsaren Ilimi da Haɓɓaka Bincike (Education Planning, Research and Development).
 6. Sashen Tallafin Ilimi na Tarayya (Federal Scholarships).
 7. Sashen Fasahar Sadarwa da Bayanai (Information and Communication Technology).
 8. Sashen Rarraba Jama’a (Human Resources Management).
 9. Sashen Kuɗi da Ƙididdiga (Finance and Accounts).
 10. Sashen Samar da Kayayyaki (Procurement).
 11. Sashen Farfaɗo da Sadar-da-Tsakani da kuma Inganta Ayyuka. (Reform Coordination and Service Improvement).
 12. Sashen Harkokin Tallafawa Ilimi (Education Support Service)
 13. Sashen Binciken Ciki (Internal Audit).
 14. Sashen Harkokin Ɗakin Karatu (Library Services).

Rassa da Cibiyoyi

Hukumar Ilimin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, babbar hukuma ce da ke da rassa da suka haura ashirin, kowane reshe yana da sassa, haka nan kuma wasu daga cikin su suma sun yi rassa. Ga rassan kamar haka:

 1. Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya (Universal Basic Education Commission (UBEC))
 2. Hukumar Yi Wa Malamai Rijista ta Nijeriya (Teachers’ Registration Commission of Nigeria (TRCN)).
 3. Cibiyar Lissafi ta Ƙasa (National Mathematical Centre (NMC)).
 4. Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i da Manyanyan Makarantu. (Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB)).
 5. Hukumar Shirya Jarabawar Sikandire ta Ƙasa (National Examinations Council (NECO)).
 6. Amintacciyar Hukumar Ɗaukar Ɗawainiyar Ilimin Manyan Makarantu (Tertiary Education Trust Fund (TETFUND)).
 7. Ɗakin Karatu Na Ƙasa (National Library of Nigeria (NLN))
 8. Hukumar Yi Wa Jami’an Ɗakin Karatu Rijista ta Nijeriya (Librarian Registration Council Of Nigeria (LRCN)).
 9. Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (National Universities Commission (NUC)).
 10. Buɗaɗɗiyar Jami’ar Ƙasa ta Nijeriya (National Open University of Nigeria (NOUN)).
 11. Ƙauyen Yaren Faransaci na Nijeriya (Nigerian French Language Village (NFLV)).
 12. Ƙauyen Yaren Larabci na Nijeriya (Nigerian Arabic Language Village (NALV)).
 13. Babbar Makarantar Tsare-Tsaren Ilimi da Gudanarwa ta Ƙasa (National Institute for Educational Planning and Administration (NIEPA)).
 14. Cibiyar Tsare-Tsaren Ilimi da Haɓɓaka Bincike ta Nijeriya (Nigerian Educational Planning and Research Development Centre (NERDC)).
 15. Hukumar Ilimin Manya da kuma Ilimin da ba na Zamani ba ta Ƙasa (National Mass Literacy, Adult and Non-Formal Education Commission (NMEC)).
 16. Hukumar Ilimin Fasaha ta Ƙasa. (National Board for Technical Education (NBTE)).
 17. Hukumar Ilimin Kasuwanci da na Fasaha ta Ƙasa (National Business and Technical Education Board (NABTEB)).
 18. Babbar Makarantar Horas da Malaman Makaranta ta Ƙasa (National Teachers’ Institute (NTI)).
 19. Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (National Commission for Colleges of Education (NCCE)).
 20. Hukumar Ilimin Makiyaya ta Ƙasa (National Commission for Nomadic Education (NCNE)).
 21. Hukumar Yi Wa Ƙwararru a Fannin Kwamfuta Rijista ta Nijeriya (Computer Registration Council of Nigeria (CRCN)).
 22. Makarantar Harsunan Nijeriya ta Ƙasa (National Institute of Nigerian Languages (NINLAN)).

Shafin Intanet

Hukumar Ilimin Najeriya tana da shafin Intanet. Latsa nan ka tsunduma cikin wannan shafi.

Manazarta


Federal Ministry of Education (2019). Our Mandate. An ciro daga: http://www.education.gov.ng/our-mandate/ a shekarar 2019

Servicom (2017). Federal-Ministry-of-Education. An ciro daga shafin: http://servicom.gov.ng/wp-content/uploads/2017/09/Federal-Ministry-of-Education.pdf a shekarar 2018.

Wikipedia (2019). Federal Ministry of Education (Nigeria). An ciro daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Federal_Ministry_of_Education _(Nigeria), a shekarar 2019.Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub