Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa


Gabatarwa

Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa, hukuma ce da take a matsayin reshen Hukumar Ilimin Najeriya wadda sashen Kula da Ilimin Manyan Makarantu na Hukumar Ilimi yake kula da ita.

Ita ce hukumar da aka ɗorawa alhakin kula da gudanawar jami’o’in Najeriya ciki kuma har da na gwamnatotcin jahohi da ma masu zaman kansu ƙari a kan na gwamnatin tarayya.

Tarihi

An kafa wannan hukuma a cikin shekarar 1962 a matsayin hukumar bayar da shawara game da harkokin jami’o’in Najeriya a ƙarƙashin ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya (Cabinet Office).

Shugabanci

Babban Sakatare (Executive Secretary), shi ne babban shugabanta. Wanda kuma shugaban ƙasa ne yake naɗa shi bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Ayyukan Hukuma

Muhimman Ayyukan Hukumar Hukumar Jami’o’i ta Najeriya su ne:

 1. Bayar da izinin gudanar da dukkan wani darasin ilimi a jami’o’in Najeriya;
 2. Bayar da izinin kafa dukkan manyan makarantun da za su riƙa horas da masu digiri a jami’o’in Najeriya;
 3. Tabbatar da nagartar dukkan shirye-shiryen ilimi da ake gudanarwa a jami’o’in Najeriya; da kuma
 4. Samar da dukkan wani tallafi daga waje ga jami’o’in Najeriya.
 5. Bunƙasa amfani da fasahar Sadarwa da Bayanai (ICT) wajen bayar da ilimin jami’a ta hanyar tsoma baki a duk bayan watanni uku-uku ta hanyar horas da ma’aikata, ɗalibai, samar da kayan aiki da kuma dasawa tare da samar da hanyoyin koyo ta hanyar kwamfuta.
 6. Tabbatar da ci gaban shirye-shiryen ilimi tsararre a matakan ƙasa da digiri da kuma sama da shi a Jami’o’in Najeriya ta hanyar tantance bayanan ilimi a cikin makwanni biyu da samun (Bayanan).
 7. Kulawar bayan watanni uku-uku da kuma tantance harkar karantarwa, kuɗaɗe da kuma gudanar da jami’o’i ta hanyar amfani da ma’aunai da sharruɗan da aka shimfiɗa.
 8. Bunƙasa ingantaccen nazari a Jami’o’in Najeriya ta hanyar samar da gamsassun hanyoyi tare da tallafi, misali, Shirin Bayar da Tallafin Shekara-Shekara na Digirin Digirgir na Jami’o’in Najeriya wanda aka kira Annual Nigerian Universities Doctoral Thesis Award Scheme (NUDTAS) a Turance da kuma samar da hanyar wallafa mafi ƙololin daraja a kan abubuwan da suka shafi kundayen digirori da kuma mujallun nagartattun rahotannin bincike.
 9. Aiwatar da duk wani abu da ya shafi kafa alaƙa da kuma sabuntata da kuma haɗin kai a tsakanin jami’o’i a ciki da wajen ƙasa a tsawon awannin 72.
 10. Tabbatar da cusa al’adar tsari da dabaru a cikin jami’o’in Najeriya ta hanyar shiryawa da kuma yaɗa ƙa’idoji tare kuma da tantance dabarun tsare-tsaren ga jami’o’in a cikin mako guda da samun waɗannan takardu.

Sassa

Wannan hukuma tana da sassa guda goma sha biyu kamar haka:

 1. Sashen Tsare-tsare (Directorate of Academic Planning).
 2. Sashen Kulawa da kuma Dubagari (Directorate of Inspection and Monitoring).
 3. Sashen Tallafawa Harkokin Gudanarwa (Directorate of Management Support Services).
 4. Sashen buɗe jami’o’i masu zaman kansu (Directorate of the Establishment of Private Universities).
 5. Sashen harkokin tallafawa ɗalibai (Directorate of Students Support Services).
 6. Sashen Nazari, Ƙirƙire-Ƙirƙire da Kuma Fasahar Sadarwa (Directorate of Research, Innovations & Information Technology).
 7. Sashen Harkokin Kuɗi da Tsimi (Directorate of Finance and Accounts).
 8. Sashen Tantancewa (Directorate of Accreditation).
 9. Sashen Buɗaɗɗen Salon Karatu da kuma Koyo Daga Nesa (Directorate of Open and Distance Education).
 10. Sashen Harkokin Haɗa Hannu da Ƙulla Alaƙoƙin Ƙasa-da-Ƙasa (Directorate of Liaison Services and International Cooperation).
 11. Sashen Kula da Hulɗa da Al’ummomi Masu Zaman Kansu (Directorate of Corporate Communications).
 12. Sashen Hulɗa da Ofishin Babban Sakatare (Directorate of the Executive Secretary’s Office).

Shafin Intent

Latsa nan ka shiga babban shafin Hukumar Jami'o'i ta Ƙasa

Manazarta


NUC (2018). National Universities Commision. An ciro daga shafin: http://nuc.edu.ng/about-us/, a shekarar 2018.

Servicom (2017). Federal-Ministry-of-Education. An ciro daga shafin: http://servicom.gov.ng/wp-content/uploads/2017/09/Federal-Ministry-of-Education.pdf a shekarar 2018.Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub