Me ka ke nema?


Shafin Farko

Buɗaɗɗiyar Jami’ar NajeriyaTambarin Noun
Hoto: Shafin Nooun

Gabatarwa

Noun, suna ne na buɗaɗɗiyar jami’ar Najeriya mai gudanar da karatu da kuma bayar da horo ta salon karatu daga nesa; wato Distance Learning kenan a Turance, wanda kuma ya yi daidai da zamani ta hanyar isar da darasi ga ɗalibai ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwar zamani wato ICTs abin da a Turance ake kira Open and Distance Learning.

Wannan jami’a, “Buɗaɗɗiyar Jami’ar Najeriya, tsohuwar makaranta ce wadda ta yi fice wajen bayar da ingantacce ilimi, mai sauƙin sarrafawa tare kuma da sauƙin kuɗi ta hanyar salon bayar da karatu a buɗe kuma daga nesa (ODL) wanda ya yi daidai da ƙarni na 21 da zamani mai zuwa a gaba” Noun (2019).

Ita ce irin ta ta farko a duk faɗin Afirka ta Yamma (Wikipedia, 2019). Haka nan kuma, ita ce jami’a mafi girma a duk faɗin Najeriya wadda take da cibiyoyin karatu 43 a faɗin ƙasa.

Haƙiƙa wannan jami’a tana bayar da gagarumar gudunmawa wajen cike giɓin da ake da shi a fannin ilimi a Najeriya musamman a tsakanin mutane masu manyan shekaru, manyan ma’aikata da kuma manyan ‘yan kasuwa waɗanda suke da ƙarancin lokacin zuwa su halarci sauran jami’o’in bayar da karatu mai zurfi.

Shugaban Ƙasa Olushegun Obasanjo, wanda shi ne ya farfaɗo da ita bayan dogon suman da ta yi na shekaru goma sha takwas (1984-1999), yana ɗaya daga cikin kyawawan misalai na wannan jami’a wanda ya yi rijista da ita, ya samu digirin farko, na biyu da na uku, wanda ya kammala a shekarar 2018.


Olusegun Obasanjo, GCFR yana kare kundin digirinsa na uku a Noun

Ƙarin haske game da wannan jami’a, da kuma ayyukan da suka rataya a wuyanta, shi ne babban dalilin yin wannan rubutu.

Tarihi

Tun da farko, an fara kafa wannan wannan makaranta a zamanin mulkin tsoho kuma sannan farkon shugaban ƙasar farar hula na Najeriya, Marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a ranar 22 ga watan Yulin Shekarar 1983. Daga bayan kuma, gwamnatin da ta biyo bayanta, wato gwamnatin soja da Janar Muhammadu Buhari ya jagoranta, ta soke ta a ranar 25 ga watan Afirilu, 1984 (Muhammad da Isma’il, 2003; Wikipedia, 2019). Kenan, duka-duka jami’ar ta yi rayuwar watannin goma, sannan kuma ta shiga dogon suma.

Sabuwar gwamnatin farar hula ta Janar (Mai ritaya), Olusegun Obasanjo, ita ta farfaɗo da wannan jami’a a shekarar 2002. Wannan shi ne abin da ya farfaɗo da wannan makaranta bayan ta ɗauki shekaru 18 a sume.

Manufofi

An kafa wannan makaranta domin ta cimma waɗannan manufofin ilimi a Tarayyar Jamhuiryar Najeriya:

 1. Samar da Ilimi ga dukkan ‘yan ƙasa da kuma haɓɓaka koyo mai ɗorewa.
 2. Cike giɓin da ke akwai wanda rufe rassa da tsangayun nesa (Satellite Campus/Outreach)  na jami’o’i ya haifar.
 3. Sauƙaƙa kashe kuɗaɗɗe.
 4. Haɓɓaka tattalin arziƙi.
 5. Yalwatattun tsare-tsaren isuwa ga jama’a.
 6. Cin cikakkiyar gajiyar ma’abota ilimi da ake da su.
 7. Horas da malamai  a halin gudanar da aiki.
 8. Gusar da talauci, horaswa da kuma ilimi mai ɗorewa.
 9. Samar da ilimin da ba tsararre a takarda ba.
 10. Isuwa ga waɗanda aka gaza kai wa gare su.
 11. Yaɗa tarbiyyar ƙasa.

Shugabanci

Kamar dukkan sauran jami’o’in Najeriya, tana da shugaba da kuma mataimakin shugaban Jami’a; wato Chancellor da kuma Vice Chancellor. Wanda a yanzu (2019), Farfesa Abdallah Uba Adamu ne Mataimakin Shugaban Jami’ar.

Shafin Intanet

Latsa nan ka buxe babban shafin wannan katafariyar jamai'a.

Manazarta


Muhammad da Isma'il. (2003). Tarihin Shehu Shagari. An buga a TPCS Ltd/Al-Rissalah Printing and Publishing Co. (Nig) Ltd. Domin M and I Essence Publi sher, Kaduna-Nigeria.

Noun (2019). The University for You. An ciro daga shafin: http://nou.edu.ng/index.php/page/uniɓersity-you-0, a shekarar 2019.

Wikipedia (2019). National Open University of Nigeria. An ciro daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/National_Open_University_of_NigeriaKoma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub