Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hukumar GargajiyaGinin Hukumar Gargajiyar Katsina

Gabatarwa

Hukumar Gargajiya, wadda ake kira Native Authority a Turance, sannan kuma ake taƙaita ta da NA; wasu marubuta a fannin tarihi kuma suke rubuta ta da en’e ko EN’E a Hausance, hukuma ce da Turawan Mulkin Mallaka suka kafa domin kare doka da oda ƙarƙashin Babban Gwamna, wato Governor General, Gwamna Lugga. Ta hanyar amfani da wannan hukuma Turawan suka gudanar da mulki a fakaice; wato indirect rule a Turance.

Bayan shelanta kafa Yankin Arewa (Northern Protectorate) da ya yi a 1900, da kuma samun nasarar kawo ƙarshen Daular Usmaniyya a shekarar 1903, Gwamna Lugga ya taras da salon tsarin gudanar da mulki na Daular Usmaniyya tsararre sannan kuma mai sauƙin gudanarwa saboda haka ya yi amfani da shi a iya yankin Arewa (Utuk, 1975) a matakin farko, daga baya kuma ya yi masa doka 1916 wato Native Authority Ordinance a Turance (Egbe, 2014), aka faɗaɗa shi zuwa Yammaci da Kudanci daga ƙarshe kuma Turawa suka yi amfani da shi a dukkanin ƙasashen Afirka ta Yamma da suka yi wa Mulkin-Mallaka (Boahen, 1986).

Wannan salon mulki shi ne na farko a ƙaramin matakin gudanar da mulki da Turawa suka yi amfani da shi wanda kuma ya mayar da mulki a fakaice tare da azbtar da mutane ruwan dare game duniya (Egbe, 2014). Gwamna Lugga, shi ne ya ƙirƙiri wannan hukuma a zamanin mulkinsa da ya gudanar a matsayin Babban Kwamashinan Birtaniya (1900 – 1906) kamar yadda ya zo a ruwayar Apata (1990).

Shugabanci

Babban shugaban Hukumar Gargajiya shi ne Sarki, shi ne sama da kowa a Hukumar Gargajiya wanda shi kuma yake karɓar umarni daga Rasdan (Resident Officer).

A ƙarƙashin wannan hukuma akwai sassa uku da suka yi kama da tsarin Tarayyar Gwamnatin Nijeriya ta yau:

  1. Ɓangaren zartarwa.
  2. Ɓangaren Shari’a.
  3. Ɓangaren Dokoki.

A ƙarƙashin waɗannan ɓangarori ake tattara haraji, gudanar da shari’o’i, ɗaukar jami’an tsaro da sauransu. Dukkan waɗannan ɓangarori sarki ne ruwa kuma shi ne langa. Maganarsa ita ce kankat.

Manazarta


Adamu  Ɗ. A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi, An Autobiography of the 24th Aku-Uka, as Told to Ɗanjuma A. Adamu. An buga a Able Productions tare da haɗin Guiwar Animation Books.

Apata Z.O. (1990). Lugard and the Creation of Provincial Administration in Northern Nigeria 190ƙ-19180l. Department of History, University of florin. African Study Monographs, 11(3): 143-152, December 1990

Boahen A. (1986). Topics in West African History. Pearson Educational Limited, Edinburg Gate, Harlow, Essex CM20 2JE, England.

King L. D. (2016). The Civilizing Mission and Indirect Rule in Northern Nigeria: A Contradiction. Department of History, James Madison University, USA. International Journal of Social Sciences Studies, Ɓol. 4, No. 8: August 2016, ISSN 2324-8033. An ciro daga shafin http://ijsss.redfame.com a shekarar 2019

Sokoh G.C. (2018). An Historical Analysis of the Changing Role of Traditional Rulers in Governance in Nigeria. IOSR Journal of Humanities and Social Science (IOSR-JHSS) Volume 23, Issue 1, Ver. 2 (January. 2018) PP 51-62 e-ISSN: 2279-0837, p-ISSN: 2279-0845. An ciro daga shafin: www.iosrjournals.org a shekarar 2019

Utuk E. I. (1975). Britain's colonial administrations and developments, 1861-1960: an analysis of Britain's colonial administrations and developments in Nigeria. Dissertations and Theses. Paper 2525. Portland State University.Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub