Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hukumar 'Yansandan NijeriyaTambarin Hukumar 'Yansanda

Gabatarwa

Hukumar ‘Yansandan Najeriya hukuma ce da ake kira Nigerian Police Commission a Turance. Ita ce hukumar da alhakin naɗa muƙaman ‘yansanda, ƙara musu girma, ladabtar da su da kuma sauran wasu ɗawainiyoyi suka rataya a wuyanta.

Kafa Hukumar ‘Yansanda

Babi na VI, sashe na 153, ƙaramin sashe na (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, shi ya bayyana cewa a kafa Hukumar ‘Yansanda.

Wakilan Hukuma

Ƙuduri na 29 na sashe na ɗaya na rataye na uku na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya zayyana rukunin mutane biyu a matsayin wakilan Hukumar ‘Yansandan Najeriya. Ga su kamar haka:

  1. Shugaba; shi ne wanda zai jagoranci hukumar.
  2. Waɗansu mutane da ba a so adadin su ya yi ƙasa da bakwai ba sannan kuma kar su haura tara bisa la’akari da yadda Majalisar Ƙasa za ta ƙayyade.

Ikon Hukuma

Ƙuduri na 29 na sashe na ɗaya na rataye na uku na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bai wa wannan Hukuma ta ‘Yansandan Najeriya ikon gudanar da ayyukan da suka shafi:

  1. Naɗa jami’an ‘yansanda kan muƙaman ‘yansanda in banda muƙamin babban sufeton ‘yansanda na ƙasa.
  2. Alhakin kora da kuma ladabtar da jami’an da aka ambata a ƙaramin shashi na (a) na ƙuduri na 29 na sashe na ɗaya na rataye na uku na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, ya rataya a wuyan wannan hukuma.
  3. Naɗa kwamashinonin ‘yansandan jahohi. A babi na VI, sashe na III,  babbar doka mai lamba 215, tanadin ƙaramar doka (1) mai lamba (b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bayyana cewa, Hukumar ‘Yansada ce ke da alhakin naɗa wa kowace jaha daga cikin jihohin Najeriya kwamashinan ‘yansanda.
Latsa nanka shiga shafin Hukumar 'Yansanda kai tsaye.

Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub