Janar TY Ɗanjuma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Janaral Theophilus Ɗanjuma, GCFR



Janaral Theophilus Ɗanjuma, GCFR

Gabatarwa

Janaral Theophilus Ɗanjuma, tsohon sojan Najeriya ne, kuma hamshaƙin ɗankasuwa, shahararren mai taimakon jama’a, ƙungiyoyi, garuruwa da jahohi. Haka nan kuma Janaral TY Ɗanjuma ta fuskar siyasa ma ba a bar shi a baya ba, shi ɗansiyasa ne.

Hamshaƙin Mai kuɗi, wanda ke ɗaya daga cikin jerin manyan masu kuɗin Afirka. Shafin Nigerian Biography (2015), ya ruwaito jaridar ƙididdigar masu kuɗin duniya (Forbes, 2014), ta ruwaito TY Ɗanjuma  cewa shi ne mutun na 22 a yawan kuɗi a duk faɗin Afirka.

Haihuwa

An haifi Theophilus a ranar 9 ga watan Disambar shekarar 1938 a garin Takun ta tsohuwar jahar Gwangola wacce a yanzu ƙaramar hukuma ce a cikin jahar Taraba. Sunan mahaifinsa Kuru Ɗanjuma, mahaifiyarsa kuma sunanta Rufƙatu Asibi. Shi ɗan ƙabilar Jukun ne. cikakken sunansa shi ne Theophilus Yakubu Danjuma, amma ana yi masa laƙabi da “TY Ɗanjuma”.

Karatu

Janaral Theophilus Ɗanjuma, ya yi karatunsa na firamare da sikandire a makarantun ‘St Bartholomew's Primary School’ da ke Wusasa ta Zariya, da kuma ‘Benue Provincial Secondary School’ da ke Katsina-Ala ta cikin jahar Binuwai. Inda ya kammala a 1958. Daga nan Theophilus Ɗanjuma ya samu nasarar shiga makarantar ‘Nigerian College of Arts Science and Technology’ ta Zariya wacce yanzu ta koma jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (Ahmadu Bello University) a shekarar 1959, dan karantar fannin tarihi (History), sai dai, ya bar wannan makaranta a shekarar 1960 ya koma makarantar sojojin Najeria (Nigerian Military Training College) ta Kaduna, inda ya yi karatu daga shekarar 1960 zuwa 1961.

Sannan kuma ya samu halartar ‘Mons Officer Cadet School’, da ke garin Aldershot, a ƙasar Birtaniya (United Kingdom). Sannan ya yi karatu a ‘School of Infantry’, da ke garin Hythe da Warminster a shekarar 1962, sai kuma ‘Special Warfare Centre’ a shekarar 1963, da kuma ‘Army Staff College’ a shekarar 1967, duk a ƙasar Birtaniya (United Kingdom).

Gogayyar Aiki

Tun bayan kammala samun horansa na soja, Janaral TY Ɗanjuma mai ritaya, ya riƙe muƙamai da dama, daga ciki akwai:

  1. An fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). A shekarar 1963, an tura shi rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya ta samar da zaman lafiya (UN Peace-keeping force) a garin Sante, da ke lardin Kataga a ƙasar Kwango (Congo).
  2. A shekarar 1966 aka ƙara masa girma zuwa Kyaptin (captain) ɗin soja. A shekarar 1967 aka sake ɗaga shi zuwa laftanar kanal (lieutenant Colonel).
  3. A shekarar 1970, TY Ɗanjuma ya wakilci Najeriya a ‘International Court Martial in Trinidad and Tobago’ a matsayin ‘president of the tribunal’ inda ya jagoranci kotun da ta tuhim yunƙurin juyin mulkin da aka yi a Trinidad da kuma Tobago.
  4. 1971 aka ɗaukaka shi zuwa kanal (Colonel) da kuma muƙamin ‘court-martialling Army officers’ da ya jagoranci kula da yaƙi da rashawa da kuma ɗa’ar sojoji.
  5. A 1975, ya zama birgediya (brigadier) wanda aka yi masa muƙamin ‘General Officer Commanding (GOC)’. A 1976 aka yi masa muƙamin shugaban rundunar sojojin ƙasa na Najeriya (Chief of Army Staff) a lokacin mulkin shugaba Ubasanjo a matsayin soja.
  6. ‘Chairman of the Presidential policy Advisory Committee’, 1999.
  7. ‘Honourable Minister of Defence’, 1999 zuwa 2003.
  8. ‘Chairman of the Presidential Advisory Council’, tun daga 2010 har zuwa yau (2016).
  9. Shugaban kwamtin sake tsungunar da ‘yan gudun hijirar Najeriya (Internally Displaced Persons), muƙamin da shugaba Muhammadu Buhari ya ɗana shi a shekarar (2016). 

Kasuwanci

A shekarar 1979, ya buɗe kamfanin fito (Shiffing) mai suna America Line (NAL), kamfanin da ya samar da guraben ayyuka na sama da mutane 251. Shi ne mai kamfanini COMET Shipping Agencies Nigeria Ltd., wanda aka buɗe shi a shekarar 1984.

A shekarar 1995, T.Y. Ɗanjuma, ya shiga harkar mai inda ya buɗe kamfani mai suna South Atlantic Petroleum Limited (SAPETRO).

Shigarsa Siyasa

Tun baya miƙa mulki ga hannun farar-hula, TY Ɗanjuma ya shiga siyasa, kuma tun wannan lokaci ake damawa da shi har zuwa yau ɗin nan (2016).

Manazarta:


Gabriel C. (2016). General TY Danjuma: Soldier of political consequence and philanthropic niche. Jaridar Vangurad. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.vanguardngr.com/2016/01/general-ty-danjuma-soldier-of-political-consequence-and-philanthropic-niche/

Inside Nigeria (2015). The Man - Lt. Gen Theophilus Yakubu Danjuma Rtd. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://oajala.blogspot.com.ng/2010/06/man-lt-gen-theophilus-yakubu-danjuma.html

Nigerian Biography  (2015) Biography of Theophilus Danjuma; Billionaire; Taraba State Celebrity. An ciro a shekarar 2016, daga shafin:http://www.nigerianbiography.com/2015/05/ biography-of-theophilus-danjuma.html

Premium Times (2016). Buhari names TY Danjuma, Dangote in committee on North-East rehabilitation. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.premiumtimesng.com

South Atlantic Petroleum Limited (ba kwanan wata). General TY Danjuma. An ciro a shekarar 2016, daga shafin:http://www.sapetro.com/general-ty-danjuma/

Wikipedia (2016). Theophilus Danjuma. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Theophilus_Danjuma


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub