Janar Suleimanu Isa Wali

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Janar Suleimanu Isa Wali, GSS, Psc, Fdc (+), Meng


Gabatarwa

Manjo Suleimanu Isa Wali gogaggen injiniyan lantarki, masanin fannin laturonik, kwamfuta da kuma harkokin fasahar sadarwa da bayanai, kuma, janar ɗin sojan Najeriya mai ritaya.

Suleimanu Wali, mutumin Kano ne sannan kuma ɗan kishin ƙasa, wanda ya saudarkar da rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasar Najeriya.

A fannin karatu kuwa, yana ɗauke da digirori uku a fannonin ilimi daban-daban. Digirin farko a fannin lantarki, sai kuma ƙarin digiri na biyu sannan kuma guda biyu a fannonin Fasahar Sadarwa da Bayanai (Information and Communication Technology) da kuma fannin Nazarin Dabarun Tsare-Tsare (Strategic Studies).

Wannan ɗan rubutu da mai karatu yake karantawa, ba komai ba ne sai wani ɗan tsinkaye game da rayuwar ɗan kishin ƙasa janar Suleimanu Isa Wali mai ritaya. Domin a ɗan haskaka wa mai karatu matakin farko na saninsa. Ga filin nan, ga mai doki.

Haihuwa

An haifi Suleimanu a garin Kano, shi ɗa ne ga Isa Wali. Shi kuwa Isa Wali yana daga cikin wanɗanda suka hidimtawa jagoran talakawa na asali; wato marigayi Malam Aminu Kano. An haife shi a ranar 5 ga watan Fabarairu na shekarar 1955.

Karatu

Suleimanu ya fara karatunsa na firamare a makarantar St. Saviours da ke Ikoyin Legas a Najeriya daga 1960 zuwa 1963. Sai kuma aka mayar da shi makarantar Corono, itama dai a Ikoyin da ke Legas daga 1963 zuwa 1965. Sannan ya ƙarasa karatun firamare a makarantar Kafital ta Kaduna a shekarar 1966.

Bayan kammala karatun firmare, sai kuma ya samu nasarar tsallakawa makarantar sikandiren gwamnati da ke Keffin Ɗanyamusa, wacce a yanzu ta ke cikin jahar Nassarawa, Najeriya, a shekarar 1967. Daga nan kuma sai aka ɗauke shi zuwa makarantar Claverham da ke garin Battle ta Sussex a ƙasar Ingila daga 1968 zuwa 1971. Ya ƙarasa karatunsa na sikandire a makarantar Bexhill Girama da ke garin Bexhill ta Sussex a Ingila a cikin shekarar 1973.

Bayan kammala karatunsa na sikandire sai kuma ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya samu digirin farko a fannin lantarki; abin da ya mayar da shi injiyan lantarki mai riƙe da shedar karatun digiri ta BSC Eng (Hons).

Kwasa-Kwasan Horon Soja

Bayan kammala karatun digirin farko da Suleimanu ya yi a fannin lantarki, sai kuma ya tsunduma gidan soja, inda ya samu shiga Makarantar Tsaro (Defense Academy) ta Najriya daga watan Janairu na 1979 zuwa Juli na 1979. Daga nan sai ƙasar Amurka a shekarar 1980, sai kuma Jaji a 1982, Jaji 1983, Jaji 1985, Jaji 1987, Jaji 1994 zuwa 1995, Jaji 1996, kwalejin yaƙi (War College) ta Abuja 2003 zuwa 2004.

Gogayyar Aiki

  1. Ya zama malamin makaranta a makarantar Nigerian Army School Signals daga 1979 zuwa 1982.
  2. Ya riƙe muƙamin Injiniyan Soja mai Lura da sadarwa tsakanin Najeriya da ƙasashen ƙetare ƙarƙashin ma’aikatar harkokin ƙasashen waje daga shekarar 1982 zuwa 1984.
  3. Ya zama jami’in nazari, haɓɓakawa da kuma tantancewa a rundunar kula da saƙonni ta Cibiyar Rundunar Sojojin Najeriya (HQ Nigerian Army Signals Corps) daga shekarar 1984 zuwa 1985.
  4. Mai bayar da horo ga rundunar kula da saƙonni. Ya yi aiki a matsayin mai tantancen buƙatar da sojojin Najeriya masu aiki a fannin saƙonni suke da ita ta sake samun horo daga shekarar 1985 zuwa 1986.
  5. Haɓɓaka horon sojoji a fannin saƙonni a Cibiyar Rundunar Sojin Najeriya (HQ Nigerian Army) daga 1986 zuwa 1987.
  6. Mataimakin Kwamadan Sojojin Najeriya a fannin saƙonni (Military Assistant to the Commander of the Nigerian Army Signal Corps) daga shekara 1987 zuwa 1989.
  7. Jami’in kula da saƙonni (Mechanized Brigade Signal officer) a runduna ta ɗaya (1 Mechanize division) daga shekarar 1989 zuwa 1991.
  8. Mataimakin Babban Jami’in Aiwatarwa (Military Assistant to chief of Operations), daga shekarar 1993 zuwa 1994.
  9. Jami’in kula da horas da sojojin Najeriya (Nigerian Army Training Depot), daga shekarar 1995 zuwa 1998.
  10.  Kwamanda mai kula da sashen saƙonni a ruduna ta biyu ta sojan ƙasa masu bindiga (Commanding Office 520 Operational Signal Regiment of 2nd Infantry Division), daga 1998 zuwa 2000.
  11.  Kanal mai kula da Harkokin Laturonik a Fannin Yaƙi (Colonel Electronic Warfare) a Cibiyar Sojan Najeriya (HQ Nigerian Army Signals Corps), daga shekarar 2000 zuwa 2001.
  12.  Kwamitin bayar da shawarar ƙwararru a fannin laturonik a hukumar nazari da haɓɓaka sararin samaniya ta Hukumar Sararin Saman Najeriya (Member of the technical advisory committee on space science and technology, Nigerian Space Research and Development Agency), daga shekarar 2001 zuwa 2003.
  13.  Mataimakin Daraktan Sadarwa na Cibiyar Tsaron Najeriya (Assistant Director Telecommunications at Defense Headquaters), a shekarar 2004.
  14.  Daraktan Sashen Sarrafa Bayanai Mai Sarrafa Kanta (Director of Directorate of Automated Data Processing) na Cibiyar Sojojin Najeriya (Army Head Quarters), 2004 zuwa 2007.
  15.  Daraktan Sadarwa (Director Communications) na sashen sadarwa (Department of Communication) na cibiyar tsaron Najeriya (Defense Head Quarters) a shekarar 2008.
  16.  Daratkan Gwaji da Tantancewa (Director Test and Evaluation) na sashen nazari da haɓɓakawa (Department of research and development) a Cibiyar Tsaro ta Najeria (Defense Head Quarters) daga 2008 zuwa 2009.
  17.  Mataimakin kwamandan  sannan kuma daraktan karatu a kwalejin tsaro na ƙasa (Deputy commandant and Director Studies, National Defense College), daga 2009 zuwa 2011.

Ritaya

Ya yi ritayar ƙashin kai (Voluntary Retire) bayan shekaru 35 yana aikin soja; wato ya bar aiki domin raɗin-kansa ba domin ya ƙure aikin ba. Domin ya shigo cikin fararen hula ya cigaba da bayar da gudunmawa.

Kyaututtukan Girmamawa

  1. Ya karɓi babbar kyautar yabo da girmamawa ta gidan soja mai taken Grand Service Star (GSS) a shekarar 2009 saboda gudanar da aikin shekaru talatin a gidan soja ba tare da an yi ƙorafi game da shi ko shi ya yi ƙorafi a kan wani.
  2. Ya karɓi kyautar yabo mai taken Commandant’s Award mai ɗauke da shedar yabon Best Foreign Student on Signal Officers Radio Course; wato ɗalibi mafi nagarta a cikin ɗaliban ƙasashen waje waɗanda suka karanci fannin saƙonnin radiyo na soja a ƙasar Amurka a shekarar 1980.
  3. Takardar Yabo (Commendation Letter) a game da ɗalibin da ya rubuta kundin digiri na biyu mafi kyau, a New York ta Amurka, 1993
  4. Takardar Yabo daga shugaban rundunar sojan Najeriya (Chief of Army Staff). Domin samar da tsarin Imel na sojojin Najeriya, 2007.
  5. Kyautar Jinjina da Girmamawa saboda bayar da gudunmawa wajen haɓɓaka ƙwarewar sojojin Najeriya a fannonin aiki, 2008.

Mamba

Yanzu haka shi mamba ne a kwamitin lura da hukumar tsara manhajar karatun makarantun Najeriya daga firmare zuwa aji uku na ƙaramar sikandire (Board Member, Nigerian Educational Research and Deɓelopment Council).

Wannan shi ne Janar Suleimanu Wani, Bakanon Kano a taƙaice.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub