Shafin Farko

Alƙur'an



Alƙur'an

Gabatarwa

Alƙur'an, zancen Allah ne wanda aka saukar da shi ga Annabi Muhammadu (SAW) ta hannun Mala’ika Jibirilu, cikin lafazin Larabci, abin furtawa daki-daki, wanda karanta shi ibada ce.

Sunayen Alƙur’ani

Alƙur’ani yana da sunaye da dama. Kaɗan daga cikin su akwai:

  1. Alƙur’ani (ألْقٌرْآن), kamar yadda Allah ya ambace shi cikin Suratul Baƙara aya ta 185.

    شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِى أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْءَانُ هُدًى لِّلنَّاس...

    Fassara: Watan Ramalana ne wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa yana shiriya ga mutane… (Gumi, 2:185).

  2. Alfurƙaan (ألْفٌرْقَان), kamar yadda ya zo a Suratul Furƙaan, aya ta 1.

    تَبَارَكَ الَّذِى نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَى عَبْدِهِ لِيَكُنَ لِلْعَلَمِينَ نَذِيرًا

    Fassara: Albarka ta tabbata ga Wanda Ya saukar da (Littafi) mai rarrabewa a kan BawanSa, domin ya kasance mai gargaɗi ga halitta (Gumi, 25:1).

  3. Zikr (ذِكْر), kamar yadda ya zo a Suratul Hijri aya ta 9.

    انَّانَحْنُ نَزَّالْنَاالذِّكْرَوَاِنَّالَهُ لَحَفِظُونَ

    Fassara: Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ani), kuma lalle Mu, haƙiƙa, Masu kiyayewa ne gare shi (Gumi, 15:9).

  4. Kitaab (كِتَبْ), kamar yadda ya zo a cikin Suratul Kahfi aya ta 1.

    الْحَمْدُ الِلَّهِ الَّذِى أَنْزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَبَ وَلَمْ يَجْعَلْ لَّهُ عِوَجَا

    Fassara: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bawanSa kuma bai sanya karkata ba a gare shi (Gumi, 18:1).

Saukar da Alƙur’ani


Jabal Nur, dutsen da Kogon Hira ya ke a cikinsa

Abin da ake nufi da saukarwa a nan shi ne Nuzul, kalmar da a nan ta ke ɗaukar ma’anar sadar da shi (Alƙur’ani) daga Ubangiji zuwa ga Annabi Muhammadu (S.A.W.).

Kenan a nan, ana nufin isuwar Alƙur’ani ga zuwa Manzon Allah (S.A.W.). Wannan sauka ta Alƙur’ani kuma ta faru a matakai uku kamar yadda Dakta Musɗafa Murad ya wassafa cewa:

  1. Saukar Lauhul Mahfuz. Cewa an fara saukar da Alƙur’ani a dunƙule a jikin Lauhul Mahfuz. Saboda faɗin Allah Maɗaukakin Sarki cewa:

    بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَجِيدٌ ۞  فِي لَوْحٍ مَحْفُوظٍ ۞

    Fassara: A'aha! Shi Alƙur'ani ne mai girma. A cikin Allo tsararre (Gumi, 85: 21-22).

  2. Sauka ta biyu daga Lauhul Mafuz zuwa Baitil Izza da ke saman duniya. Cewa an sauke Alƙur’ani baki ɗayansa daga Lauhul Mahfuz zuwa saman duniya. Hujjojin da ke tabbatar da wannan su ne faɗin Allah Maɗaukakin Sarki cewa:

    إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ۞ إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُبَارَكَةٍ إِنَّا كُنَّا مُنْذِرِ ۞ ينَشَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي  أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ

    Fassara: Lalle ne Mu, Mun saukar da shi (Alƙur'ani) a cikin Lailatul Ƙadari (daren daraja).  Lalle ne Mu, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mu, Mun kasance Masu yin gargaɗi (Gumi, 97:1, 44:3, 2:1).

  3. Sauka ta uku daga saman duniya zuwa ga Annabi Muhammadu. A Wannan mataki shi ne aka saukar da Alƙur’ani zuwa ga Annabi (S.A.W.) a tsawon shekaru 23, daga shekarar 569 zuwa 592 Miladiyya. Ko kuma a ce daga shekara ta 10 kafin hijira zuwa shekara ta 13 bayan hijirar Annabi (S.A.W.) daga Makka zuwa Madina; abin da ake nufin a nan shi ne cewa, an ɗauki shekaru 10 ana saukar da Alƙur’ani zuwa ga Manzon Allah (S.A.W.) a lokacin da ya ke Makka. Sannan kuma bayan ya bar Makka ya koma Madina da zama, aka ci gaba da saukar masa da shi har na tsawon shekaru 13. Shekarar da Annabi (S.A.W.) ya bar garin Makka ya koma Madina da zama, da ita ake fara ƙirgar shekaru a Musuluci; watao ita ta zama shekarar farko (1) daga nan aka ɗora har yau ta kawo 1438 (shekarar da aka yi wannan rubutu).

    Farkon saƙon da aka fara saukar wa da Annabi (S.A.W.) shi ne ayoyi biyar na farkon Suratul Alaƙ. Wannan shi ne abin da ya fi shahara. Ayoyin su ne:

    اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ ۞ خَلَقَ الإنْسَانَ مِنْ عَلَقٍ ۞ اقْرَأْ وَرَبُّكَ الأكْرَمُ ۞ الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ ۞ عَلَّمَ الإنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ ۞

    Waɗannan ayoyi sun sauƙa gare shi a cikin Kogon Hira, wanda ya ke a cikin Dutsen Haske (جَبَلْ نر) a garin Makka. Wannan kuma ta faru ne saboda kasantuwar wannan waje, wani guri da Annabi (S.A.W.) ya saba zuwa yana keɓewa a ciki tun kafin aiko shi a matsayin Annabi.


Mashigar Kogon Hira, gurin da Annabi Muhammadu (SAW) ya fara karɓar wahayi a sararin duniya

Girman Alƙur’ani

Abin da ake nufi da girma a nan shi ne yawa; irin yawan da Alƙur’ani ya ke da shi. An auna wannan yawa na Alƙur’ani ta sigogi da dama:

  1. Juzu’i wato yanki. Alƙur’ani yana da juzu’i 30. Misalin juzu’i shi ne kamar juzu’in Amma, wanda ke ɗauke da izu-izu guda biyu; izun Sabbi da kuma na Amman kanta.
  2. Izu (Hizbu). Izu shi ne rabin Juzu’i. Akwai izu-izu guda sittin a cikin Alƙur’ani. Wato izu biyu shi ya ke samar da Juzu’i ɗaya. Misalin izu shi ne izun Sabbi, wanda ya fara daga kan sura ta 87 (Sabbi) zuwa sura ta 114 (Nas).
  3. Rubu; rubu shi ne ɗaya bisa huɗu na izu. Saboda haka akwai rubu 240 a cikin Alƙur’ani.
  4. Sumuni. Sumuni shi ne kashi ɗaya cikin takwas na izu; wato za a raba izu zuwa kashi takwas daidai-wa-daida, to ko wane ɗaya ya zama simuni. Akwai simuni 480 a cikin Alƙur’ani.
  5. Surori. Akwai surori 114 a cikin Alƙur’ani. Ta farkon su ita ce Suratul Fatiha, ta ƙarshe kuma Suratun-Nas.

    Sura mafi tsawo daga cikin surorin Alƙur’ani ita ce sura ta 2; wato Suratul Baƙara kenan, wacce ke da ayoyi 286 a salon karatun Hafsu 285 kuma a salon karatun Warshu. Sura mafi gajarta a cikin Alƙur’ani ita ce sura ta 108; wato Suratul Kausar kenan wacce ke da ayoyi uku.

  6. Ayoyi. Dangane da yawan ayoyin Alƙur’ani, akwai wasu abubuwa da suka tasirantu da shi. Waɗannan abubuwa sun haifar da bambance- bambance dangane da adadin ayoyin Alƙur’ani. Daga ciki akwai:
    • Salon Karatu (Ƙira’a). Misali idan ana karatu da Ƙira’ar Warshu, ayoyin (الم ، ذَلِكَ الْكِتَابُ لا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِينَ) ana karanta su a matsayin aya guda.

      Amma a Ƙira’ar Hafsu kuma ana karanta su a matsayin ayoyi biyu kamar haka (الم ۞ ذَلِكَ الْكِتَابُ لا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِينَ۞).

      Kenan, a salon karatu na Warshu, Suratul Baƙara tana da ayoyi 285. A salon karatu na Hafsu kuma, Suratul Baƙara tana da ayoyi 286.

      Saboda haka a salon Karatu na Ƙira’ar Hafsu, Alƙur’ani yana da ayoyi dubu shida da ɗari biyu da talatin da shida (6236), kamar yadda ya zo a tarjamar Gui. A salon karatu na Warshu kuma, yawan ayoyin Alƙur’ani shi ne dubu shida da ɗari biyu da goma sha huɗu (6214) kamar yadda Sharu Bala ya ruwaito.

    • Matsayin Bismillah. Wannan shi ma wani abu ne da ya ke da tasiri wajen kimanta yawan ayoyin Alƙur’ani. Idan aka ƙirga Bismillah a matsayin ayar farko ta kowace sura, yawan ayoyin zai ƙaru. Idan kuma aka ɗauka cewa Fatiha ce kaɗai ta ke da Bismillah a matsayin aya, yawan ayoyin zai ragu.

      Saboda haka a dunƙule, Alƙur’ani yana da ayoyi dubu shida da ɗari biyu da talatin da shida (6,236) idan ka saka Bismillah a matsayin ayar farko ta Suratul Fatiha, sauran surorin kuma, a ƙirga su ba Bisillah. Sai kuma adadin na biyu da ya kama ayoyi dubu ɗaya da ɗari uku da arba’in da takwas (6,348), wannan idan aka ƙirga Bismillah a matsayin ayar farko ta kowace sura in ban da Suratut-Tauba.

      Ayar farko a cikin Alƙur’ani ita ce Bismillar (بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ) farkon Suratul Fatiha.

      Aya ta ƙarshe kuma ita ce (مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ).

      Dangane da aya mafi tsawo kuwa a Alƙur’ani, ita ce aya ta 282 ta cikin Suratul Baƙara:

      يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا تَدَايَنْتُمْ بِدَيْنٍ إِلَى أَجَلٍ مُسَمًّى فَاكْتُبُوهُ وَلْيَكْتُبْ بَيْنَكُمْ كَاتِبٌ بِالْعَدْلِ وَلا يَأْبَ كَاتِبٌ أَنْ يَكْتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ اللَّهُ فَلْيَكْتُبْ وَلْيُمْلِلِ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ وَلْيَتَّقِ اللَّهَ رَبَّهُ وَلا يَبْخَسْ مِنْهُ شَيْئًا فَإِنْ كَانَ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ سَفِيهًا أَوْ ضَعِيفًا أَوْ لا يَسْتَطِيعُ أَنْ يُمِلَّ هُوَ فَلْيُمْلِلْ وَلِيُّهُ بِالْعَدْلِ وَاسْتَشْهِدُوا شَهِيدَيْنِ مِنْ رِجَالِكُمْ فَإِنْ لَمْ يَكُونَا رَجُلَيْنِ فَرَجُلٌ وَامْرَأَتَانِ مِمَّنْ تَرْضَوْنَ مِنَ الشُّهَدَاءِ أَنْ تَضِلَّ إِحْدَاهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحْدَاهُمَا الأخْرَى وَلا يَأْبَ الشُّهَدَاءُ إِذَا مَا دُعُوا وَلا تَسْأَمُوا أَنْ تَكْتُبُوهُ صَغِيرًا أَوْ كَبِيرًا إِلَى أَجَلِهِ ذَلِكُمْ أَقْسَطُ عِنْدَ اللَّهِ وَأَقْوَمُ لِلشَّهَادَةِ وَأَدْنَى أَلا تَرْتَابُوا إِلا أَنْ تَكُونَ تِجَارَةً حَاضِرَةً تُدِيرُونَهَا بَيْنَكُمْ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَلا تَكْتُبُوهَا وَأَشْهِدُوا إِذَا تَبَايَعْتُمْ وَلا يُضَارَّ كَاتِبٌ وَلا شَهِيدٌ وَإِنْ تَفْعَلُوا فَإِنَّهُ فُسُوقٌ بِكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

      Dangane da aya mafi gajarta kuma akwai abin lura: da farko akwai ayoyi masu harrufa biyu-biyu kamar irin su (طه، يس) da sauran su. Sai ta fuskacin aya mai cikakkiyar ma’ana. Nan kuma akwai ayar farko ta cikin Suratur Rahman, wato (الرَّحْمَنُ).

  7. Harrufa. An ruwaito Ibn Kathir yana cewa Alƙur’ani yana da Harrufa 320,015.
  8. Kalmomi. An samu adadi har hawa uku: 77,934; 77,437; da kuma 77,277. Allah ne Mafi sani.

Manazarta:


Alƙur’ani (Babu Shekarar Bugu). Alƙur’anul Kareem, Wa Biha Mishi’it-Tafseerul Mubeen. Wallafar Maɗaba’ar Alƙur’ani ta Fahad.

Amin M. S. M. (1996). Attabsiratu fiy Ulumul Ƙur’an. Faulty of Ƙur’an, Islamic University, Madina – Saudi-Arabia.

Arzai M.N.M (1998). Irshadus-Sibyaani Ila Mubadi’u Ulumil Ƙur’ani Wa Ɗaa’ifatan Min Ahadiithi Fadha’ilihi An Sayyidi Bani Adnaan. Ƙwalejin Koyon Ƙur’ani Kano-Nijeriya. Wallafar Ibrahi Na-Alhaji Umar, Kasuwar Kurmi, Kano.

Gumi, A. M. (1985). Alƙur’ani Mai Girma da Kuma Tarjaman Ma’anoninsa Zuwa ga Harshen Hausa. Madina: Wuri da aka tanada musamman don buga Al-Ƙur’ani Mai girma.

Murad M. (2012). Kaifa Tahfizul Ƙur’an, Ahkaamu Tilawatil Ƙur’an, Ulumul Ƙur’an, Mawaƙifu Li-Ahlil Ƙur’an. Sashen Da’awa, Jami’ar Azhar. Wallafar Darul Fajar Lil-Tiraath, Alƙahira.

Sharu B. (Babu Shekarar Bugu). Huwal Ƙur’anu-Majeed. Wallafar Alhaji Shareef Bala, Gabari, Kano-Nijeriya.