Sarki Musulmi Ahmadu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Ahmadu


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiƙu ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na biyar. Ya gaji ɗan baffansa. An yi masa mubaya’a a masallacin Juma’a na Wurno, a cikin watan Rabbi’ul Auwal, kwanaki uku bayan rasuwar Sarkin Musulmi Aliyu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo.

Sarakuna da wazirai, da sauran jama’a su suka haɗu suka yi masa mubaya’a, sannan kuma suka hore shi da tsayar da sunna da kuma nisantar bidi’a.

Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafa adalci a cikin gari. An samu aminci a lokacinsa, ya kawar da zalunci a harkar cinikayya. Shi ya ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da wata ƙabilar Auzinawa (Azbin). Sun yi yarjejeniya kamar haka: na farko su daina sayen gonaki; na biyu, su daina shigo da gunki; na uku, su amsa kiran sarakunansu; na huɗu, su amsa kiran sa idan ya neme su a kan wasu abubuwan da suka shafi jama’a kamar jihadi da sauran su; na biyar, su giramama shugabannin su.

Sarkin Musulmi Ahmadu, ya yaƙi garuruwa da dama daga ciki akwai Rambori, Tasawa, Gumi, da sauran su. Shi ne sarkin da ya faɗaɗa Daular Musulunci Arewaci.

Ya rasu a garin Chimmola, garin da ya zamar masa fadar mulkinsa kuma aka binne shi a can. Ya rasu ranar Juma’a a daidai lokacin sallar Juma’a a cikin watan Jimada Akhir. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru bakwai da watanni biyu da kwanaki ashirin da shida. Ya rayu tsawon shekaru sittin da ɗaya da kwanaki uku a duniya.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub