Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Aliyu Babba


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Aliyu, ɗa ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne farkon wanda ya fara sarauta a cikin jikokin Shehu Mujaddadi. Mutum ne shi mai basira. Allah ya yi masa baiwa da hankali, da tunani; Mutum ne mai son jama’a kuma gwani a ɓangaren siyasar mulki da ta addini. Yana da ɗaukaka da kuma sakin fuska ga jama’a. Haƙiƙa yana da tawakkali da kuma miƙa al’amura ga Allah.

Sarkin Musulmi Aliyu ɗan Muhammadu Ballo, shi ne Sarkin Musulmi na huɗu. An yi masa mubaya’a Masallain Shehu Usmanu Ɗanfodiye da ke Sakkwato a cikin watan Shawwal, bayan rasuwar ɗan’uwan mahaifinsa Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu.


Masallacin Shehu, gurin da aka yi wa Sarkin Musulmi Aliyu Babba Mubaya'a.

Sarkin Musulmi Aliyu ɗan Muhammadu Ballo, ya yaƙi manya da ƙananan garuruwa, wasu kuma ya yi sulhu da su. Daga cikin garuruwan da ya yaƙa akwai Madarumfa, Zoma, Haɗejiya, Zamfara, Kabi, Argungun, Kwatarkwashi, da sauran su. An ce yaƙuƙuwan da ya yi ba za  su gaza ashirin ba.

Sarkin Musulmi Aliyu ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen gyaran masallatai, ginin ganuwa, ginin ƙofofin gari tare da sabunta wasu. Shi ne farkon wanda ya saka wa ƙofofin gari ƙyamare/gabun ƙarfe.

Ya rasu a garin Wurno, ranar Juma’a a cikin watan Rabbi’ul Auwal. An yi masa ƙabari kusa da mahaifinsa daga ɓarin dama. Ya yi sarauta tsawon shekaru bakwai. Ya rayu tsawon shekaru hamsin da uku a duniya.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub