Hijirar Shehu Ɗanfodiye

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hijirar Shehu Ɗanfodiye


Gabatarwa

Hijra kalma ce ta Larabci wacce ke da ma'ana ta ƙaura; tashi daga wani gari a koma wani garin da zama. Shehu Usmanu ya yi ƙaura daga garin Ɗagel, ya koma dajin Gudu da zama wanda daga baya ya zama gari. Gagarumar nasarar da kiran Shehu ɗan Fodiye ya samu, shi ne abin da ya aukar da ƙiyayya tsakanin Shehu da sarakunan daular Gobir ƙarƙashin Yunfa; abin da ya kai ga shi sarki Yunfa baiwa Shehu umarnin ficewa daga ƙasar Gobir wanda kuma hakan ce ta saka Shehu tashi daga Ɗagel ya koma Gudu da zama kama-kama har zuwa Sakkwato.


Wani Sashen Gidan Shehu a Ɗagel

Daga Ɗagel Zuwa Gudu

Kiran da Mujadaddi Shehu Ɗanfodiye ya yi, ya samu gagarumar karuwa a Ƙasar Hausa, abin da ya haifar da ƙiyayya mai zafi daga malamai da sarakunan Ƙasar Hausa. Saboda haka sai su malaman da sarakuna suka haɗu a kan matsanta wa Shehu da almajiransa. Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya ce, “Dukkanin masu mulkin garuruwan sun jajirce wajen bishe wannan haske, suna yi wa Shehu da jama’arsa makirce-makirce da ƙulle-ƙulle, saboda haka suka haɗa kawukansu dan su yaƙi Shehu da jama’arsa”.

Ana cikin haka sai sarkin Gobir Nafata ya kafa dokar hana kowa yin wa’azi in banda Shehu shi kaɗai. Sannan kuma cewa ba mai sake karɓar Musulunci sai wanda ya gada daga iyayensa; duk kuma wanda bai gada ba to ya koma addininsa na gado. Sannan kuma ya hana naɗa rawani ga maza mata kuma aka hana su saka suturar da za ta suturce dukkan jikin su (hijabi mai yalwa). Nafata bai jima da kafa waɗannan dokoki ba sai ya mutu.

Hijirar Farko

Hijirar farko a tarihin Jihadin Shehu Usamanu Mujaddadi an yi ta ne zuwa garin Gimbana. Wannan kuwa ta faru bayan rasuwar Sarkin Gobir Nafata. Da ɗansa Yunfa ya gaje shi, sai ya tsananta wannan doka da Nafata ya kafa game da Shehu da almajiransa har ta kai ga Malam Abdurrahman ya yi gudun hijira shi da jama’arsa zuwa wani gari da ake Kira Gimbana. Nan ma dai basu tsira ba, Sarki Yunfa ya tura rundunar yaƙi aka yaƙe su. Abin da ya haifar da karkashe jama’a da dama’ da kuma kama ribatattun yaƙi, da tarwatsawa su daga wannan gari zuwa wasu garuruwan a cikin ƙasar Kabi.


Wani Sashen Gidan Shehu a Ɗagel

Zuwan Shehu Fadar Yunfa

Bayan afkuwar waccan kisan gilla da aka yi wa alajiran Shehu sai Sarkin Gobir Yunfa ya kirayi Shehu. Shehu ya amsa ya tafi zuwa gare shi tare da rakiyar ƙaninsa Abdullahi bn Fodiye da kuma babban abokin sa Umaru Alkammu. Da suka isa, sai suka shiga gare shi, suna shiga sai ya harbe su da bindigarsa da nufin ya halaka su. Nan take sai wannan harbi ya juya gare shi, saura ƙiris ya ƙone shi, amma dai bai ƙone shin ba. Su kuma su Shehu babu wanda ya kaɗu da faruwar wannan lamari, maimakon haka sai ma abin ya basu dariya. Jim kaɗan bayan wani ɗan taƙin lokaci, sai shi Yunfa ya kusance su, ya zauna, sannan ya ce da su, ku sani! Haƙiƙa bani da wasu maƙiya a duniya kamar ku. Ya bayyana musu ƙiyayyarsa gare su, su kuma suka nuna masa cewa basa jin tsoron sa. Allah bai bashi nasara a kan su ba, suka fice lami-lafiya daga gare shi, suka koma masaukin su. Bayan sun fito, sai Shehu ya ce da su kar su bari wani ya ji wannan magana. Sannan ya yi addu’a a kan haka, su kuma suka amsa masa da amin. Daga nan sai suka koma garin su Ɗagel.

Shehu ya bar Ɗagel

Ganin sun samu wancar galaba a garin Gimbana, sai girman kai da ɗagawar jama’ar Yunfa suka ƙaru, saboda haka sai suka wuce zuwa Ɗagel, suka ɓullo wa gidan Shehu ta Gabas. Da suka kai gurin, sai suka afka wa jama’ar Shehu. Jama’ar Shehu kuma suka kare kansu, suka ƙwace sauran ‘yan’uwan su da aka kamo a garin Gimbana. Su kuma kafirai, sai suka riƙi masun da suka je gurin da su, suka kai wa sarkin Gobir, suka ce da shi waɗannan su ne masun da jama’ar Shehu suka harbe mu da su, suka kuma ƙwace dukkan abubuwan da ke hannuwanmu.

Wannan abu ya yi matuƙar ɓata wa Sarki Yunfa rai. Daga nan kuma sai ya aike wa da Shehu saƙon cewa ya fice ya bar masa ƙasarsa, kuma idan ya tashi tafiya kar ya fita da kowa sai iyalansa. Shi kuwa Shehu ya ba shi amsa da cewa zai fita ya bar masa garin, amma tare da dukkan jama’ar sa, ai ƙasar Allah tana da faɗi. Shehu ya bar garin Ɗagel a ranar Alhamis, rana ta goma sha biyu a cikin watan Zulƙa’adah na shekara ta dubu ɗaya da ɗari biyu da goma sha takwas (Alhamis, 12/11/1218) na hijirar Manzon Allah (SAW).

Shehu a Gudu

Da Shehu ya fita daga Ɗagel ya tafi zuwa Kuran Gizo, sai Ɗamba, sai suka bi ta Kalmalu, sannan sai Farkaji, sai Ruwawar, sannan suka sauka a Gudu. Da suka isa Gudu, sai suka taras da Aliyu Jeɗo ya gina wa Shehu gida a wannan daji.

Bayan wani ɗan lokaci da isar Shehu Gudu sai ya umarci dukkan mabiyansa da su koma Gudu. Haka jama’ar Shehu suka riƙa tururuwa zuwa Gudu. Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya  ce, “haka jama’a suka riƙa riskar mu, wasu da iyalansu da dukiyoyinsu wasu da iyalan ba dukiyar wasu da ba iyalan ba dukiyar”, saboda tare su a hanya da jama’ar Yunfa su ke yi; suna karkashe su suna ƙwace musu dukiya.

Mubaya’a

Lokacin da jama’ar Shehu suka taru a Gudu, sai manyan ciki suka yi shawarar cewa, ya kamata a samu shugaba kuma jagora guda ɗaya wanda dukkan al’amuran Musulmi za su zama a hannunsa. Baki ɗayan su sai suka haɗu a kan cewa, Shehu ne ya dace da wannan matsayi. Saboda haka sai suka yi masa mubaya’a. Ƙaninsa Abdullahi bn Fodiye, shi ya fara yi masa mubaya’a, sai kuma ɗan sa Muhammadu Ballo, sai babban abokin sa Umaru Alkammu, sai kuma sauran jama’a. Sun yi masa wannan mubaya’a bisa karantarwar addinin Musulunci (kitabu-wa-ssunna) a daren ranar Alhamis a ƙarƙashin wata itaciyar faru.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Boyi U.M. (Ba shekarar bugu). Mallam Abdullahi Ɗan Fodiyo Rayuwarsa da Ayyukansa. K.U.B. Printing Press Sokoto Nigeria.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub