Hubbaren Shehu Ɗanfodiye

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hubbaren Shehu Ɗanfodiye


Gabatarwa

Hubbaren Shehu, gida ne na Shehu Usmanu Ɗanfodiye, wanda ɗan sa Muhammadu Ballo ya gina masa a cikin unguwar Sabon Birni da ke cikin garin Sakkwato. Bayan zaman shekaru biyu da Shehu Usmanu ya yi a cikin wannan gida, sai jinyar ajali ta kama shi a cikin ɗakin ɗaya daga cikin matansa mai suna Hawwa'u wacce ita ce mahaifiyar sarkin Musulmi Muhammadu Ballo da kuma Nana Asma'u. Bayan rasuwar Shehu, sai aka binne shi a cikin wannan gida. Tun daga wannan lokaci, sai wannan gida ya canja suna daga gidan Shehu ya koma Hubbaren Shehu.

Asali

Kalmar Hubbare, kalma ce ta Fullanci, wacce ke da ma’ana ta gurin binne salihan mutane; wato maƙabartar waliyayyai kenan. Saboda haka idan aka ce Hubbaren Shehu, to ana nufin Maƙabartar Shehu. Ita kuwa wannan maƙabarta ta Shehu, asalin ta gida ne na shi Shehu Usmanu Ɗanfodiye, wanda ɗansa, Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya gina masa shi a cikin shekarar 1809, bayan shi Muhammadu Ballon ya koma garin Sakkwato. Gidan yana nan a cikin wata unguwa a cikin garin Sakkwato da ake kira Sabon Birni.

Shehu Mujaddadi, ya rayu tsawon shekaru biyu a wannan gida, shi da iyalansa da sauran jama’arsa masu yi masa hidima. A lokacin da jinyar ajali ta kama shi yana ɗakin ɗaya daga cikin matansa wacce ita ce Hawwa’u mahaifiyar Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, da kuma fitacciyar marubuciyar nan Nana Asma’u. Saboda haka sai aka bar shi cikin wannan ɗaki, ita kuma aka sake gina mata wani ɗakin daban, duk dai a cikin gidan.

Bayan da ajalin Shehu ya yi a wannan ɗaki, sai aka haƙa masa ƙabari a wannan ɗaki, aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Tun daga wannan lokaci sai jama’a waɗanda mafiya yawan su Fulani ne, suka riƙa kai ziyara zuwa wannan gida. Waɗannan Fulani masu ziyara, sai suka riƙa kiran wannan gida da Hubbaren Shehu.

Ba jimawa da rasuwar Shehu, sai kuma ɗan sa, wanda ya sallace shi mai suna Muhammad Sambo ya rasu, sai shi ma aka binne shi a wannan ɗaki da aka binne Shehu. Bayan rasuwar Muhammadu Sambo, sai kuma wani ɗan na Shehu mai suna Hassan shi ma ya rasu kuma aka binne shi a wannan ɗaki. Saboda haka sai wannan gida ya rikiɗe ya koma gurin binne makusanta daga cikin almajiran Shehu da kuma sauran ‘ya’ya, mata, da kuma haular Shehu har zuwa yau.

Sannan kuma bayan zamowarsa Hubbaren, sai ya zama wani gurin ziyara da jama’a ke zuwa daga ciki da kuma wajen Nijeriya.

Fasalin Hubbaren Shehu

Kafin fasalta Hubbaren Shehu, bari mu fara da fasalta yadda gidan Shehu ya ke, asalin wannan gida na Shehu, gida ne mai faɗi, wanda ke da sassa daban-daban. Daga cikin waɗannan sassa, akwai:

Biyo mu ka fara shiga gidan ta wannan ƙofar.


Ƙofar Gidan Shehu

 • Farfajiyar gida/Tsakar gida.
 • Sashen iyalan Shehu, wanda ya kasu zuwa sassa huɗu da kowace ɗaya daga cikin matansa ke zaune ita da ‘ya’yanta da duk wasu abubuwa nata.
 • Sashen sa-ɗakan Shehu.
 • Majalisar Shehu.
 • Sashen wasu daga cikin al’majiran Shehu.

Waɗannan sassa na gidan Shehu, su ne aka mayar da su sassan wannan Hubbare na Shehu, tunda dama gidan ne aka mayar da shi Hubbare. Ga su kamar haka:

 1. Soro: Daga farko akwai soron gidan wanda ke da ƙofofi guda uku kamar haka:
  • Ƙofar Gida: Ita ce asalin ƙofar gidan wacce ke kallon Yamma, ita ke shigar da mutum zuwa cikin Hubbaren baki ɗayansa.
  • Ƙofar Arewa: Idan aka shiga cikin soron gidan, akwai ƙofa daga Arewa.
  • Ƙofa daga Gabas: Daga cikin soro akwai wata ƙofa daga Gabas, wacce kuma ita ke shigar da mutum zuwa asalin farfajiyar Hubbaren.
 2. Farfajiyar Hubbare: Hubbaren yana da wata farfajiya mai tsawo da kuma matsakaicin faɗi; ba tsukakkiya ba ce, sannan kuma ba faffaɗa ba. Wannan farfajiya ita ke sada mutum da dukkan sauran sassan Hubbare.

 3. Majalisar Shehu: da zarar an fito daga wannan soro na shiga Hubbaren ta ƙofar Gabas aka kuma fuskanci gabas ɗin, to za a hangi wani zaure, wannan zaure nan ne asalin bigiren da Shehu ke zama yana bayar da karatu.

 4. Majalisar Shehu

 5. Sashen Kudu: Wannan sashe na Kudu, yana da rassa:
  • Sashen matan Shehu guda huɗu; Hawwa'u, Gabɗo, Hajjo, da kuma A'ishatu Shaturu.
  • Sashen sa-ɗakan Shehu Maryama.

  • Sashen Hubbaren Hawwa

 6. Sashen Arewa: Ƙaburbura ne na jama'a da suka shafi jinin Shehu.
 7. Sashen Arewa daga Gabas: Nan ne asalin inda ƙabarin Shehu da 'ya'yansa da wasu daga cikin almajiransa su ke. Wannan guri yana da zauren da ake shiga ta cikinsa, ƙofar zauren tana kallon Yamma: Idan aka shiga ciki kuma akwai wata ƙofar da ke kallon Kudu, daga wajensa kuma tana kallon Arewa. A cikin wannan guri akwai:
  • Ƙabarin Shehu: A cikin wannan ɗaki, wanda aka yi wa fasalin ɗaki da rumfa ko kuma a ce ciki da falo. Ɗakin yana da ƙofofi guda biyu; ɗaya daga ɓarin Yamma, ɗayar kuma daga ɓarin Arewa na ɗakin. Idan aka shiga falon, to kuma akwai wata ƙofa guda ɗaya da ke kallon Yamma wacce ke isar da mutum ga asalin ƙabarin Shehu. A cikin wannan ɗaki akwai ƙaburbura guda uku da aka lulluɓe da baiƙin zani/yadi mai ƙyalƙyali amma ƙyalƙyalin ba can ba, da aka yi wa ado da zanen taurari da kuma rubuce-rubuce cikin rubutun Larabci da aka yi wa launi da ruwan gwal. Ƙaburburan su ne; ƙabarin Shehu da kuma 'ya'yansa guda biyu; Muhammadu Sambo da Hassan. Wannan ɗakin shi ne asalin bigiren ɗakin Hawwa'u matar Shehu wanda Shehu ya yi jinya a ciki, bayan rasuwarsa kuma aka binne shi a gurin.

  • Ƙubbar Shehu ta waje


   Ƙubbar Shehu ta ciki

  • Ƙabarin Nana Asma'u: Bayan ɗakin da ƙabarin Shehu ke ciki daga Gabas, akwai wani ɗaki da ƙabarin Nana Asma'u da Ahmadu Rufa'i su ke ciki.

  • Ƙabarin Hassan Mu'azu da Abubakar III: Ɗaki na biyu daga gabas, ɗaki ne da ƙaburburan Hassan Mu'azu da kuma sarkin Musulmi Abubakar III ke ciki.
  • Rumfa/Baranda: Daga Arewa da waɗannan ɗakuna guda uku, akwai wata rumfa/baranda wacce wani ɗan kwararo ya raba su a tsakiya da waɗancan ɗakuna. Wannan rumfa, tana ɗauke da ƙaburbura guda goma a jere. Idan aka koma daga ɓarin Yamma na wannan rumfa, za a samu ƙaburburan mutane kamar haka:
   i. Ƙabarin Abdurrahman Suyuɗi. ii. Ƙabarin Liman Aliyu. iii. Ƙabarin Aliyu Jeɗo. iv. Ƙabarin Abdurrahaman ɗan Ahmad Rufa'i. v. Ba a tantance sunan wanda ke ƙabarin ba. vi. Ba a tantance sunan wanda ke ƙabarin ba. vii. Ƙabarin Hodiyo ɗan Abdulƙadir. viii. Ƙabarin Ahmadu rufa'i ɗan Atiku. ix. Ƙabarin Muɗegel. x. Ƙabarin A'ishatu 'yar Umar.
 8. Sashen Arewan Gabas: Daga Bayan wancan ɗaki da ƙabarin Shehu ke ciki, akwai wani sashe da ke ɗauke da ƙaburburan matan Shehu da kuma wasu sarakunan Musulunci. Daga ciki akwai:
  • Ƙabarin Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo.
  • Ƙabarin Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi.
  • Ƙabarin Sarkin Musulmi Attahiru ɗan Aliyu.
  • Ƙaburburan Matan Shehu.
  • Sashen Gabas: Ƙaburbura ne na haular Shehu a ciki.

Manazarta:


Balarabe B. (2016). Hubbaren Shehu A Mahangar al'adun Hausawa. Kundin Digirin Kammala Karatun Digiri Na Farko (B.A. Hausa), Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiye, Sakkwato.

Junaidu W. (1961). Hubbaren Mujadaddi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Sifawa Printing and Enterprise, Sokot - Nijeriya.

Tattaunawa da Malam Ahmad Bala Maibuɗin Hubbare.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub