Kiran Shehu Ɗanfodiye

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kiran Shehu Ɗanfodiye


Gabatarwa

Kira shi ne matakin farko na jahadin Shehu. Shehu ya fara kiran jama’a zuwa ga bin haƙiƙanin addinin Musulunci da kuma watsar da dukkan wani abu sabo ko wanda ba addini ba a garin Ɗagel, lokacin bai wuce shekaru 20 da haihuwa ba a cikin shekarar 1188 ta Hijirar Annabi Muhammadu (SAW) wanda kuma ya yi daidai da 1774 miladiyya. Wannan kira na Shehu ya yi shi a cikin shekaru 30 (1774 - 1804).

Tushe

Buƙatar wannan kira na Shehu ta taso ne bayan da Shehu ya nazarci jama’ar Ƙasar Hausa ya kuma taras cewa, masu mulkin Ƙasar Hausa a wannan zamanin kafirai ne kai tsaye ko kuma fasiƙai, mafiya yawa daga cikin malamai kuma ma’abota bidi’a ne, saboda haka sai jama’a suka zamo suna kafircewa Allah a aƙida, sannan kuma suna saɓa masa. Saboda haka sai Shehu ya yi ƙoƙari wajen ilimantar da waɗannan jama’a.

Wa’azi, da kuma rubuta waƙoƙi cikin harshen Fullanci da Larabci, su ne hanyoyin da Shehu ya riƙa bi wajen rushe gurɓatacciyar bauta, rushe bidi’a, kawar da tsafi, da kuma yaɗa sunna da ilimantar da jama’a. Yakan fita a duk daren Juma’a dan yin wa’azi. Sauran ranaku kuma (Asabar zuwa Laraba) yakan fita dan bayar da karatu a fannoni ilimin addinin da kuma ganawa da baƙi. Bayan la’asar kuma, yakan fita dan bayar da darasi a fannonin fassarar Alƙur’ani, hadisai, fiƙihu, da kuma sufanci.

Bayan waɗannan lokuta da Shehu ke gudanar da waɗannan ayyuka a Ɗagel, yakan kuma samu wani lokaci ya fita zuwa wasu garuruwan dan yaɗa wannan kira nasa ta hanyar wa’azi. A wannan lokaci duk garuruwan da Shehu ya je, yakan koma gida; wato garin Ɗagel.


Ƙofar Gidan Shehu a Ɗagel

Haka Shehu ya ci gaba da wannan kira nasa kuma jama’a suna amsa, suna tururuwa zuwa gare shi, har sai da ya kai garuruwan Kabi, ya kiraye su zuwa ga tsarkake imanin su da kuma Musuluncin su, da kyautatawa, da kuma barin mummunar bauta. Sai aka samu jama’a masu yawa suka tuba, sannan kuma suka bishi zuwa garin sa ƙungiya-ƙungiya a lokacin da ya koma gida, suna sauraron wa’azin sa. Da waɗannan jama’a Allah ya buɗe kiran Shehu.

Kiran Shehu a Fadar Bawa

A farkon kiran nasa, Shehu ya zamo mai nisantar sarakuna, baya zuwa fadodinsu, baya hulɗa da su. Daga baya kuma da jama’arsa suka yawaita, sai ya ga akwai buƙatar kiran sarakuna zuwa ga bin Allah tsantsa. Saboda haka sai ya je fadar sarkin Gobir Bawa, ya sanar da shi nagartaccen addinin Musulunci, ya kuma kira ye shi da bin wannan tafarkin da kuma tsayar da adalci a cikin mulkin sa. Daga na sai Shehu ya koma gida.

Kiran Shehu a Garuruwan Zamfara

Bayan wannan kuma sai Shehu ya tafi zuwa garuruwan Zamfara, inda ya shafe kimanin shekaru biyar yana kira zuwa ga Allah. Jama’a da yawa sun amsa wannan kira na Shehu.

Yarjejeniyar Shehu da Bawa

Karɓuwar da wannan kira na Shehu ya samu a waɗannan yankuna, ya matuƙar tayar da hankalin sarakunan Ƙasar Hausa. Da Bawa ya tambayi labarin Shehu aka gaya masa, sai ya aikawa dukkan malaman da ke ƙasar sa cewa yana neman su a cikin watan Zulhijja, da nufin idan suka je zai kashe su. A lokacin da Shehu ya isa Gobir, sarkin Gobir Bawa ya fita zuwa Sallar Idi. Haka nan ma Shehu ya fita tare da jama’ar Musulmi zuwa masallaci a kan raƙuminsa. Da jama’ar Bawa suka hangi Shehu, sai suka tafi zuwa gare shi suka bar sarki Bawa shi kaɗai.

Faruwar wannan lamari ya yi matuƙar ƙona zuciyar Bawa. Da aka idar da salla, sai Bawa ya tara malamai, Shehu ma ya shiga cikin su. Bawa, ya ɗauki sama da awa guda ya kasa magana. Sai wani daga cikin aminan sa ya miƙe tsaye ya ce, ya wane, babu wani mutum da ya isa aikata wannan face da izinin Allah. Daga nan sai sarki Bawa ya yi umarni cewa a baiwa Shehu da almajiransa misƙalin zinare ɗari biyar. Daga nan sai Shehu ya miƙe tsaye ya ce da Bawa, “Ni da mutane na bama buƙatar dukiyarka, maimakon haka, ina buƙatar abubuwa biyar a wajenka: na farko, ka ƙyale ni na yi kira a ƙasarka; na biyu, kar a hana duk wanda ke son amsa kira na; na uku, a girmama duk wanda ke saka hula ko naɗa rawani; na huɗu, ka saki dukkan waɗanda ka tsare a kurkukunka; na biyar, kar a ɗorawa talakawa harajin da zai cutar da su”. Nan take bawa ya amince da waɗannan buƙatu na Shehu yana mai cewa, “Na yarje maka, sannan kuma na baka dukkan abin da ka roƙa. Kuma na yarje maka dukkan abubuwan da ka ke son aikatawa a waɗannan garuruwan namu”. Albarkacin Shehu aka saki sarkin Zamfara Abarshi daga kurkuku.

Daga nan sai Bawa ya roƙi albarkar Shehu cewa ya buɗe masa Maraɗi, garin da ya gagari Bawa a fagen yaƙi. Sai Shehu ya amsa masa da cewa, da sannu za ka ci Maraɗi da yaƙi tun kafin ka sauka daga kan abin hawanka. Sannan Shehu ya gargaɗe shi da cewa, kar ya kuskura ya wuce Maraɗi bayan ya yi nasara. Daga nan sai Shehu ya hau raƙuminsa, ya yi bankwana da sarki.

Bayan tafiyar Shehu, Bawa ya ƙura wa Shehu ido kamar na awa guda, sannan sai ya juya ga mutanensa, ya kiraye su har sau uku, yana mai cewa, “Ya ku mutanen Gobir, ku kalli wancan Bafilatanin mutumin, babu wani wanda ya fi shi ɗaukaka in banda manyan garin ku”.

Daga nan kuma sai Bawa ya fara shirya rundunar yaƙi zuwa Maraɗi. Bayan sun gama shiri suka ɗauki hanya zuwa Maraɗi, da isar su Maraɗi, basu ko sauka daga kan abin hawansu ba suka ci Maraɗi da yaƙi. Bayan samun nasara, sai shi Bawa ya tsaya ya ce, mun ga aikin addu’ar Shehu, saura kuma mu ga aikin takkubanmu, saboda haka sai suka wuce zuwa gaba. Suna zuwa Dankish ko Dankeshi, sai aka tarwatsa rundunar tasa, aka kashe shi, shi da ɗansa.

Yayin da Shehu ya samu gagarumar nasara a waɗannan garuruwa na Zamfara, sai ya koma gida Ɗagel.

Kiran Shehu a Kogin Kwara (Ilorin)

Bayan mutuwar sarkin Gobir Bawa, sai kuma ƙaninsa Yakubu ya gaje shi, wanda shi kuma ya tsananta ƙiyayyarsa da Shehu, ya riƙa shisshirya wa Shehu makirce-makirce. Bayan haka kuma sai ya shirya runduna ya tafi Dankish dan ya ɗauki fansar ɗan’uwansa. Sai Shehu ya aika masa cewa ya dawo, har ya kusa juyowa, sai jama’ar sa suka hana shi dawowa suka ci gaba da tafiya. Allah ya ƙaddara mutuwar sa a can bai dawo zuwa gidansa ba.

Shehu ya ci gaba da kira, ya runtuma ya yi yankin Kabi har sai da ya dangana da Kogin Kwara, wanda shi ne babban kogi a wannan yankin, ya kai zuwa wani gari mai suna Ilo (Ilori). Duk gun da ya je jama’a suna amsa masa. Daga nan kuma sai ya dawo gida Ɗagel.

Makircin Nafata

Bayan mutuwar sarki Yakubu, sai ƙaninsa Nafata ya gaje shi, wanda shi ya fi tsananta ƙiyaya ga Shehu da kuma jama’arsa. Daga cikin irin ƙulle-ƙullen da ya ke yi wa Shehu, wata rana sai ya tara tsofaffin ƙasarsa, da sauran manyan mutanen ƙasar, ya saka kujera ya zauna a gaban su, sannan ya ce da Shehu ya shigo da nufin ya kunyata Shehu. Da Shehu ya shiga ciki, sai Shehu ya jefe shi da wani abu, sai ya bugi ɗagutu a wuya, nan take ya faɗi sumamme jama’arsa suka ɗauke shi zuwa gidansa. Daga nan kuma sai Shehu ya fita ya koma masaukin sa, ya yi shiri ya koma gida garin Ɗagel.

Makircin Yunfa

Bayan mutuwar sarki Nafata, sai Yunfa ya gaje shi, wanda shi kuma ƙiyayyarsa ga Shehu da kuma jama’arsa ta fi dukkan sarakunan da suka gabace shi. Daga cikin irin ƙulle-ƙulle da makirce-makircen da Yunfa ya ke yi wa Shehu, akwai wata rana da ya haƙa rami ya shimfiɗa tabarma a kan ramin sannan ya gayyaci Shehu da almajiransa cewa su zo a tattauna. Da Shehu ya isa wannan waje, sai ƙanin sa Abdullahi bn Fodiye ya yi nufin zama a kan wannan tabarma, sai Shehu ya ce da shi kar ya zauna. Haka Shehu ya zauna a kan wannan tabarma har aka kammala tattaunawa bai rufta ba. Daga nan sai hankalin Yunfa ya sake tashi.

Haka Shehu ya ci gaba da yin kiransa ta hanyar wa’azi da karantarwa na tsawon shekaru 30 (1774 – 1804). Gawurtar wannan kira na Shehu shi ne abin da ya jefa barazana a cikin zuciyar Yunfa har ta kai ga kori Shehu da jama’arsa daga garin Ɗagel.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Boyi U.M. (Ba shekarar bugu). Mallam Abdullahi Ɗan Fodiyo Rayuwarsa da Ayyukansa. K.U.B. Printing Press Sokoto Nigeria.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub