Sarki Musulmi Muhammadu Ballo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Muhammadu Ballo


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiye, almajirinsa, wazirinsa, daga ƙarshe kuma magajin Shehu. Mutum ne masani, jarumi, haziƙi, fasihi, kuma marubuci. Jarumtakarsa bata ɓuya ba, shi ya ci birnin Alƙalawa da yaƙi; cibiyar Daular Gobir, ya shiga har gida ya fatattaki jama’ar sarki Yunfa, ya kashe shi. Ya halarci yaƙuƙuwan jahadin Shehu har sama da arba’in.

An haife shi tun kafin kiran Shehu. Da shi aka yi kiran Shehu, da shi aka yi hijira, da shi aka yi jihadi, daga ƙarshe kuma shi ya kafa Sakkwato, ya ginawa Shehu gida da masallaci wacce ta zama cibiyar Daular Musulunci.

Haihuwa

Muhammadu Ballo ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiye. Sunan mahaifiyarsa Hauwa’u. An haifi Sarkin Musulmi Muhamadu Ballo a ranar Laraba cikin watan Zilƙa’ada na shekarar 1195 hijira a garin Gidan Shehu na Ɗagel. Kenan, an haife shi bayan Shehu ya fara kira da shekaru bakwai (1188 – 1195 hijira).

Sunansa shi ne Muhammad (محمد ), laƙabinsa kuma shi ne Ballo (بَلُّو ), wacce kuma Bafilatanar kalma ce da ke da ma’ana ta mataimaki; kamar yadda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya faɗa a tsokacin da yi a littafin Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur na Muhammadu Ballo.


Gidan Shehu na Ɗagel

Tasowarsa

Sarkin Musulmi ya tashi da kyakkyawar tarbiyya a hannun mahaifinsa Shehu Usmanu bn Fodiye. Shehu Usmanu shi ne malaminsa na farko, a hannunsa ya fara karatun Alƙur’ani da sauran ilimomi na wajibin farko. Daga baya kuma ya koma hannun baffansa Abdullahi bn Fodiye; shi kuma Abdullahi ƙanin Shehu ne sannan kuma alajirinsa. Shi Abdullahi shi ya karantar da Muhamau Ballo abubuwan da suka shafi Larabci kamawa tun daga yaren, zuwa nahawu, su sarfu har zuwa kan balaga, da sauran su.

Haka nan kuma sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya yi karatuttuka a hannu Shehi Muhammadu Nuraz-Zaman. A wajen sa ya koyi fassarar Alƙur’ani, ilimin usuluddin, ilimin haƙiƙa, da sauran ilimomi masu tarin yawa. Haka ya yi ta karatu har sai da ya zama babban malami. A wannan fage na neman ilimi, an ce Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya karanta littattafai dubu ashirin da ɗari uku (20,300) ko fiye da haka.

Haliftakarsa

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya zamo halifan Shehu Usmanu bn Fodiye a wayewar garin daren da Shehu ya rasu. Musulmi sun yi masa mubaya’a a gidan malam Shafa. Ɗan’uwansa Muhammadu Sambo shi ya fara yi masa mubaya’a.


Masallacin Sarki Musulmi Muhammadu Ballo

Yaƙuƙuwan da ya yi

Bayan rasuwar Shehu Usmanu da kuma zamowar Muhammadu Ballo Sarkin Musulmi, jihadi ya ci gaba bai tsaya ba.

Tun da farko, a cikin watan Rajab na shekarar farko da zamowarsa halifa jama’ar Zamfara suka yi ridda, saboda haka Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya tashi runduna suka rankaya zuwa Burmi, suka yi ta yaƙi har sai da suka samu nasara. Haka nan a cikin watan Zulƙa’ada, malam Abdussalam ya fice ya jiɓinci al’amuran kafirai, sai Muhammadu Ballo ya tashi tsaye ya yaƙe su, bai gushe ba yana yaƙar su har sai da ya ci Kware, a ƙareshen watan Safar.

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya yaƙi Kadaye, Gunki Ganƙa, Kalambaina, da Dakarawa; ya yi yaƙi da rundunar haɗaka ta sarkin Gobir Ali da kuma Auzinawa (Azbin) da Abaru ya jagoranta; ya fatattake su har sai da suka tsere.

Sannan ya yaƙi rundunar haɗaka ta Zamfara da Bauchi. Sai kuma wata rundunar ta haɗaka da ta tattara mayaƙa daga sassan Katsina, Gobir da kuma Azbin, haka nan ma Maraɗi. Dukkan waɗannan yaƙe-yaƙe an yi su cikin nasara.

Wasu garuruwan yankunan Zamfara da Gwandu kamar irin su Anka, na daga cikin guraren da Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya yaƙa. An ƙiyasta cewa ya yi yaƙuƙuwan da basu gaza arba’in da bakwai ba.

Rasuwarsa

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya rasu a gidansa da ke Wurno; gidan da ya ke zuwa yana keɓewa dan yin bauta ga Allah (Ribaɗ). Ya rasu a ranar Alhamis da yamma, cikin shekarar 1253 hijirar Annabi (SAW). Kalmomin sa na ƙarshe su ne (لااله الاالله محمدرسولالله ). An yi jana’izar sa bisa sunna, an kuma binne shi a wannan gida kamar yadda ya yi wasiyya da a yi masa.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub