Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muhammad Sa'ad Abubakar III, CFR, MNI

Gabatarwa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar III, shi ne sarkin Musulmin Najeriya na 20 da ake ƙiyasta yawansu ya kai kimanin mutum miliyan 80 (The Authority, 2016). Shi soja ne mai ritaya, sai da ya kai matsayin birgediya janaral (Brigadier General) a soja kafin zamowarsa sarkin Musulmi.

Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’adu Abubakar ya zamo ɗaya daga cikin Musulmi 500 da suke da tasiri a duniya, sannan kuma a cikin waɗannan mutane 500, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar III shi aka ɗauka ya zama na goma sha shida a cikinsu (Gumel, ba kwanan wata).

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, mutum ne mai sadaukar da kai, son jama’a, da kuma haƙuri. Haka nan kuma ya yi fice wajen son zaman lafiya da haɗin kai. “Sultan Sa’ad sananne ne wajen sadaukar da kansa ga Najeriya, jama’arta, da kuma yunƙurin samar da zaman lafiya tsakanin addinai da al’adun da ke karo da juna”, Religion for Peace (ba kwanan wata).


Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Haihuwa

An haifi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar III a ranar 24 ga watan Agusta na shekarar 1956 a garin Sakkwato, a Najeriya. Shi ɗa ne ga Sarkin Musulmi na 17, Mai Alfarma Siddiƙ Abubakar ɗan Usuman.

Karatu

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi karatunsa na firmare a makarantar firmare ta ‘Sultan’s Ward Primary School’, da ke Sokoto. Bayan kammala firamare kuma sai ya shiga kwalejin Barewa (Barewa College) da ke Zariya.

A shekarar 1975 ya samu shiga makarantar soja ta NDA (Nigerian Defence Academy) da ke Kaduna. Bayan kammala wannan karatu nasa, aka ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant) a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1977.

Kwasa-Kwasai

Bayan zamowarsa sakan laftanar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya samu nasarar samun ƙarin horo da karatu a gida Najeriya da kuma ƙasashen ƙetare. Daga ciki akwai: ‘T55 Armament Instructor Course’, a ƙasar Indiya, ‘Junior Division, Armed Forces Command and Staff College’, a Jaji, Kaduna, Najeriya, sannan ya je makarantar ‘Land Force Command and Staff College’, da ke ƙasar Kanada, sai kuma ‘Senior Executive Course 28, National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPPS)’ da ke Kuru, Jos, Najeriya, haka nan ya je ‘United Nations Training Assistance Team Seminar on Peacekeeping, Disarmament, Demobilisation and Reintegration’ a garin Accra, ta ƙasar Ghana, ya kuma halarci taron ƙarawa juna sani ‘Conference on Sub-regional Security Protocols and Demilitarisation in Africa’, ya kuma samu horon ‘ECOWAS Mechanism for Conflict Prevention, Management and Resolution, Peacekeeping and Security’ wanda aka yi a Banjul, ta ƙasar Gambiya, da kuma horo da ya samu na ‘All Central Organ Chiefs of Defence Staff Conference on Conflict Prevention, Management and Resolution’ wanda aka yi a helikwatar Tarayyar Hainkan Afirka da ke Addis-Ababa, ta ƙasa Itofiya. Da sauran ɗimbin kwasa-kwasai da horo da ya samu.

Muƙaman da ya Riƙe

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar III ya riƙe muƙamai da dama a tsawon zamansa a gidan soja na shekaru 31, tun bayan ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar.  Manya daga cikin waɗannan muƙamai da ya riƙe akwai: Ya jagoranci runduna 245 (245 Recce Batallion) wacce aka tura ta Chadi dan tabbatar da zaman lafiya a ƙarƙashin (Organisation of African Unity) daga shekarar 1981 zuwa 1982. Sannan daga shekarar 1987 zuwa 1988 ya jagoranci rundunar tsaro ta mayaƙan tanka masu tsaron fadar shugaban ƙasa (presidential security unit of the Armoured Corps) a lokacin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida. Sai kuma ya zama jami’in tuntuɓa na sojojin gamayyar tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta yamma (military liaison officer for the Economic Community of West African States (ECOWAS)).

A shekarar 1993 ya zama kwamandan bataliya ta 241 (Commanding Officer 241 Recce Battalion), ta Kaduna. Daga shekarar 1995 zuwa 1999 ya zama jami’in tuntuɓa na rundunar sojan  ‘ECOWAS’ (ECOWAS military liaison officer). Daga shekarar 1999 zuwa 2000 ya zama kwamanda na rundunar mayaƙan tanka mai lamba 231 na ƙungiyar ‘ECOMOG’ waɗanda suka yi aiki ƙasar Saliyo (Commanding Officer, 231 Tank Battalion ECOMOG Operations in Sierra Leone).

Daga shekarar 2003 zuwa 2006, ya zama (Defence Attaché) a ƙasar Pakistan wanda daga baya aka ɗaukaka shi zuwa Iran, Iraƙ, Saudi Arabia, da Afghanistan.

Barinsa Aikin Soja

Mai Alfarma Sarkin Musulumi Muhammad Sa’adu Abubakar III ya bar aikin soja a shekarar 2006. Aikin da ya yi shekara 31 a cikinsa, daga 1975 har zuwa 2006.

Zamowarsa Sarkin Musulmi

A ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2006 aka naɗa shi a wannan muƙami. Naɗin da ya biyo bayan rasuwar ‘ya’yansa a sakamakon hatsarin jirgin sama. Wannan naɗi shi ya mai da shi sarkin Musulmi na 20.


Mai Alfarma Sarkin Musulmi Yana Jawabi

Ɗawainiyoyi

Duk mai muƙamin irin wannan shi ne shugaban dukkan Musulmin Najeriya, sannan kuma babban shugaban Majalisar Ƙoli ta Al’amuran Musulunci a Najeriya (Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA)) sannan kuma babban shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI).

Ƙari a kan wannan kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ciyaman ne na ‘Nigeria Inter-Religious Council’. Haka nan kuma shi ne shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (Chancellor of the Ahmadu Bello University, Zaria).

Lambobin Yabo da Girmamawa

  • Shi ne mutum na 16 daga cikin Muslmi 500 masu tasiri a duniya.
  • An bashi muƙamin girmamawa na ‘Commander of the Order of the Federal Republic (CFR)’ a 2007.
  • Yana daga cikin mutane 10 kacal da suka karɓi lambar yabon ‘Global Seal of Integrity (GSOI)’ a shekarar 2015.

Manazarta:


Abubakar Y. (2011). Soldier-Turned Sultan, Brigadier General Sa'ad Abubakar (rtd). An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://beegeagle.wordpress.com/2011/07/02/soldier-turned-sultan-brigadier-general-saad-abubakarrtd/

Gumel B. (Ba kwanan wata). Sultan Saad Abubakar Among The Most Influential Muslims In The World. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/article8000/NEWS8940.htm

Religion for Peace (ba kwanan wata). H.M. Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sultan of Sokoto. 777 United Nations Plaza, 9th Floor New York, NY 10017.

The Authority (2016). The Authority Icon: Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar III. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.authorityngr.com/2016/01/The-Authority-Icon--Sultan-Muhammadu-Sa-Ad-Abubakar-III/

Wikipedia (2016). Sa'adu Abubakar. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Sa%27adu_Abubakar


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub