Ƙasar Zamfara a Bakin Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Alhaji Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin-Magaji (Ɗan Alin Birnin-Magaji),
Jihar Zamfara.
08149388452
birninbagaji4040@gmail.com
Tsakure
Wannan aiki a kan Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ne. Za a dubi fasihancinsa na adana tarihin ƙasar Zamfara a waƙe. Idan aka dubi ayyukan da suka gabaci wannan maƙala kan Alhaji Musa Ɗanƙwairo, za a daidaita sahun tunanin duk abinda aka ci karo da shi ta hanyar binciken Tarihinsa da tarihin waƙoƙinsa a bakin ‘ya’ya da jikoki da aminansa waɗanda ke raye. Wannan zai kai wannan bincike ga amfani da nau’in bincike na tattaunawa da kai ziyarar gani da ido a wurin mutane da wurare daban-daban. Wannan zai samu jagorancin ra’o’i guda biyu: Ra’in Tushe da Asali da Ra’in Fandarewa. Wadannan ra’o’i sun tsayu a cikin wannan aiki domin sanin asalin Musa Dankwairo, da kuma taskace tarihinsa da wakokinsa a cikin ayyukan da aka gabatar kansa. A fahimtar da na yi wa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun saboda sauraren waƙoƙinsa da nake yi tsawon lokaci, yana da matsayin da tarihin mawaƙan ƙasar Hausa da na Zamfara ba zai cika ba, ba tare da kawo sunansa da waƙoƙinsa ba. Fasihancinsa a waƙe, ya zama tamkar kotun yanke hukunci ga kowane al’amari na rayuwa.Takarda/Muƙala
- Gudunmmawar Harshe...
- Matsayin Sana'o'i...
- Tasirin Mawaƙan Baka...
- Jiya da Yau...
- Gudunmawar Shafuka..
- Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' ...
- 'Fathers' and 'Mothers' in Hausa...
- Friendship Requires Visits...
- Indigenous Languages...
- Dialectal Variation...
- Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan Baka
- Makaɗa Ibrahim Narambaɗa
- Mukala kan Dankwairo
- Ganuwar Birnin Kano...
- Fir'aunonin Masar Ta Dauri
- Shari’ar Muslunci...
Kwamfuta
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin