Tasirin Mawaƙan Baka

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tasirin Mawaƙan Baka Wajen Haɓaka Al-adun Hausa


Ibrahim Muhammad
birninbagaji4040@gmail.com
+2348091503592, +2347088700562


Tsakure

Hausawa mutane ne masu matukar riƙo da al'adunsu, wannan ta haifar da tasirin al'adu rayuwarsu ta yau da kullum. Abu ne mayuwaci ka raba al'umma da al'adunta don taron al'ummar ne ya haifar da ita.Ko bayan da addinin muslunci ya zo ƙasar Hausa,Hausawa sun ci gaba da aiwatar da al'adunsu kyawawa wadanda ba su ketare iyakar addini ba.Al'ada hanya ce ta rayuwa wadda ta ƙunshi dukkan wani abu da wannan al'ada ta ke gudanar da shi kama daga zamantakewarsu da sana'oinsu da iliminsu da bukukuwansu da tufafinsu da dukkan buƙatunsu.Babu wata al'umma da za ta rayu a doron ƙasa face sai tana da al'adunta masu kyau da marassa kyau.Don haka al'ada tsarin rayuwar al'umma ce gaba ɗayanta tun daga haihuwa zuwa mutuwa.

Mawakan baka na gargajiya sun bayar da gagarumar gudummawa wajen fito da waɗannan al'adun Hausawan da kuma haɓakasu.Ire-iren wannan gudummawa da mawakan baka suka bayar wajen raya al'adun Hausawa wannan takarda za ta duba tare da fito da su fili ta hanyar kawo misalai cikin waƙoƙinsu.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub