Tatsuniya: Biri da Kura

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Biri da Kura


Gata nan gata nanku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana kura ta biyo biri za ta cinye shi, sai ya tsere da gudu ta bishi amma bata iya cim-masa ba (ta kasa kamo shi). Da biri ya tsere wa kura sai ya je ya hau bishiyar kanya kuma ya yi sa’a ‘ya’yan kanyar sun nuna, saboda haka ya yi ta sha.

Bayan ya sakankance a kan wannan kanya sai kwatsam ya ga kura a gidin wannan bishiya tana kalen kanyar tana sha. Da biri ya ga haka sai ya samu wasu nunannu guda biyu ya zubo mata da su.

Da kura ta ga haka sai ta ce kai-kai-kai, amma ɗan tsuntsun nan kana so na. da biri ya ji haka sai ya yi dariya, sai ya sake yago wasu guburi (‘ya’yan kanya wanɗanda basu nuna ba) ya zubo mata, sai suka zubo a kan kura ji ka ke ram! Sai kura ta ce kai, haba ɗan tsuntsu kar ka kashe ni mana! Da kura ta cira kanta sama sai ta ga ashe birin da ta biyo ne. Sai ta kada baki ta ce, “Yawwa, sauko, yau za ka ci ubanka”.

Da biri ya sauko sai kura ta kama shi za ta cinye, sai ya ce da ita, “tsaya-tsaya-tsaya”. Sai ya ce da ita, “haba yaya kura, wa ya ce da ke ana cinye abu da kashi a cikinsa”, sai kura ta ce, “e, gaskiya haka ne”. Sai biri ya ce da kura, “yanzu yadda za a yi shi ne ki ɗaure ni da igiya mai tsawo, ta yadda zan yi nesa da ke dan kar warin kashin ya dame ki. Idan na gama kashin sai na dawo. Amma fa idan kin ja igiyar kin ji ta yi sako-sako, to ban tsaya ba na gudu kenan. Idan kuma ki ka ja igiyar ki ka ji da tauri, to ina nan ban gudu ba”. Sai kura ta yarda ta ɗaure biri da doguwar igiya, da biri ya tafi, sai ya ci karo da zaki, sai ya ce da zaki, sarkin dawa ga wani nama da na kama, amma saboda girmansa na kasa jansa. Sai zaki ya karɓa. Sai can kura ta ji an fara janta kiriririririri, a jefa ta can, a dungura ta can. Can tana ɗagowa daga wani dungure da ta yi sai ta ga zaki ne yake jan ta. Da ganin zaki sai kawai ta hau bashi haƙuri tana cewa ba za ta ƙara ba. Sai ya sake ta ita ma ta ranta da gudu tana ta zawo. Tun daga wannan rana kura take tsoron biri saboda shaƙiyancinsa.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub