Tatsuniya: Ƙuda da Kwaɗo da Sauro

Me ka ke nema?


Shafin Farko

atsuniya: Ƙuda da Kwaɗo da Sauro


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana ce dai, wata rana ce dai. Sai ƙuda da kwaɗo da sauro suka tafi ciyawa cikin gonaki a daji. Da suka je, sai ƙuda, da sauro suka yi ciyawarsu ‘yar kaɗan, shi kuma kwaɗo ya yi tasa da yawa. A garin ɗaukar ciyawar, sai kan kwaɗo ya ɓalle. Shi kuma ƙuda a garin dariya bakinsa ya ɓurme. Shi kuma sauro a garin gudu ƙafarsa ta karye.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub