Kofofin Zazzau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofofin Birnin Zazzau


Suleiman (2007), ya ruwaito Baikie ya ce ƙofofin Zariya guda tara ne, sai ya lissafo su kamar haka:

  1. Ƙofar Kona
  2. Ƙofar Gayan
  3. Ƙofar Kuyambana
  4. Ƙofar Doka
  5. Ƙofar Bai
  6. Ƙofar Galadima
  7. Ƙofar Matarkwasa
  8. Ƙofar Jatau
  9.  Ƙofar Tukur-Tukur/ Ƙofar Kibo

Ya kuma ci gaba da faɗin cewa ƙofar Matarkwasa ana kiranta da Sabuwar ƙofa, ƙofar da aka rufe ta a cikin ƙarni na 19.

Waɗannan ƙofofi ba a lokaci guda aka gina su ba, an gina shida ne da farko sannan kuma daga baya aka sake gina wasu guda uku. Shidan da aka fara ginawa su ne:

  1. Ƙofar Gayan.
  2. Ƙofar Kuyambana.
  3. Ƙofar Kona.
  4. Ƙofar Tukur-Tukur/Ƙofar Kibo.
  5. Ƙofar Doka.
  6. Ƙofar Bai.

A farkon ƙarni na 17 bakwa sai aka sake gina wasu guda biyu:

  1. Ƙofar Jatau.
  2. Ƙofar Galadima.
Sai kuma Ƙofar Matarkwasa wacce a ƙarni na 19, a shekarar 1808, da sarki Makau ya fasa tsakanin Ƙofar Jatau da Ƙofar Kuyambana ya shiga fada ya ɗauke takobin sarki ya gudu da shi.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub