Sarkin Zazzau Abdullahi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Abdullahi ɗan Hammada 1874 - 1879 A.D.


Gabatarwa

Bayan rasuwar sarkin Musulmi Aliyu Babba, sai sarkin Zazzau Malam Abubakar ɗan Malam Musa ya rasu. Wannan rasuwa ta sarkin Zazzau malam Abubakar, ita ta bawa sabon sarkin Musulmi Ahmad Atiƙu dama ya sake waiwaitar Malam Abdullahi ɗan Hammadan a matsayin sarkin Zazzau a karo na biyu.

Wannan naɗi, ya zo wa masu zaɓen sarkin Zazzau cikin rashin tsammani, saboda sarkin Musulmi shi ya yi gaban kansa ya naɗa sarki Abdullahi kai tsaye tun daga Sakkwato.

Sabon Madakin da tsohon sarki Malam Abdullahi ya naɗa mai suna Ali, sai ya haɗa tawaga mai ƙarfi ya fice daga Zariya ya je ya kafa tunga a garin Ifira da ke kusa da Rigachukum. Wannan gari na Ifira da ma matattara ce ta bayi. Da Madaki Aliyu ya haɗa ƙarfi a wannan gari, sai ya ɗaga tutar tawaye. Shi kuma sabon Sarki Malam Abdullahi ta nasa ɓangaren sai ya aika ɗan saƙo zuwa ga Madaki Aliyu da cewa lallai-lallai ya dawo Zariya. Wannan ɗan aiken sarki wanda ake kira Maigoto, sai suka kashe shi. Faruwar wannan lamari ta saka sarkin Zazzau malam Abdullahi tura runduna dan yaƙar mutanen Ifira, wanda kuma hakan ta ci tura.

Da sarki Abdullahi ya ga lamari ya rincaɓe, sai ya nemi Sakkwato da shigo ta sasanta, daga nan kuma sai sarkin Musulmi ya buƙaci Kano da ta shiga tsakanin. Ganin irin dangantar yaƙin da ke tsakanin Kano da Zariya, sai sarkin Kano ya tura Madakinsa da nufin ya je Ifira ya tambayi takwaransa Madakin Zazzau Ali, dalilin tawayensa. Shi kuma Madaki Ali bai ɓoye komai ba ya ce ya za a yi sarkin Musulmi ya yi musu haka, sai ya kafa hujja da cewa ai ko Shehu Usmanu Ɗanfodiyo sai da ya nemi amincewar mutanen Zazzau kafin ya bawa Malam Musa tuta.

Saboda haka Madakin Kano ya rarrashi Madakin Zazzau Ali, ya tafi Sakkwato ya kai ƙara. Bayan an saurari dukkan koken Madaki Ali, sai Sakkwato ta alƙawarta masa cewa shi ne wanda zai gaji Malam Abdullahi. Wato kenan shi zai zama sarki nag aba. Wannan ta saka yadawo ya zauna a Zariya.

Faruwar waɗannan al’amura sun jefa sarkin Zazzau Malam Abdullahi cikin ruɗani. Amma sannu-a-hankali da kuma ƙwarewar da yake da ita a baya, ya sake sabunta tsarin masarautar da kuma sake rarraba muƙamai.

Kasantuwar shekarunsa sun tafi, sannan kuma ya da lafiya gobe babu, Malam Abdullahi bai sake samun damar fita yaƙi dan faɗaɗa ƙasa da kuma ƙarfafa dangataka tsakanin Zazzau da maƙwabtanta ba. Sannan kuma a ta ɗaya ɓangaren ya daina zuwa taron shekara-shekara da ake yin a sarakuna a Sakkwato. Wannan ta tabbatar da taɓarɓarewar dangatakarsa da Sakkwato. A saboda haka bayan rasuwar Sarkin Musulmi a shekarar 1881, kamar yadda ya zo a (Smith, 1970), sai sabon sarki Musulmi ya sake tsige shi a karo na biyu.

Da aka tsige kuma sai sarkin Musulmi a aiko da takardar naɗin ga tsohon Madaki Ali, amma a dalilin tsufa da kuma matsananciyar rashin lafiyar da yake ganin ba ta tashi ba ce, sai Ali ya yi godiya sannan kuma ya ƙi amincewa da naɗinsa a matsayin sarki.

Faruwar wannan lamari ta bawa Sakkwato cikakkiyar damar miƙa lamarin sake zaɓen sabon sarki ga waɗanda abun yake hannunsu, wato masu naɗin sarkin Zariya da suka haɗa da, manyan Limaman Zariya guda biyu, Galadima, da kuma alƙalin alƙalai.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria. Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London:

Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub