Sarkin Zazzau Yamusa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Yamusa Babarbare 1821 – 1834 A.D.


Gabatarwa

Ɗalhatu (2002), ya ruwaito cewa, Malam Yamusa Babarbare, ɗa ne ga Malam Sadauki Ibrahim, wanda shi kuma malam Sadauki Ibrahim asalin sa mutumin Bagadaza ne (Iraƙi ta yau), wanda ya samu tarin ilimin addini daga gidansu kasantuwar Bagadaza cibiyar ilimi a wannan zamanin. Ya taso daga Bagadaza ya zo ya zauna a Sudan ya koyar da ilimin Alƙur’ani da sauran ilimai. Yana nan zaune a Sudan sai ya samu labarin daular Barno ta hannun fatake masu fatauci, saboda haka sai ya taso daga Sudan ya dawo Barno.

Da isowarsa Barno sai ya samu kyakkyawar tarba daga Shehun Barno na wancan lokacin. Sarkin Barno ya zaunar da shi a garin har ya aura masa ‘yarsa. Da wannan ‘ya ta sarkin Barno Malam Ibrahim ya haifi ɗa wanda aka saka wa suna Musa. Wannan suna na Musa shi Barebari ke kira Yamusa.

Malam Yamusa ya samu kyakkyawar kulawar karatu a wajen mahaifinsa. Tun yana ɗan shekara biyar ya fara koyon karatun Alƙur’ani a wajen mahaifin nasa. Ya samu nasarar sauke Alƙur’ani lokacin da yake ɗan shekara goma a duniya. Sannan kuma ya samu nasarar maimaita shi a lokacin da yake da shekara goma sha biyu. Sannan kuma ya samu ilimi mai zurfi a sauran fannoni duk a hannun mahaifinsa.

Bayan rasuwar mahaifinsa, lokacin yana da shekaru 18 a duniya, sai malam Yamusa ya bar garin Barno ya ƙaura zuwa garin Misau. A wannan gari na Misau ya shiga cikin jerin manyan malaman garin ya fara bayar da karatu. Yana wannan gari ya samu labarin Shehu Usmanu Ɗanfodiye, a saboda haka ya ƙuduri aniyar ziyartar Shehun.

Daga Misau, malam Yamusa ya ɗauko hanyar zuwa Gobir, ƙasar da Shehu yake gudanar da wa’azinsa. Amma a kan hanyarsa ta zuwa Gobir, sai ya yada zango a Zariya, garin da ya iske shi cike maƙil da malamai ana ta harkokin bada karatu. Wannan ta saka ya zauna a wannan gari na Zariya ya ci gaba da aikinsa na koyar da karatu da kuma yin wa’azi. A wannan dalili ya kewaye birni da ƙauyukan Zariya. Ta wannan dalili ya haɗu da Malam Musa Bamalli da kuma sauran ƙabilun Fulani da ke zaune a wannan yanki na Zariya. Haka nan a irin yawon wa’azin da yake yi ya haɗu da Malam Kilba a garin Barnawa da ke Kudu-maso-Yamma da garin Kaduna (Amma yanzu ya zama unguwa a cikin garin Kaduna). Zamansa tare da Malam Kilba a matsayin almajiri, ta saka shi Malam Kilba ya yaba da hazaƙarsa saboda haka ya aura masa ‘yarsa. Bayan an yi wannan aure ne Malam Yamusa ya ci gaba da tafiyarsa zuwa Gobir domin haɗuwa da Shehu Usmanu Ɗanfodiye.

Kwanci-tashi, Malam Yamusa ya isa Gobir, ya zama ɗaya daga cikin almajiran Shehu Usmanu Ɗanfodiye. A nan ma ya sake gamuwa da Malam Musa Bamalli wanda shi ma yake karatu a wajen Shehu. Daga baya Malam Musa Bakatsine ya same su a Gobir. Waɗannan malamai da su aka yi jahadin Shehu Usmanu Ɗanfodiye wanda aka gwabza da sarki Yunfa har aka fatattake shi da mayaƙansa.

Bayan kafuwar Daular Shehu Usmanu Ɗanfodiye, da kuma ayyana kora da sarkin Zazzau Makau ya yi ga dukkan wani malami Bafulatani da ke yankin Zazzau, sai Shehu Usmanu Ɗanfodiye ya ayyana jihadi a Masarautar Zazzau. Malam Musa Bamalli wanda shi Shehu ya bai wa tuta, shi ya fara zama sarkin Zazzau bayan samun nasarar fatattakar sarki Makau da jama’arsa.

Bayan dukkan yaƙuƙuwan da aka yi, an fatattaki sarki Makau da jama’arsa ƙarƙashin kwamadancin Malam Yamusa har zuwa Zuba. Daga nan kuma sai Malam Yamusa ya dawo gida Zariya. Dawowarsa gida Zariya sai Shehu Usmanu ya umarci Malam Musa Bamalli da ya yi wa Malam Yamusa naɗin Madakin Zazzau.

Zamowarsa Sarki

Yamusa Barbare, shi ne sarkin Zazzau na biyu a jerin sarakunan Fulani. Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne ya naɗa shi bayan rasuwar Malam Musa Bamalli.

Wannan naɗi nasa ya biyo bayan shawarar da masu zaɓen sarki suka bada wanda ya haɗa da Galadima da kuma Limamin Juma’a na masarautar ta Zazzau, da kuma wasiyyar da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya bari. Malam Yamusa Babarbare shi ne tushen gidan Barebari na Zazzau.

Malam Yamusa ya yi sarautar Zazzau ta tsawon shekaru goma sha uku, ya rasu a shekarar 1834 A.D.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.

 


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub