Shafin Farko

Kariya Daga Larurar Hankali


Gabatarwa

Kariya a nan ita ce abar da aka kira Prevention a Turance. Bincike ya tabbatar da cewa, da yawa daga cikin matsalolin da ke haifar da wannan larurar ta hankali, masu magantuwa ne; abin nufi, ana iya maganin da yawa daga cikin matsalolin da ke haifar da larurar hankali. Misali, ana iya kawar da cutar ƙyanda ta hanyar riga-kafi; ana iya magance matsalar ƙarancin abinci ta hanyar samar da abincin da ya dace; ana iya magance matsalar cututtuka masu yaɗuwa; ana iya rage tsawon naƙuda ta hanyar allura; ana iya magance matsalolin da suka shafi larurorin goyon ciki ta hanyar zuwa asibiti awon-ciki; ana iya magance matsalar wariya, wahalar da yara da rashin kula da su ta hanyar adalci da sauransu.

Manazarta:


Alhassan F.A. (2015). A Guide in Special Education. Tamasi Computers, Kano, Nigeria.

Child Care Law Centre (1990). Caring for Children With Speciall Need: The Americans With Disablities Act and Childe Care. Child Care Law Centre, USA. 10016, Deekay Printers, India.

National Council of Educational Research and Training (2001). Education of Children With Special Needs. Sri, Aurobinda Marg, New Delhi.

Federal Ministry of Education (2015). National Policy on Special Needs Education. Federal Ministry of Education, Abuja, Nigeria.

National Teachers Institute (2000). NCE/DLS Course Book On Education Cycle 4. National Teachers Institute, Kaduna, Nigeria.

Repp A.C. da Coutinho M.J. (2008). Special Education. Microsoft Encarta 2009. © 1993-2008 Microsoft Corporation.