Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Kano Ado Ɗan Abdullahi Bayero (1963 - 2014)Alhaji (Dr.) Ado Abdullahi Bayero


Gabatarwa

Alhaji Ado Bayero. Shi ne Sarki na 55 a jerin sarakunan Kano kuma sarki na 13 a sarakunan Fulani. Tun daga farkon sarautar Kano zuwa yau (2017), marigayi Alhaji (Dr.) Ado Bayero shi ne sarkin da ya fi kowane sarki daɗewa a kan karagar mulkin Kano. Sarki ya mulki Kano na tsawon shekaru 51 tun daga 1963 har zuwa 2014.

Tsohon ma’aikacin banki, wakilin doka, ma’aikacin hukumar En’e (NA), kuma tsohon wakilin Najeriya a ƙasar Sinigal. Daraja, da martabar masarautar Kano ta ɗaukaka a iya tsawon mulkinsa.

Haihuwarsa

An haifi Alhaji (Dr.) Ado Bayero a ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1930 (Wikipedia, 2014; Mahmood, 2014; Umar, 2008). Shi ɗa ne ga sarki Abdullahi Bayero, shi kuma ɗan sarki Muhammadu Abbas, shi kuma ɗan sarki malam Ibrahim Dabo bafulatani kuma basulluɓe. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Hasiya. Saboda haka cikakken sunansa shi ne Alhaji (Dr.) Ado Abdullahi Bayero (CFR, LLD, JP). Amma an fi kiransa da Alhaji (Dr.) Ado Bayero.

Tasowarsa

Alhaji (Dr.) Ado Abdullahi Bayero, ya fara karatunsa na addini tun yana ƙarami kamar yadda aka saba. Sannan daga baya aka saka shi a makarantar ‘Middle School’, ya samu nasarar zarcewa zuwa makarantar koyon Larabci ta Kano wato ‘School for Arabic Studies’ (SAS) inda ya fita a shekarar 1947. Ya kuma halaraci makarantar ‘Zaria Clerical College’ da ke Zariya a shekarar 1952.

Ayyukan da Ya Yi

Kafin zamowarsa sarki, Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya yi aikin banki tare da ‘The Bank of British West Africa’ har zuwa shekarar 1949, inda daga nan kuma ya zarce zuwa hukumar nan ta ‘Native Authority’ wacce ake yiwa laƙabi da (NA) a matsayin akawun majalisa. A shekarar 1954 kuma aka zaɓe shi a matsayin wakili a Majilisar Lardin Arewa da ke Kaduna. Daga kan wannan muƙamin kuma aka yi masa wakilin doka na Kano tun daga shekarar 1957 har zuwa 1962. Sannan ya zama wakilin Najeriya a ƙasar Sinigal muƙamin da yana kansa aka yi masa Sarautar Kano.

Zamowarsa Sarki

Alhji (Dr.) Ado Abdullahi Bayero, ya zamo sarkin Kano a shekarar 1963. Shi ne sarkin Kano na 55, sannan kuma sarki na goma sha uku a jerin sarakunan Fulani.

Gudunmawar da ya Bayar

Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawar da ba zai yiwu a ƙididdige ta ba. Shi ne sarkin da Kano ta zama jaha a hannunsa. Ya yi zamani da gwamnoni goma sha biyar, sannan kuma ya yi aiki da shugabannin ƙasa guda goma sha uku. Ya ga canje-canje iri-iri. Da bakinsa yake cewa, “Da mu muke yi, aka zo ana yi da mu, yanzu kuma sai an yi a gaya mana” (Mahmood, 2014).

Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya ciyar da Kano gaba, kamawa tun daga taimakon ɗaiɗaikun mutane; dalilin da ya sa ake yi masa kirari da Baya goya marayu, Uban maras uba, har zuwa kan ƙungiyoyi, har zuwa gina masallatai, makarantu, da sauran ayyukan alheri masu tarin yawa. Bari mu leƙa Umaru (2008), mu ɗan tsakuro:

 1. Kira zuwa ga addinin Musulunci da tsayar da ibada, da kuma musuluntar da waɗanda ba musulmi ba.
 2. Gina masallatai da makarantun Islamiyya a cikin birni da ƙauyukan Kano.
 3. Nuna soyayya ga malamai da masu wa’azi da sauran masu yiwa addini hidima.
 4. Bada goyon baya ga aiwatar da shari’ar Musulunci da ƙarfafa aiki da ita, da zartar da hukunce-hukunce bisa tafarkinta daidaitacce.
 5. Sake gina katangar gidan sarki da duwatsu da siminti.
 6. Lulluɓe titunan cikin gidan sarki da tayil mai kyau.
 7. Sake gina gidajen Wambai, Galadima, Waziri, da gidajen hakimai da ke ƙananan hukumomi.
 8. Wadata hakimai da ababen hawa.

Rasuwarsa

Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya mulki Kano na tsawon shekaru 51. Ya rasu a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2014. Ya rasu ya bar ‘ya’ya maza 31 da kuma ‘ya’ya mata 30. Allah ya jiƙansa da rahama amin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.

 • Masarautar Kano

 • Sarakunan Fulani


  Kasuwanni  Bukukuwa

  Kasuwanni  Bukukuwa


  Wasu Gurare


  Tashoshin Mota


  Yaƙuƙuwa


  Ƙofofin Kano


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub