Me ka ke nema?


Shafin Farko

Aliyu Ɗan Abdullahi 1894 – 1903 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Aliyu ɗan Abdullahi wanda aka fi sani da Sarki Alu. Shi ne sarki na 50 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 7 a jerin sarakunan Fulani.

Ya shiga gidan sarautar Kano bayan ya ci sarki Tukur da yaƙi a garin Tafashiya. Da shigarsa gidan saurata sai ya sa aka riƙa bi gida-gida ana kamo talakwa ana kashewa wasu kuma ana mayar da su bayi, kamar yadda ya zo a cikin littafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu littafi na biyu (1979). 

Daga sunayen da ake kiransa da su akwai Alu Mai Sango. Wannan suna ya samo asali ne saboda wasu irin dogwayen alburusan bindiga da yake amfani da su wanda tarihi ya nuna cewa sarkin Nupe ne ya aiko masa da su.

A zamanin sarki Alu, Kano ta yi yaƙuƙuwa da dama, waɗanda masana ke cewa da kamar wuya, gurguwa da auren nesa, a iya tantance yawan yaƙuƙuwan da ya yi. Daga cikin garuruwan da Sarki Alu ya yi munanan yaƙuƙuwa da su akwai Damagaran.

Tun zamanin Sarkin Kano Bello, wasu Kanawa suka je Damagaran kasuwanci, sai aka kama su aka yi musu wasoson dukiya. Da sarki Bello ya tura jakada dan jin bahasi, sarkin Damagaran na wannan lokacin bai bashi wata cikakkiyar amsa ba.

Tarihi ya nuna cewa, a zamanin sarki Alu, sarkin Damagaran ya nufo Kano da yaƙi. Maimakon ya tafo Kano kai tsaye sai ya turawa sarkin Sankara cewa ya nan tafe. Da Sarkin Sankara ya samu wannan saƙo, sai ya sanar da wani malami da ya ke tare da shi. Wannan malami mai suna Malam Almajir, sai ya yi wasu abubuwa irin nasa, ya kewaya garin Sankara, sai ya ce da sarki ya mayarwa da sarkin Damagaran amsa da cewa ƙarya yake bai isa ba. Da wannan amsa takai kunnen sarkin Damagaran, sai ya hau ya nufo Sankara gadan-gadan. Da isowarsa Sankara sai ta ɓace masa da gani ya nemeta ya rasa. Sama-ko-ƙasa.  Shike nan, daga nan sai ya zarce zuwa Kano bai tsaya ko’ina ba sai Gezawa, inda a nan sarkin Kano Alu ya je ya datse shi.

Cikin jaruman sarkin Damagaran akwai wani jarumi mai suna Mayana, shi ya fara ɗaura ɗamara ya yiwa sarkin Damagaran alƙawarin zai kawo masa sarki Alu. Daga nan ya fara ratsa rundunar Kanawa, da ya iso daf da fadawan sarki suka yi masa caaa, sai sarki ya dakatar da su ya ce su ƙyale shi ya ƙaraso. Da isowarsa gaban sarki sai sarki ya saka takobi ya yi masa saran kabewa; wato ya raba shi gida biyu ke nan daga sama zuwa ƙasa.

Da labari ya je kunnen sarkin Damagaran cewa Mayana ya zama gawa, sai hankalin Damagarawa ya tashi; wato sun san abin na yi ne. Daga nan mazaje suka gauraya ake ta fafatawa har zuwa wani lokaci mai tsawo, Kanawa suka fatattaki Damagarawa. An ce saboda tsabar ruɗewa da Damagarawa suka yi, har cikin kara mata ke bi suna kamo jaruman Damagarawa da hannu suna kashewa. A lokacin wannan yaƙi an ce sarki Alu ya yi ɓad-da-kama ne ya yi shigar Buzaye, ya shiga cikinsu ya yi ta kisa.

Bayan komawar sarkin Damagaran gida, sai ya fara bincike kan dalilin da ya saka bai ga garin Sankara ba. Sai ya samu labarin cewa ai wani malami ne mai suna Malam Almajir ya yi aiki irin nasa. Da sarkin Damagaran ya samu wannan labari, sai da ya bi duk hanyoyin da zai bi, ya samu ganawa da Malam Almajir kuma ya roƙe shi kan cewa ya taimaka masa ya ci Kano da yaƙi. Malam Almajir ya amsa wa sarkin Damagaran amma da sharaɗin ba zai biyo ta Sankara ba. Jin haka shima sarkin Damagaran ya amince.

Da sarkin Damagaran ya tashi komawa Kano da yaƙi, sai ya bi ta wani gari mai suna Tattarawa wanda a yanzu yake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bichi. Shi kuma sarki Alu ya je Damargu; ita ma dai duk a cikin ƙaramar hukumar Bichi ta ke, sai ya datse shi a can suka fafata. Wannan yaƙi bai yiwa Kanawa daɗi ba, saboda Damagarawa sun yi galaba a kansu. Amma dama tun kafin fita wannan yaƙi da labari ya zo gari, malamai sun gayawa sarki Alu cewa kar ya fita, fita a wannan rana ba daɗi a bari sai gobe. Amma da sarki ya yi shawara da hakimansa da sauran waɗanda suka kamata, sai suka ce da shi ai bari sai gobe tsoro ne, a hau kawai a fita. To a wannan yaƙi sai da Damagarwa suka koro Kanawa har dab da ganuwar gari. A wannan hali ba mafita sai sarki Alu ya je ya samu malamai suka duƙufa cikin addu’a, sannan kuma a lokaci guda ya nemi agajin Turabulusawa mazauna Kano; wato mutanen Turabulus kenan, garin da a yanzu ya ke cikin ƙasar Mali, suka ɗauko bindigunsu suka hau kan ganuwa suka tsare gari. Ana wannan hali sai zazzaɓi ya saukawa sarkin Damagaran, saboda haka sai suka juya suka koma. Wannan shi ya kawo ƙarshen wannan yaƙin.

Fafatawar ƙarshe tsakanin Sarki Alu da Danagarawa an yi ta ne a bakin Tomas da ke cikin ƙaramar hukumar Ɗambatta ta yau. A wannan zamani kuma sarki Ahmadu ne yake sarautar Damagaran. Da suka yiwo hawa suka ɓullo ta Ɗambata, sai sarki Alu ya yi maza-maza ya tare su a Tomas. Haƙiƙa wannan yaƙi kowa bai ji da daɗi ba. Amma dai a ƙarshe Kanawa ne suka galabci Damagarawa bayan sun kori Kanawa har gida. An ce sai da Damagarawa suka kori Kanawa suka koma gida suka shiga ta Ƙofar Kansakali. A nan sarki Alu ya zambace su kamar yadda dama aka sani ana cewa yaƙi ɗan ɗamba. To hakan ce ta faru. Da Kanawa suka dawo gida sai sarki Alu ya ce a bar ƙofar garin a buɗe kar a rufe. Su kuma Damagarwa da suka ga ƙofa a buɗe sai suka sanar da sarki Ahmadu cewa sun ga ƙofa a buɗe saboda haka za su je har gida su kamo sarki Alu. Ashe shi kuma sarki Alu ya laɓe daf da ƙofa, ya yi shiga irin ta Buzaye. Saboda haka duk Buzun da ya shigo nan take sai sarki Alu ya kashe shi. Haka ya yi ta yi musu, har sai da ta kai jallin da su Damagarwa suka fahimci cewa duk fa wanda ya shiga baya dawowa. Saboda haka sai suka haƙura suka juya.

Sannan kuma a zamanin sarki Alu an samu sa-in-sa tsakanin Ningi da Kano. Amma saboda sarki Ɗanyaya yana jin tsoron sarki Alu sai ya zama ba a gwabza yaƙi ba.

Sannan kuma dai a zamanin sarki Alu ne gaba ta tsananta tsakanin Kano da Haɗeja. A wannan zamani sarki Muhammadu ne yake sarautar Haɗeja.

Sarkin Kano Alu shi ya gina garuruwan Fajewa, Ɗando, Magami, Bura, Kwajali da Musa duk a Kudancin Kano a zamaninsa.

Daga ƙarshe, sarkin Kano Alu ya tafi kai caffa Sakkwato Turawa suka zo suka ci Kano. Wannan labari na shigar Turawa Kano ya iske sarki Alu a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa Kano shi da jama’arsa da suka haɗa da sarakuna, hakimai, fadawa, lifidai, da sauransu. Da labari ya same su, jama’arsa sun bashi shawarwari kamar haka: “Ko dai ka tsaya mu yi faɗa da Turawa, ko kuma ka nemi sulhu da su". Wasu kuma suka ce a’a, ya koma Sakkwato wanda kuma hakan ce ta faru. Shi sarki Alu da wasu jama’a sai suka koma Sakkwato. Wasu kuma ciki har da Wambai Abbas da Waziri Ahmadu da wasu jama’ar sai suka ci gaba da tafiya Kano.

Da wannan tawaga ta iso Kwatarkwashi sai ta yada zango. A wannan zango nasu sai suka haɗu da Turawa. Zatonsu Damagarawa ne saboda haka sai suka far musu da yaƙi. A karon farko sai aka kashe Waziri Ahmadu, da ɗansa da ɗanmorinsa. Haka yaƙi ya ƙare. Wambai Abbas da sauran jama’a suka dawo Kano.

A lokacin da Wambai Abbas ke kan hanyarsa ta komawa Kano, sai Turawa suka tura aka tarbe shi. Wambai Abbas da tawagarsa sun iso Kano ranar Juma’a. Sun shigo Kano ta Ƙofar Kansakali. Kafin shigarsu Kano sai da Turawa suka caccaje kayayyakinsu suka ƙwace dukkan makamansu.

Sarki Aliyu mai laƙabi da Alu Mai Sango, ya rasu bayan ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara tara da wata tara.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub