Shafin Farko

Ibrahim Dabo Ɗan Mahmudu 1819 – 1846 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Ibrahim Dabo shi ne sarki na arba’in da biyar sannan kuma sarki na biyu a sarakunan Fulani. Sarki Ibrahim Dabo mutum ne adali kuma masanin furu’a (fiƙihu), sannan kuma mutum ne mai taimako.

Sarki Ibrahim Dabo shi ake yiwa laƙabi da “Mai buɗe Garuruwa”. Sabon Galadima da ya naɗa; wato malam Sani a matsayin Galadiman Kano, ya yi nufin cin amanarsa amma Allah bai nufa ba.

Bayan zamowar Sani Galadiman Kano sai ya riƙa haɗa munafurci ta ƙarƙashin ƙasa, ya riƙa aikawa sarakuna kudu-da-arewa, gabas-da-yamma kan su haɗu su yaƙi sarki. Daga ciki akwai manyan garuruwa irin su Ƙaraye, Ɗambatta, Kazaure, Dutse, Birnin Kudu, Rano da sauransu. Da sarki ya samu labari sai ya shiga addu’a sai da ya yi kwana arba’in bai fita. Da ya fito sai ya haɗa runduna ya je gindin Dala ya yada sansani sai da ya yi wasu kwanaki a wurin. Sa’an nan ya koma gida. Sai ya aika sarkin Dawaki Mai tuta zuwa Ƙaraye ya je ya yaƙe ta kuma ya yi galaba. Daga nan shi da kansa ya yi shiri ya fita zuwa Jirima ya yaƙe ta ya yi nasara. Haka-haka ya yi tayi har sai da sauran garuruwa suka tabbatar zai ci su da yaƙi sannan suka zo suka bishi. Saboda haka ake yi masa kirari da “Mai buɗe garuruwa”.

Bayan mutuwar Galadima Sani sai sarkin Kano Ibrahim Dabo ya sake naɗa wani abokinsa mai suna Ango a matsayin Galadiman Kano.

Sarki Ibrahim Dabo ya mulki Kano tsawon shekara ishirin da bakwai da wata tara. Ya rasu a watan Safar. Allah ya jiƙansa da rahama. Amin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.