Shafin Farko

Kutumbi Ɗan Muhammadu Nazaki 1623 – 1648 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Kutumbi shi ne sarki na ishirin da tara a jerin sarakunan Kano. Asalin sunansa shi ne Muhammadu Auwalu. Akwai matuƙar himma tare da wannan sarki. Shi ne sarkin day a fara karɓar jangali (kuɗin harajin dabbobi) a hannun Fulani. Sannan kuma shi ne sarkin day a fara naɗa sarautar Barde Ƙerarriya.

Kasancewars mutum mai himma, da jarumtaka, Sarki Kutumbi ya shimfiɗa mulki a ƙasar Hausa bakwai (Kano, Daura, Rano, Katsina, Gobir, Zazzau da kuma Birom (Garun Gasa)). Shi ne sarkin day a gina gida a Guduwawa, saboda duk lokacin da zai fita yaƙi yakan je can ya haɗa tawagarsa, haka nan idan ya dawo yakan je can ya yada zango ya huta. Sarki Kutumbi ya yaƙi  da Bauchi sannan Katsina, amma Katsina ta gagare shi. A ƙarshe ya mutu sakamakon sukan mashi da ya samu a lokacin yaƙinsu da Katsina. Sarki Kutumbi ya mulki Kano tsawon shekara ishirin da shida.  

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.