Shafin Farko

Muhammadu Inuwa Abbas (1963)


Gabatarwa

Sarki Muhammadu Inuwa shi ne sarki na 54 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 12 a jerin sarakunan Fulani. An yi masa sarautar Kano lokacin yana riƙe da muƙamin Turakin Kano. Sannan kuma ya yi hakimi a Bichi, da kuma gundumar Minjibiri wacce ta haɗa da Kunya da Kuru kafin zamowarsa sarki.

Sarki Muhammadu Inuwa Abbas bai yi tsawon zamani a kan karagar mulkin Kano ba. Ya yi sarauta ta tsawon wata shida kacal. Ya rasu a cikin shekarar 1963. Allah ya jiƙansa. Amin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.