Shafin Farko

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (2014 zuwa yau)Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II


Gabatarwa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Mutu ne masanin addini da kuma zamani, basarake kuma malami. Malamin makaranta sannann kuma ma'aikacin banki; gogaggen masanin tattalin arziƙi. Ya yi karatun addini da na zamani a matakai masu zurfi. Yana da digirorin farko biyu a fannuka daban-daban, ɗaya a fannin tsimi da tanadi (Economics) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ɗayan kuma a fannin Shari’ar Musulunci (Islamic law) daga Jami’ar Afirka ta ƙasa-da-ƙasa (African International University) da ke Kartum ta ƙasar Sudan. Sannan kuma ya yi digiri na biyu a fanninsa na tsimi da tanadi (economics).

Ya bada gagarumar gudunmawa wajen ci gaban addinisa da kuma ƙasarsa. Hamshaƙin masani ne, mai mulki, kuma basarake.

Kafin zamowarsa sarki, ya fara karantarwa a Jami’arsa ta Ahmadu Bello, sannan ya koma ainkinsa na banki wanda har sai da ya zamo gwamnan babban bankin Najeriya. Shi ne ɗan Arewa na farko da ya fara zama shugaban bankin First Bank.

Shi ne Sarkin Kano na farko da aka naɗa a ƙarƙashin gwamnatin jahar Kano. ya karɓi kyaututtukan girmamawa da dama.

Haihuwa

An hafi Mai Martaba Sarki, Muhammadu Sanusi II a ranar 31 ga watan Yuli na shekarar 1961 (31 July, 1961). Shekara ɗaya kenan bayan samun ‘yancin kan Najeriya. Shi ɗa ne ga Ambasada Muhammad Aminu Sunusi. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Saudatu. Jika ne shi ga sarkin Kano marigayi Muhammadu Sunusi (Maje Azarai).

Salsala

Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ɗa ne ga Muhammadu Aminu Sanusi. Wanda shi kuma ɗa ne ga Marigayi Sarki Muhammadu Sanusi I (Allah ya jiƙansa da Rahama) wato sarkin Kano na 54 (1953-1963). Kenan, kakansa ya bar kujerar mulki lokacin yana shekara 2 da haihuwa. Shi kuma Sarki Muhammadu Sanusi ɗan ne ga Sarki Abdullahi Bayero, sarkin Kano na 54. Shi kuma ɗan Sarki Muhammadu Abbas, sarkin Kano na 51. Shi Kuma ɗan Sarki Abdullahi, sarkin Kano na 47. Shi kuma ɗan Sarki Ibrahim Dabo, sarkin Kano na 45.

Karatu

Mai Martaba Sarki, Muhammadu Sanusi II, ya yi karatunsa na firamare a makarantar St. Anne’s Catholic Primary School da ke Kakuri, Kaduna daga shekarar 1967 zuwa 1972. Daga nan kuma ya wuce zuwa makarantar sikandire ta King's College da ke Lagas daga shekarar 1973 zuwa 1977. Bayan kammala karatunsa na sikandire ne ya samu nasarar shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi (economics) a shekarar 1981. Ya kuma samu digirinsa na biyu shima a fannin tsimi da tanadi (economics) a wannan Jami’a ta Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1983.

Haka nan a fannin ilimin addini ma ba a bar Mai Martaba Sarki, kuma malami a baya ba, saboda ya yi karatun addini mai zurfi. Ya yi karatun digiri a fannin Shari’ar Musulunci a Jami’ar ƙasa-da-ƙasa ta Afirka (African International University) da ke kartum ɗin Sudan, inda ya yi karatu daga shekarar 1991 zuwa 1997.

Gogayyar Aiki

Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya fara da aikin malanta a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Ya zama malami a wannan jami’ar bayan gama karatun digirinsa na biyu. Ya yi wannan aiki na malinta na tsawon shekara 2, daga shekarar 1983 zuwa 1985.

Ya bar aikin Malanta a shekarar 1985 inda ya koma aiki da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Icon Limited wanda shi kuma wannan kamfani reshe nena bakuna biyu; Morgan Guaranty Trust Bank da ke New York ta ƙasar Amurka, da kuma Baring Brothers da ke London ta ƙasar Burtaniya ko kuma kai tsaye mu ce ta ƙasar Ingila.

A shekarar 1997 ya bari ya koma bankin haɗin kai; wato United Bank for Africa wanda aka fi sani da UBA, wanda ya shiga a matsayin manajan gama-gari (General Manager) na sashen bashi da kuma sarrafa hatsari (Credit and Risk Management Division). Ya yi aiki da wannan banki na UBA har sai da ya kai matsayin babban manaja a wannan fanni nasa.

A shekarar 2005, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya bar wannan banki na UBA ya koma First Bank. A wannan banki sai da ya riƙe muƙamin babban Manaja (MD) a shekarar 2009, muƙamin da ya zama shi ne ɗan Arewa na farko da ya fara riƙe shi tun daga lokacin da aka buɗe bankin a shekarar 1894. Wato kenan, iya tsawon shekara ɗari da goma sha biyar (115) da wannan banki ya yi, ba a taɓa samun ɗan Arewa da ya riƙe wannan muƙami da Mai Martaba Sarki ya riƙe ba.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya

A ranar ɗaya ga watan Yuli na shekarar 2009 (1st June, 2009), shugaban Najeriya Umaru Musa ‘Yar’aduwa mai rasuwa (Allah ya jiƙansa), ya yi masa muƙamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Zamowarsa Sarki

Bayan rasuwar marigayin sarkin Kano, Alhaji (Dr.) Ado Bayero, sai manyan 'yan majalisar sarki; masu zaɓen sabon sarkin Kano suka tantance sunan Muhammadu Sanusi II, suka miƙa wa gwamnatin jahar Kano ƙarƙashin Engr. (Dr.) Rabi'u Musa Kwankwaso. Zaɓen da ya samu amincewar gwamnatin jahar inda ta bayyana Muhammadu Sanusi II, a matsayin sabon sarkin Kano.

Wannan sanarwa ta fito ta bakin sakataren gwamnatin jahar Kano, Alhaji Rabi'u Suleman Bichi, da yammacin ranar Lahadi 8 ga watan Juli na shekarar 2014 (8/06/2014).

Tun daga wannan rana, har zuwa yanzu nan (2017), Muhammadu Sanusi II, shi ne sarkin Kano.

Manazarta:


BBC Hausa. (2014). Tarihin Mallam Sanusi Lamido Sanusi. An ciro daga: http://www.bbc.com/hausa/news/2014/06/140608_ sanusi_sarki. A shekarar 2016.

Central Bank of Nigeria (2016). Past Governors. An ciro daga: http://www.cenbank.org/aboutcbn/allgoɓernors.asp. An ciro a shekarar 2016.

Muryar Amurka. (2014). Sabon Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, yana fitowa don tara baki, Yuni 12, 2014. An ciro daga: http://www.ɓoahausa.com/media/ɓideo/sabon-sarkin-kano-alhaji-sanusi-lamido-sanusi-yana-fitowa-don-tar-at-baki-yuni-12-2014/1935858.html. An ciro a shekarar 2016

Nigerian Biography. (2015). Biography of Sanusi Lamido Sanusi. An ciro daga: http://www.nigerianbiography.com/2015/10/biography-of-sanusi-lamido-sanusi.html. A shekarar 2016.

Otuchikere C.(2008). Nigeria: Sanusi Lamido Sanusi Becomes First Bank MD. An ciro daga: www.http://allafrica.com/stories/200808110742.html. An ciro a shekarar 2016.

Peoples Daily. (2016). The Boy destined to be King: The Story of SANUSI LAMIDO SANUSI. An ciro Daga: http://weekend.peoplesdailyng.com/indeɗ.php/lifestyle /lifestyle/3447-the-boy-destined-to-be-king-the-story-of-sanusi-lamido-sanusi. A shekarar 2016.

Wikipedia (2016). Sanusi Lamido Sanusi. An ciro daga: https://en.wikipedia.org/wiki/Sanusi_Lamido_Sanusi.