Shafin Farko

Muhammadu Zaki ɗan Kisoke 1582 – 1618M


Gabatarwa

Sarki Muhammadu Zaki shi ne sarki na ishirin da bakwai a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Hafsatu. Shi ne sarkin da ya ci Katsina da yaƙi. Bayan hawansa karagar Mulki, ya yi ɗamarar yaƙi ya fita zuwa Daura. Katsinawa suka dinga kai hari iya duk faɗin ƙasar Kano, sannan kuma ga matsananciyar yunwa. An shiga wannan mayuwacin hali har tsawon shekara goma sha ɗaya.

Da sarki ya ga haka sai ya tara malamai ya ce da su, “Ban tara ku domin komai ba sai domin mu yi shawara akan abin da za mu yi mu kawad da wannan musiba”. Shehu Abubakar Bayammi ya ce da shi, “Idan kana so ka rinjayi Katsinawa, nab aka abin da za ka rinjaye su da shi. In har ka rinjaye su kada ka komo wannan alƙarya”. Ya ce, “Na yarda”. Ya kawo dukiya mai yawa ya bawa Shehu Abubakar Bayammi. Shi kuma ya bashi abin day a bashi. Sarki ya yi ɗamara ya fita a ranar ishirin da biyu ga watan Ramalana. Ya isa Katsina ranar idi, suna shirin fita idi abin ya koma yaƙi. Sarkin Kano ya fattattaki Katsinawa suka waste. Kanawa suka samu ganima mai tarin yawa. Daga ciki akwai dawakai arbamiya da lifida sittin da tarin dukiya da bayi. Babu wanda zai iya ƙissima adadin mutanen da aka kashe. Daga nan sarki ya dawo Ƙaraye ya mutum a can. Ya mulki Kano tsawon shekara Talatin da bakwai da wata biyar.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.